← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 205

Sashe 6

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

goyan bayanki, nima na shigo team in Omar and Nayla forever Dariya ya bawa Nayla ta yi dariya tana kallonsa. Yayi murmushi ya ce, Wallahi da gaske nake miki Nayla, dan haka kar ki bar komai ya dame ki, komai zai wuce kamar bai faru ba. In na koma gida zan saka a kawo miki motarki, na kuma yi al awarin sabuwar mota za a kawo miki Kano ba wacce kika bari a gida ba. Sannan batun transfer na wajan aikinki mun fara maganar yadda za a yi, zaki cigaba da aikin ki kamar kina Kaduna. Murmushi tayi cikin jin da in ganinsa ta ce, To Yaya J. Na gode sosai. Kar ki damu. In akwai za in motar da ki ke so ki fa a min sai a siya miki ita. Jidda ta ce, lallai Yaya J ni fa?. Harararta ya yi ya ce, motar da ki ke hawa tafi tawa tsada, ai ke mijinki ya shagwa aki, kinfi arfina yanzu. Dariya tayi ta ce, ta sa daban ta ka daban. Murmushi ya yi bai ce komai ba sai kallon Nayla yake yi cikin tausayinta. Mama ta ri e hannunta ta ce, ta so mu je aki. Nayla ta bi bayan Mama har aki ta zaunar da ita akan gado ta ce, komai na gidan ya yi miki?. Kai ta aga alamun eh Mama ta ce, in akwai abinda bai yi miki ba ki fa a min sai a siyo a aiko miki dashi. Turaren wuta duk an saka miki na wajan wacce muke siya in nan daga Sudan. Spices da komai akwai a kitchen dan akwai kayan abinci da aka kawo duk suna store. To Mama ta amsa a sanyaye. Zuwa jibi Baba Salisu zai kawo miki ragowar kayanki da abinda na san zaki amfani dashi a akin ki. In akwai abinda ki ke so shima sai ki fa a min. Kai ta aga kawai Mama ta sake cewa, kar ki damu kin ji? kar ki dinga ajjiye damuwa a ranki, duk abinda yake damunki ki sanar dani. Omar in ya zo kuwa?. Kai ta girgiza alamun bai zo bac Mama cikin damuwa ta ce, ya Allah! Ke ka ai ki ka kwana a gidan nan?. Ni da Salma ta bata amsa hawaye na sakkowa daga idanunta. Mama ta ce, duk abinda yake faruwa ki dinga sanar min dan ba komai zamu dinga jurewa mu zuba idanu ba, duk abinda ya faru ki sanar dani ni kuma zan san abinda zan yi. Nayla ta aga kai dan magana wahala take mata. Mama ta ce, kar fa ki ce zaki oye min, in baki fa i damuwarki ba baza ki ji da i ba. Nayla ta ce, to Mama. i Mama ta ajjiye mata ta ce, ga sadakin auren ki nan, sannan ga wannan ki ri e a hannunki, zan ha o har Atm card inki a kawo miki. Nayla ta ce, To Mama, an gode. Mama ta ce, kina son housemaid a kawo miki daga Kaduna?. Nayla ta ce, E Mama. To zan duba na gani, ko Khajida ce jikar Uwani ta gida wacce take yiwa Abiy osan sadaka sai a kawo miki, naga kuna shiri da yarinyar. Sai dai babu akin da za a ajjiyeta. Nayla bata ce komai ba Mama ta ce, zan san yadda zanyi dai. Mama ta arewa akin kallo tana ta e baki ta ce, zaki sha zafi, naga gaba aya gidan babu ac, iskar fanka me take sakawa banda mura da ciwon kunne?. Har gwara ma na falo naga stand fan ce, ai sunfi akan wannan ta fa a tana nuna fankar Nayla dai bata tanka ba suka fito tare da Mama. Nayla kalli Jawad ta ce, Yaya J Ina Yaya ne?. Yaya ya koma Lagos, zai yi miki waya ya ce min zai kiraki. Allah ya taimaka ta bashi amsa a ta aice. Mama ta ce, To Nayla, mu zamu wuce Kaduna yanzu, amma zan dawo dan ganin halin da ki ke ciki. Kawai sai Nayla ta fara kuka, Jawad ya araso ya ri eta ya ce, Haba Hauwan Abiy meye na kukan kuma? Allah da na san zaki kuka bazan bari mu zo miki sallamar ba. Ga twiny ki a Kano kullum kuna tare, sannan ga Salma meye na damuwa kuma?. Yaya J Ina kewar Abiy, in ka je ka ce ina gaishe shi don Allah. Zan fa a masa, kema na san yana kawarki sosai. Ki share hawayenki kin ji?. Ido ta goge, tare suka raka su har gate bayan Jalila tayi mata alqawarin zuwa ta kwana suka tafi. Tare suka dawo cikin gidan ita dasu Salma, sai ta sake takura kanta, ta zauna shiru babu hira sai dai ta dinga bin su da ido. Shiru suka yi mata suna hira tsakaninsu amma bata saka musu baki. A haka har aka yi sallar la asar, suka tashi suka yi sallah bayan sun idar ne aka sake buga gidan. Salma ce ta sake zuwa ta bu e sai gata sun dawo da Didi. Nayla na ganin Didi sai ta murmusa domin gaba aya fuskar Didin ta koma mata ta Omaar. Ganin tayi murmushi sai Didi taji sanyi a zuciyarta araso a sanyaye ta ce, Nayla ya jikin?. Abinda ta fara tambaya kenan tun kafin ta zauna. Nayla ta ce, jiki ya yi sau i Didi. Amma na ga fuskarki tayi ja, kuka ko Nayla?. Salma ta ce, kuka tayi, su Mama ne suka zo yi mata sallama sun koma Kaduna, shine ta sha kukanta son ranta. Didi ta ce, to ki yi ha uri. Nayla sai tayi murmushi jin yadda Didin tayi magana a raunane. Didi ta kalle su ta ce, Jidda bamu gaisa ba. Jidda ta yi dariya ta ce, ai baza ma ki kula dani ba, kina ta sirikarki. Didi ta yi dariya suka gaisa gaba aya kana ta ce, ya gajiyar hidima?. Alhamdu lillah Didi. Ke ma ai za a yi miki ya gajiya, kullum sai kin fito daga wannan unguwar ta ki mai shegen nisa. Didi ta yi murmushi ta kalli Nayla ta ce, amma dai kin ci abinci ko?. Nayla ta ce, na ci Didi. Didi ta girgiza kai bata ce komai ba dan kunya take ji ta rasa abinda zata ce. Sai daga baya sannan ta ce, ban ma shiga ciki ba unguwarmu ba, nan na fara zuwa mu gaisa sannan na shiga. an murmushi suka yi babu wanda ce mata komai. Didi ta kalli Nayla ta ce, in akwai abinda ki ke so ki fa a min. Nayla ta ce, Babu komai Didi, kar ki damu. Didi ta sake yin murmushin ya e dan gaba aya ta rasa abinda zata yi. Duk suna lura da ita, ta kasa sakewa ba kamar yadda suka saba ba, su kam basa ganin laifinta ko ka an kawai dai itace ta tsargu. Hirar littafin baya da ura aka fara tsakanin Jidda da Salma har Didi ta saka baki Nayla ma haka sai hira ta bu e gaba aya suka fara hira da nisha Har aka yi i sha Didi tana nan, a sake kawo abinci daga gidan Hajja tare suka ci gaba aya. Harabar gidan suka fita ita da Jidda da Salma zasu rakata zata tafi gisq ta kalle su ta ce, na ce zan kawo Omar yau gashi bai yi ba ko? Ku yi ha uri ban ma yi magana dashi ba so nake sai gobe in sha Allah. Salma ta ce, Kar ki damu Didi babu komai, iya wannan wahalar da yake saka ki ma ai yana aukar ha inki. Ina gani gaba aya yanzu bakya sakewa damu kamar ba ke ba. Murmushi ta yi ta ce, Ku dai bawa Nayla ha uri don Allah, na san bamu kyauta ba nida Omar. Jidda tacce, urin me Didi? Omar fa ko yazo ba kallon Nayla zai yi matsayin matarsa ba, zama kana jin motsin wani shine amfaninsa kawai a gidan nan, amma baya ga haka bashi da amfani. Didi ta ce, zai yi amfani in sha Allah Jidda. Kuma na sanar da yaran sa komai akan auren, babu abu na cutarwa da zai shigo ta ofa ya cutar da Nayla in sha Allah. Dan unguwar nan kaf a san nan gidansa ne kuma matarsa ce a ciki, babu abinda zai same ta da izinin Allah. Salma ta ce, Allah ya amince. Amin Salma. Don Allah ki sake taya ta kwana kin ga bata da lafiya. Kar ki damu Didi. Na gode, Allah ya bar zumunci. Suka amsa da amin ta fita ta shiga motar mijinta. Tana shiga motar ta kalle AbdulHamid ta ce, Wallahi ban ji da in rashin zuwan Omar ba Yalla Ya ce, ba ina sane na ce ki yale shi yau ba, sai dai ko kin je yau in abinda ki ka bari jiya zaki tarar, ke ki ke fa i min zafin ransa shiyasa na tabbatar har yanzu yana tare da wannan acin ran. Gwara a bashi lokaci zuwa gobe, in sha Allah dani dake zamu je mu same shi zamu san ta inda zamu ullo masa in sha Allah. Didi ta ce, to Allah ya sa ya amince. Amin, zai amince ma in sha Allah. Ni ko ciki ban shiga ba Ina nan tun azu. Ko wajan Hajjan?. Wallahi, kunyar Hajja nake ji ne. Sai an daidai komai sannan zan samu nutsuwa. Murmushi ya yi ya ja motar suka bar unguwar. KRB3P004 ArewaBooks@nanahaleema11. Mama da suka koma Kaduna bata tarar da Abiy ba har suka yi baccin gajiya suka tashi Abiy baya nan. Sai bayan sallar i sha ta same shi a zaune a falon sa yana amsa waya. Kafin ya gama wayar ta kawo masa abinci da ruwan lemon da ta san yana sha sannan ta zauna a gefensa. Yana ajjiye wayar ya kalle ta ya ce, mutanen Kano, ashe kun dawo. Mama ta ce, mun dawo tun azu, lokacin da muka shigo baka nan. Jalil ne ya shigo a guje yana cewa, Abiy oyoyo. Abiy ya yi dariya yana cewa, Autana, ka tafi Kano ka barni ko?. Jalil ya ce, Zan koma wajan Yaya Nayla sai mu je tare ko?. Shikenan Jalil. Ya Kano?. Da da i Abiy. Abiy gidan Anty Nayla mai kyau yana ta hamshi. Abiy ya
Chapter 6 · 0% Book details