Sashe 110
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya ara masa kyau da kwarjini. Nayla bata san ta mi e tsaye tana kallonsa ba sai da ta ji afafunta sun tsaya cak. Murmushin da ya yi mata ya sake kashe mata jiki, da sauri ta arasa ta rungume shi ta ce, "gaskiya a fasa fitar nan, wannan kyaun da ka yi kallon ka za a dinga yi." ago ta ya yi daga jikinsa ya ja kumatunta ya ce, "Ni babu wanda zan kalla sai ke kawai. Mu je dare yana yi." Tare suka fito, ya kira masu gadinsa waya suka shigo suka bu e gate ya fita da motar suka fara tafiya ba tare da ta san inda zasu je ba. Hannunsa yana cikin nata yana tu a motar da hannu aya, juyowa ya yi ya kalle ta suka ha a ido, ya aga mata gira guda aya tayi dariya shi kuma ya auke kai yana murmushi. Nayla ta ce, "kamar ba kaine a gidan Didi ba, kamar ba kai ne mai cewa ina yi maka shishshigi a lamarinka. Naji tsoronka kamar mutuwata, amma yanzu kamar an canja ka. Dariya ya yi mai sauti yana cize bakinsa, ya sake kallon ta kafin ya auke kai ya cigaba da abinda yake yi bai ce komai ba. Hannunta da yake cikin nasa ya ago ya kai bakinsa ya sumbaci hannun ba tare da ya yi magana ba. Nayla ta bu e baki kamar zata yi magana sai ta fasa, ya sake kallonta yana antar da idanunsa tare da aga gira a lokaci guda ya ce, "fa i abinda yake ranki." Nayla ta yi dariya ta ce, "na i." Murmushi ya sake yi yana cigaba da tu a motar cikin nisha Babban gidan abinci ta ga ya tsaya, ta kalle shi ya kalle ta shima ya ce, "mu je." Tare suka fito zuwa ciki ya ri o hannunta suka shiga tare. Gaba aya sai ido ya dawo kansu, dan ba aramin kyau da dacewa da junan su suka yi. Yadda ya lura ana kallon su ana magana asa- asa ya saka shi aure fuska, ya jawa Nayla kujera aya ta zauna shima ya zauna. Waiter ce ta zo ta kawo masa menu ya kar a yana juyawa ganin shi bai ga komai a rubuce ba. Nayla tayi dariya ta kar asa- asa ta ce, "Scan ake yi, gaskiya YaMar sai mun zauna ni da kai mun tattauna, in ba haka ba zaka dinga bada ni." Murmushi ya yi ya ce, "ban ta a zuwa ba, yau in ma saboda ke ne kawai." Scaning in menu tayi ta mi a amsa wayarta ta ce, "Sai ka yi order abinda ka ke so." Bai kar i wayar ba ya ce, "ki siyi duk abinda ki ke so." Nayla bata i ba, ta fara dubawa tana fa awa waiter in ita kuma tana rubutawa har ta gama. Nayla tana ji daga table in bayanta ana ta muhawara, wata ta ce ta fi Omar kyau sauran sun ce Oma ya fita kyau. Kallon su ta yi ta kalle shi ta ga ya basar ya ora afa kan aya, sai hakan da yayi ya sake fitowa da masa kyau da kwarjininsa. Nayla ta ce, "Wa ancan matan sai yabon ka suke yi, ni kawai ka tashi mu tafi." Kallon ta ya yi fuskarsa a ha e ya ce, "Babu inda zamu je fa, sai kin ci abinda ki ka siya." Ba jimawa aka kawo abinda yi order aka ajjiye musu, da kansa yake bawa Nayla abincin hakan ya burge mutanen wajan. Abinda suka ci shida ita gaba aya babu yawa suka bar ragowar, aka kawo masa bill ya biya ya ri e hannun ta suka fita. Ya ga alama ta ji da in fitowar da suka yi, hakan ya yi masa da i ganin tana farin ciki, ta auka gida zasu tafi sai ta ga sun sake auke hanya. Abinda ya bata mamaki ganin sun tsaya a babban hotel in da ake ji dashi a garin Kano, ta kalle shi bayan ya ajjiye motar a cikin Car park in hotel ta ce, "Rouhii hotel fa." "na sani, fito mu je." Ba musu ta fita ya sake ri e hannunta suka shiga ciki. Yadda suka wuce direct ba tare da ya nemi aki ba sai ta yi tunanin ko wani ba o ya yi daga masu zuwa order in takalmansa ya zo da ita dan a tattauna. Elevator ta ga ya kunna yana kallonta, ta kalle shi bayan sun shiga ya matsa kusa da ita ya ce, "na saba shiga lift in na naje Abuja, naga kina kallona, to ki daina kallona." Dariya ta yi sosai ta kwantar da kanta a kafa arsa shima ya yi dariya ya danna floor in da zasu je. Floor 17 suka sauka, yadda wajan akunan suke a jere ya burge ta sosai, yana ri e da hannunta har ofar room in da zasu shiga. Ya auko card in a aljihunsa ya saka a ofar akin, bai mur a handle in ba ya kalle ta ya ce, "rufe idonki." Nayla ta kalle shi zata yi magana ya zagaya ta bayanta ya rufe mata ido ya bu ofar akin suka shiga ya mayar da ofar ya rufe. Ya kalle ta ya ce, "kar fa ki bu e ido, kar ki bu e na fa a miki." Nayla bata bu e ba, ta ji dai ya bar inda take ya an yi taku nesa da ita kafin ya ce, "To bu A hankali take bu e ido a daidai lokacin da wasu jajayen flowers suka zubo kanta, ta kalli saman ganin wata chandiliar light tana juyawa a hankali tana bada kaloli masu kyau. Kallon akin ta yi ganin an yi amsa ado da balloons jajaye ga kuma happy birthday sticker a rataye a saman gadon akin. KRB3P065 Nana haleema. Nayla ta shagala da kallon akin dan ya yi mata matu ar kyau musamman kan gadon da aka yi masa ado irin na gadon india, an yi atuwar heart da flowers an kuma rubuta Happy birthday Jidda a kan gadon. Ta kasa rufe baki saboda mamaki da farin ciki, kallon akin take yi tana ganin adon da aka yi masa mai shegen kyau. Ta juyo tana kallon inda yake tsaye sai ta ji ya shafa mata cream in cake a fuska, ta bishi da kallo tana murmushi mai nuni da tsantsar farin cikin da take ciki. Idanunsa take kallo kamar yadda yake kallon nata, ya aga mata gira aya ita kuma ta shagwa e fuska kamar zata yi kuka. A hankali ta ji sautin ki a, wa a tana tashi ka an-ka an, shiru ta yi tana sauraren wa ar da take tashi a cikin akin. _In dai a kan ki ne komai ki san zan yi shi, indai zan faranta ranki zan ci koda bashi, aikin arfi nayi ko zai tsaya numfashi, ko duka zana ci.. gare ki zan kai toshi, a aunaaa na tsunduma nake juree tsangwama, ina sonki an gama zan ci koda on rama, fito na yi sallama da juna mu runguma, indai kin tashi lafiya ni ina jin farin ciki. Na so ki, kema kin so ni.....na baki, kema kin bani...ni ban da abinda zan baki an mata....amma zan baki farin ciki cikin kwallata..cikin kwallata. Kyakykyawa, ke ce kyakykyawa...ke nake so, kyakykyawa yarinya kyakyautawa ke nake so._ ar Kyakykyawa ta Auta Mg boy kenan da take tashi ka an-ka an a akin. Nayla ta sauke numfashi zuciyarta ta nutse cikin farin ciki ji take kamar ta yi ihu saboda murya. Kallon cake in da yake hannunsa ta yi ta ga an rubuta abinda aka rubuta a jikin gadon, ta kalle shi a lokacin ya kai cake in bakin ta ya ce, "Barka da arin shekara Jiddana." Murmushi ta yi, ya ajjiye cake in ta fa a jikinsa ta fashe masa da kuka. Lokaci aya ya ru e, Calmly ya ce, "hakan bai miki ba ko? Ni ban ta a irin wannan abun ba sai yau, ban yi daidai ba?." Nayla ta ago tana kallonsa cikin muryar kuka ta ce, "ni haka na ce maka? Ka ji na ce bai yi min ba..?." Ya shafi hawayen fuskarta ya ce, "gashi ina ganin abinda na fi tsana akan kyakykyawar fuskar ki, in da ya burge ki baza ki yi kuka ba." Nayla ta ce, "YaMar!." Ya zuba mata ido kamar yadda take kallonsa ta ce, "ina sonka!" ta fa a tana sake komawa jikinsa tana kuka. Ya ce, "ni kukan da ki ke yi ya saka ina tunanin bai miki ba, tun azu abinda nake ta yi kenan kawai dan ki yi farin ciki. Ban san komai a kai ba, ban ta a yi ba, ban ta a zuwa ba, ko karo nayi da birthday party a social media ina wucewa bana kalla Jidda. Saboda ke azu da na gani na tsaya na kalla sai ya burge ni, na yi magana masu wannan decor in na ce ina so ayiwa matata zan bata mamaki, sune suka shirya min komai har cake in. Na so na saka ki farin cikin da zaki yi murmushi da fara'a, amma sai gashi na gaza kina kuka." Nayla ta share hawayenta tana kallonsa ta ce, "Kukan farin ciki nake yi Rouhii, in na ce maka ban yi farin ciki ba arya nake maka wallahi. Abin ya burge ni sosai, ban ta a jin da in wannan rana kamar yau ba, na rasa me zan ce maka shiyasa kawai nake kuka." Ya kalli idanunta ya ce, "ban yarda ba, kawai bai burge ki ba ne." "Wallahi ya burge ni, kukan murna nake yi ba kukan bai burge ni ba. Haba Rouhi wa za ayi wannan surprising in ace bai burge shi ba? Wallahi ya burge ni. Na ara sonka, na ara kishinka!. Ina sonka, ka saka naji farin da ban ta a ji ba, ka mayar da wannan rana ta musamman a rayuwata!." Murmushi ya yi yana share mata hawaye ya ce, "dama so nake ki yi farin ciki, ina so na yi miki abinda babu wanda ya ta a yi miki shi a duniya, ina so na saka ki farin ciki ta ko wacce hanya koda zan rasa abinda na mallaka ne, shiyasa na ata lokaci na