← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 205

Sashe 104

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da yaji a kan Narman ba komai bace akan wacce yake ji akan Nayla. KRB3P061 Nanahaleema Har cikin akin Mama Abiy ya shiga fuskarsa a aure sosai, ya kalle ta daga tsaye ya ce, "Me ya kai ki gidan Nayla? Ina ki ka ce min zaki je a Kano?." Mama ta kalle shi da mamaki ta ce, "dan na shiga Kano bazan je gidan ata ba? Akwai laifi dan na je gidan Nayla?." Abiy ya ce, "inda ace da zuciya aya ki ka je da bazan yi miki magana ba, amma duk abinda ki ka aikata ya dawo kunena. Meyasa ki ke son kashe auren Nayla bayan a lokacin baya ke kika bata goyan bayan aurensa?." Mama ta ce, "kamar ya ba da zuciya aya na je ba Abiy? To da zuciya nawa na je in ba da zuciya aya ba?." Abiy ya ce, "duk abinda ki ka aikata a gidan ya dawo kunnena Zeenatu, kin je kin fa i magana mara da i a gaban mijinta, kina cewa indai kina da rai sai kin raba aurensu, ba haka aka yi ba?." Mama bata musa ba ta ce, "Saboda bai dace da ita ba, ita ba kalar aurensa ba ce. Duk wani farin cikin gidan miji ita take siyawa kanta, aikin da take yi da shagonsu tana yi ne saboda taimakon kanta. Me yake dashi da zai iya ri eta?." Abiy ya bita da kallon mamaki ya ce, "kin san da hakan meyasa da ki ka bata goyan baya?." Mama ta kalle shi da mamakin abinda yace, ya aga mata kai ya ce, "na san ke kika zuga Nayla, ke kika fa a mata auren ta dashi abu ne mai yuwa tunda tana so, ki ka sake orata akan turbar zaki saka na amince ya aureta. Ki ka sakata ta amsa min tana sonsa, sannan da ki ka ga na yi fushi da amsarta sai kika saka ta tafi Kano, ni kuma ki ka ce min baki san ta tafi ba guduwa ta yi. Ki ka saka aka yi hacking WhatsApp account inta aka turo min messages in da take bayyana min in ban aura mata Omar ba zata shiga duniya. Ki ka dinga fa ar kalaman da zasu zuga ni na sake jin bana son auren kuma na yi fushi da ita, Ba a yi haka ba Zeenatu?." Jikin Mama ya yi sanyi matu a, ta kalle shi zata yi magana ya katse ta ya ce, "Kin fi kowa murna a lokacin auren, Nayla tana kwance bata da lafiya amma ke murna ki ke kina siyan kayan aurenta, kece kan gaba a kaita gidanta. Baki ta a fa a min alkhairi akan auren nan ba, kullum cikin kushewa ki ke. A bayan idanuna kuma kin fi kowa son aurenta dashi. Me ya saka ki ka canja yanzu kina ganin bai dace da ita ba?." Mama ta dake kamar ba ita ba ta ce, "ni fa ban gane akan wa ka ke magana ba, ni gaba aya ban fahimta ba." Abiy ya yi murmushin takaici ya ce, "meyasa ki ke son Nayla ta sha wahala a gidan aurenta? Dan kin ga yanzu tana cikin farin ciki ko? Kina ganin wanda ki ka raina kika tsaya kai da fata aka yi auren ya baki mamaki shiyasa ki ke so a raba auren?. Kin ga yanzu keda da Nayla ba ku da banbanci, kina cikin farin ciki, tana cikin farin ciki, babu abinda ya gagareki, babu abinda ya gagareta, ganin hakan shine ya jawo bakya jin da i a zuciyarki. Ba haka ki ke so ki gani ba, so ki ke Nayla ta wahala kullum ki kasnace mai taimaka mata. Haka ne ko Zeenatu?." Mama ta kalli Abiy cikin son oye yanayinta ta ce, "ni ka ke fa awa wannan maganar akan Nayla? Ni ce mai yiwa Nayla ba in ciki saboda kar ta samu jin da in gidan aure?." "Ke in fa Zeenatu!. Kin raini Nayla tamkar ar da kika haifa, kin bata tarbiyya daidai da ta Jidda, kin so ta, kin nuna mata auna, baki ta a barinta ta yi kukan rashin uwa ba. Amma daga arshe kin zobe ladanki, kin gaza arasa amanar da aka bar miki, kin gaza ri e amanar marainiya da Allah ya dam ata a hannunki, kin gaza cigaba da kula da amanar da mahaifiyarta ta bar miki. Mahaifiyarta ta amince dake ta bar miki arta guda aya da ta haifa a duniya, mahaifiyar Bilkisu tana da rai a duniya har yanzu, amma ta ce ita ke take so a barwa Nayla ki raine ta saboda ta yarda dake. Tana da an uwa maza da mata a duniya, amma ta ce ita da Zeenatu ta amince, a hannunki take so Nayla ta tashi. Anya baki ci amanar wacce ta amince miki ba?." Mama ta fara kukan borin kunya ta ce, "'ni ka ke fa awa bana so Nayla ta yi farin ciki? Ni na raini Nayla fa, na bata tarbiyya mai kyau, ni ka ke kallo ka ke cewa bana son ta yi farin ciki na fi so ta sha wahala?." Abiy ya ce, "ke in!. Duk laifin mahaifiyarta ne ya shafeta, mahifiyarta ta baki wahala saboda kin zo a bayan ta kina haihuwa ita bata haihu ba, kin manta kafin ta samu cikin Nayla ta ro eki afuwa kuma ki kace kin yafe mata ku ka daidaita zaman ku. Ta auki Ahmad da Jawad kamar yaranta, a lokacin da aka tabbatar kina da cikin Jidda ta sadaukar da lokacinta da komai wajan kula dake, ashe itama da cikin Nayla a jikinta ba a sani ba. Kin rigata haihuwa da sati biyu ta haihu, ku ka cigaba da kula da yaran a tare har Nayla ta kai shekara shida a duniya. Lokacin da mahaifiyarta Nayla take ciwon ajali me ta ce miki? Amanar Nayla ta bar miki a hannunki saboda ta yarda dake zaki kula da ita ko babu ranta. Ashe ke kin kar i amanar kula da ita ne saboda ta girma ki zuga ni na aurar da ita ga wanda bai dace ba, mu kaita inda zata sha wahalar rayuwa kamar yadda ki ka ana ka an a hannun mahaifiyarta kafin komai ya wuce. Ashe a fatar baki ki ka yafe mata, ashe baki yafe mata har zuciya ba ko Zeenatu!?." Mama kuka take yi domin ta san Abiy ya gama ganota, sai ta ji kunyar da bata ta a ji ba a duniya, kunyar ta mamaye mata zuciyarta da gangar jikinta, idanunta sun yi mata nauyi saboda tsananin kunyar da take ji, guiwarta ta sage ji take kamar ta zube a wajan saboda kunya. Musamman da ta ago ido ta ga Jawad, Ahmad, Jalila da Jidda a tsaye a bayan Abiy da alama duk sun ji abinda aka ce. Abiy ya girgiza kai cikin takaici ya ce, "Meye ribar ki in Nayla ta sha wahala a gidan mijinta? Wacce riba zaki zamu?. Kin manta kina da Jidda, kina da Jalila? Su ba mata ba ne..? Meyasa bakya tunanin abinda ki ke arin yiwa marainiyar da aka bar miki amana za a iya yi musu suma?. Kin manta su ma mata ne zasu iya fa awa irin gidan da ki ke so Nayla ta fa a? Ko dan kina ganin Jidda ta yi aure ta samu mai ku i bazata wahala ba? Ba ki san sakayya na iya canja komai ba ko Zeenatu?. Ba ki san alhaki kwikwiyo ba ne? Ba ki san duk antar ha i sai Allah ya fitarwa da wanda aka zalunta ba?. Kin san masifar da take cikin cutar da maraya? Kin tashin hankali da sakayyar da take cikin cutar da wanda bai yi maka komai ba?. Zeenatu kin san illar cin amanar wanda ya yarda da kai?." Mama bata ce komai ba kanta yana asa cikin kunyar anta da shi kansa Abiy in. Bata ta a jin kunya wani ba kamar yadda take jin kunyar Abiy da yaranta. Abiy ya kuma cewa, "Yanzu kun je gidan Nayla kin fa i magana mara da i, kin zagi mijinta, kin fa i magana wacce bai kamata a ji ta a bakin ki ba matsayinki na uwa a gareta. Yanzu da ya biyewa zuciya ya rama abinda kika fa a masa da bai cuce ki ba?...." Ya ara fa a yana binta da kallo ganin ta kasa ko motsin kirki. Abiy ya girgiza kai ya ce, "yaron da yake amsa sunan siriki a gare ki ya bu e baki ya fa a miki magana mara da i a gaban arki ai ya gama cutar da ke. arki Jalila har fa a miki ta ke yi, tana cewa Mama hakan bai kamata ba amma sai ki ka mare ta saboda bakya a fa a son gaskiya, idanunki ya rufe burinki kawai Nayla ta sha wahala. Kin je kin ga ba wahala take sha ba hankalinki ya tashi ba haka ki ke son gani ba." Abiya ya sauke numfashi ya ce, "Wallahil azim kin bani mamaki matu a, na auka in ki ka ga maciji zai sari Nayla zaki shiga ki kare ta ya sare ki a madadinta, ashe ke ce macijin da ki ke kai mata rasa. Kin zuga ni an yi auren nan ba tare da laifin Nayla ba, na gano hakan nayi miki shiru saboda ke uwace a gare ta har gobe, kin yi mata abinda ko wacce ta haife ta bata yi mata ba shiyasa na yaleki. Na san ke kika saka aka turo min text in da ya tunzura ni har na kai ga aura mata Omar, na san ke kika shirya komai, kallon ki kawai nake yi. Duk abinda ki ka yi bai ishe ki ba, sai da ki ka auki afa har gidanta ki ka je dan kawai ki tarwatsa mata farin cikin da ke ciki, Hakan a gare ki daidai ne ko?." Abiy ya kalli Mama inda take kallo tana kuka, ya juya ya ga yaranta ne gaba aya a tsaye jikinsu ya yi sanyi. Abiy ya nuna su ya ce, "ko kun san itace ta saka na aurar da Nayla ga Omar?" Ya fa a yana auko wayarsa ya shiga whatsapp ya mi awa Ahmad ya ce, "karanta wannan." Ba musu ya kar a
Chapter 104 · 0% Book details