← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 205

Sashe 76

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kasuwancin na ka?." Omar ya ce, "Alhamdu lillah Abiy." "Haka ake so." Nayla ta kalli takalmin afar Abiy ta ce, "Abiy takalmin afarka ma product in mu ne." Abiy ya kalli afarsa ya kalle ta da mamaki ya ce, "Da gaske?." Nayla ta ce, "Allah da gaske." "Shagon ku na je wancan satin sai na ganshi ya burge ni sai na ce a bani, ai ban san na ku bane." "Eh Abiy, ina bayar ana kawowa, ana siyansa sosai a nan Kaduna." Abiy ya ce, "Ma sha Allah. Omar Ashe haka takalman na ku suke da kyau?." Omar ya yi murmushi bai ce komai ba. Abiy ya ce, "Abinda zai faru mu ma a fara kawowa storea in mu, na tabbatar za a siya sosai. Zan yi waya da wanda zai zo ya kar a, za a raba states in da shopping complex in suke. Amma muna son pieces da yawa gaskiya, dan wannan takalman da wuri za a neme su a rasa." Omar ya yi murmushi ya ce, "i sha Allah." Abiy ya ce, "gaskiya takalman suna da kyau, babu wanda zai ce na gida ne kuma hannu ne yake yi. Allah ya arawa nema albarka." Omar ya ce, "Amin ya rabbi, An gode Abiy." Jawad ne ya shigo Abiy yake yi masa maganar takalmin har yake nuna masa. Jawad ya ce, "Nima da na auka sai da abokai na da yawa suka siya, gaskiya yana da kyau sosai. Omar Allah ya aro kasuwa." Ya amsa da amin amma baya ara ko wacce magana daga amin in nan. Omar ya kalli Abiy da girmamawa ya ce, "Abiy zamu koma Kano." Abiy ya ce, "da wuri haka? Na auka sai gobe." "Ba mu taho da shirin kwana ba, daman mun zo ne dan ka saka mana albarka kuma mun samu, na kawo ta dan mu tabbatar da ka daina fushi da ita da auren gaba aya." Abiy yayi murmushin jin da in kalaman Omar, hakan da ya yi ya ara masa girma a idanun abiy sosai. Abiy ya ce, "Ai kam gwara ku tafi, ban cika son tafiya in dare ya yi a hanya ba." Nayla ta ce, "Abiy Ina Mama?." "Bata nan ta fita, gashi har zaki koma baku ha u ba. Amma na san zaku dawo ai." Nayla ta ce, "na so na ganta." Nayla ta mi e ya shiga ciki dan ta yi missing akinta. Sama ta hau ta shiga akin ta komai yana nan yadda yake har kayan ta akwai ragowa a cikin wardrobe. Jalila ta shigo suka rungume juna suna ta murna, Nayla ta ce ta bata pad ta auko mata ta canja, duk abinda take so sai da ta auka sannan ta sakko. A tsaye ta same shi shida Jawad suna hira kamar sun san juna, ta ga dai ledodin company su Omar a hannun Jawad amma bata san meye ba, sannan ga apples da manyan watermelons a ajjiye, Nayla bata ka kawo a ranta Omar ne ya kawo ba ta araso wajan. Abiy ta gani ya fito da kansa dan yi musu rakiya; Nayla ta rungume shi ya dafa kanta ya ce, "Allah ya kiyaye hanya, in na shigo Kano zan zo har gidan na ku in sha Allah." Nayla ta ce, "Abiy ka gaishe da Mama don Allah, ina ta kiranta bata auka." "In sha Allah zan fa a mata." Abiy ya kalli Omar ya ce, "Omar Allah ya kiyaye hanya." Omar ya urkusa har asa a karo na farko a rayuwarsa yana yiwa Abiy sallama amma Abiy ya mi a masa hannu dole suka gaisa. Jawad ya ce, "Abiy ga sa o Omar ya bayar na ka da Mama harda ni ma." Abiy ya yi murmushi cikin farin cikin da ya mamaye masa zuciya ya ce, "Omar harda hidima kamar ba o?." "Babu yawa Abiy, a saka mana albarka." "Mai yawan kenan, an gode sosai, Allah ya arawa nema albarka." "Amin Abiy, Mu ne da godiya, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya ara girma." "Amin ya rabbi, Allah ya kiyaye hanya." "Amin ya rabbi." Nayla tana jikin Abiy har lokacin ya ce, "To Nayla, a gaishe da Hajja." Nayla ta ce, "Zata ji Abiy." Ma'aikatan gidan ne suka zo wajan ganin Abiy yana tsaye, ya kalle su ya ce, "Ga mijin Nayla fa, na san ba ku san shi ba." Nan da nan aka fara gaisawa da Omar yana amsawa. Kusan ma'aikatan gidan kaf sai da suka zo suka gaisa kafin su tafi. Mota ta shiga daman shi ya jima a ciki aka bu e musu gate suka fita daga gidan. Abiy ya kalli Jawad da yake ta murmushi ya ce, "Hundred percent na amince da auren Nayla da Omar, addararta alkhairi ta za a mata." Jawad ya ce, "Daman ni Abiy tun farko na amince dashi sosai, na tabbatar da baza ta yi kuka a aurensa ba. Allah ya basu zaman lafiya." Suka amsa da amin Abiy ya koma ciki. KRB3P042 Tafiya suke yi Nayla na murmushi, ko babu komai ta san yanzu mahaifinta baya fushi da ita kuma ya sakawa aurenta albarka. Farin ciki take ji sosai yana ratsa sassan jikinta ta kasa oye farin cikin ta. Shi dai yana kallon ta dan shi kansa yana jin farin ciki, ko babu komai ya sauke wani nauyi da ya ke a kansa, ya kuma tabbatar da mahaifinta yana goyan bayan aurensa da ita. Bata yi magana ba shima kuma bai yi ba, haka suka tafiya motar shiru ko radio babu balle ta auke musu kewa. Kowa bugun zuciyarsa yake ji a kunne sa bayan wannan dukkan su sun kasa furta komai. Sai yamma sosai suka shiga Kano, a ofar gate yayi parking ta auki jakarta shiga cikin gidan. aki ta wuce kai tsaye tayi wanka ta canja kaya ta zauna da niyar ta huta bacci ya auketa. Sai bayan magriba ta farka ta tashi tana yamutsa fuska ta kalli agogo, ganin lokaci ya tafi sosai ya saka ta mi e ta koma aki ta sake yin sabon wanka ta shafe jikinta da turare ta saka kaya marasa nauyi ta fito falo. Tana fitowa yana shigowa suka ha a ido, sai ta yi murmushi ta ce, "Sannu da zuwa." Murmushin shima ya yi mata amma ya auke kai daga kallonta ya ce, "Yauwa, k in sha bacci." Nayla ta yi murmushi ta ce, "ban san ma nayi baccin ba, me zan dafa maka?." Kai ya girgiza mata ya ce, "ki bar shi." Nayla ta kwa e fuska cikin shagwa a ta ce, "Haba YaMar, wai ban iya girki ba ne ya saka baka son cim abincina ko kuma laifi nayi maka? Ko yaushe na ce ga abinci sai ka ce baka ci." Yadda take maganar da muryar da take amfani da ita kamar zata yi kuka ya saka ya kalle ta ya auke kai bai ce komai ba. Ta matso kusa dashi ta ce, "ka fa a min abinda zan dafa maka." Ya lura da farin cikin azu yana nan a kan fuskarta, ya ce, "kin gaji, ba sai kin yi girki ba." "Ai na huta tunda na yi bacci, ka fa a min abinda zan girka maka." Shiru ya yi dan bai san me zai ce ba, shi baya jin yunwa amma in ya fa a ya san baza ta amince ba. hamshin turarenta gaba aya ya gama kashe masa jikinsa, ya kulle ido ya bu e, kafin ya yi magana ta ce, "Ka fa a min." Ajiyar zuciya ya yi ya kalle ta ya ce, "ki dafa duk abinda ya yi miki." Murmushi ta yi ta ce, "To" ta fa a tana juyawa ta shiga kitchen ya bita da kallo yana kulle idanunsa. Waya aka yi masa ya auka ya magana akan aikin kasuwancin su da abubwan da ya shafi haka. Ya jima yana wayar har ta gama dafa jollof na superghetti ta kawo masa a lokacin ya kashe wayar. Ya kalle ta ya ce, "Abiy yana gaisheki, ya kira ki kina bacci." Nayla ta auki wayarta da take gefe ta duba ta ce, "Ai kam ga kiran shi, harda Ya J." Ta fa a tana kiran Abiy, yana jinta suna waya tana shagwa a shi dai ya auki abincin yana ci. Ya yi masa da i sosai, amma cikinsa gaba aya babu space kawai yana ci ne dan saboda kar ta ce bai ci ba. Tana gama wayar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya share bai ce komai ba. ta ce, "Abiy ya ce a gaishe ka." "Ina amsawa." Ta asan ido ya kalle ta ganin ita bata cin abincin ya ce, "Ina na ki abincin?." Nayla ta rausayar da kai ta ce, "kai ka ai na dafawa ai, ni bana cin abinci da daddare." "Yau zaki fara, zo ki ci" ya fa a yana nuna mata wanda yake ci. Nayla ta girgiza kai ta ce, "Allah bana ci...." Kallon da ya yi mata yana tafiya da idanunsa kamar zai kulle sai ya bu e akan fuskarta ya hanata arasawa. Matsowa tayi kusa dashi a hankali ya ce, " auki ki cinye." Nayla da shagwa a ta ce, "ya yi min yawa." "Ko dai bakya cin wanda na rage?." Ai da sauri ta auka ta fara ci yayi murmushi mai sauti yana kallonta. Daman bata da yawa ta cinye ta sha ruwa yana kallon ta amma bai ce komai ba. Tashi tayi ta kai bowl in kitchen a ta dawo bata same shi ba ya tashi. Ta kama ugu tana kallon akinsa ta ce, "Shi wai wannan haka ne soyayyar ko ne? Sai dai ya kafe ka da ido kamar zai cinyeka?." Wayarta da aka kira ya hanata cigaba da mitar da take yi a zuciyarta. Ganin Yaya Ahmad ya saka ta auka suka gaisa yana tambayarta tana bashi amsa cikin nisha i. Ya Ahmad ya ce, "Ina mijin na ki? In yana nan bashi mu gaisa." Nayla ta ce, "to bara na kai masa." Katse kiran ta yi ta nufi akinsa. Knocking ofar akin ta yi bata ji ya yi magana ba, sai ta bu e ta same shi a tsaye yana kallonta. Nayla ta ce, "Ya Ahmad ne ya ce na kawo maka waya za ku gaisa, Baban yayana." Baice komai
Chapter 76 · 0% Book details