Sashe 109
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abinda nake so ki kare martabar aurena a kan ki shikenan." Nayla tayi aramar dariya jin abinda ya ce, wai shi ba aikinta ne ba ya so ba zuwan ta ne baya so. Ya furta abinda yake zuciyarsa ba tare da ya san ya furta ba saboda kishi. Nayla ta dafa hannunsa ta ce, "Rouhii ni fa na ajjiye aikin nan, kuma a dangina babu wanda zai zarge ka balle maganar da ka fa a ta tabbata. Na sanar da Abiy zan ajjiye aikin ya ce to daman ni na nace sai nayi. Ina so na kula da kai, ina so na samu ladan aure in ina zuwa wajan aiki bazan samu ba. Kuma ka ga muna da shop ni da Twiny, yanzu haka daga Cairo ta dawo ta siyo mana dogayen riguna da za a zuba a shop in, komai gana going fiye da tunanika, kaga ai Alhamdu lillah!." Ya zuba mata ido yana kallon ta bai ce komai ba hakan ya saka ta girgiza hannunsa ta ce, "Allah ni na bar aikin nan Rouhii!." Ajiyar zuciya ya yi yana kallon ta ya ce, "Jidda ban cutar da ke ba? Kar garin faranta min rai ki cuci kan ki." "Ni baka cutar da ni ba, ra'ayin kaina ne ya saka na yi." "Kin tabbatar?." "Na tabbatar maka. Wallahi na ajjiye aikin nan ne saboda ina so na samu ladan aure kamar ko wacce mace, shine kawai." Ya girgiza kai ya ri e hannunta gam ya ce, "Na gode Ashiq, na gode miki. Yadda ki ka ajjiye abinda ki ke so saboda ni in sha Allah sai na samar miki da ninkin abinda ki ke so, zan samar miki da abinda baki ta a nema ba Jidda. Allah ya sani bana son aikin nan saboda tsananin kishinki da nake yi, kishinki nake ji mai tsanani, yadda nake ji a kan ki bazan iya kwantata miki ba. Kullum fargabata ranar da zaki koma aiki, dan ba tabbatar in kika tafi bazan iya numfashin kirki ba saboda kishi Ya ja numfashi ya sauke ya ce, sai ga shi kin ajjiye saboda ni kawai, Da me zan saka miki?." Ta yi murmushi ta ce, "Sai ka bu e Babban company mai suna Exclusive footwear by tiger a lokacin zan zama MD inka kai kuma kana C.E.O, ka yarda?." Murmushi ya yi ya rungumeta ya ce, "Allah ya tabbatar Ashiq!." "Amin Rouhii." "Na gode." "Nima na gode." Lumshe ido ya yi cikin tsnana KRB3P064 Nanahaleema A gida Omar ya yini, sai azahar ya fita ya je shago saboda akwai sabon sample in takalmin da yake so ya gwada a gani. Bayan fitarsa mai aikinta tazo ta gyara ko ina ta tafi, ita kuma tana zaune tana chat kiran Yaya Ahmad ya shigo wayarta. Ta yi dariya ta auka ta ce, "Yaya ina yini." Daga can angaren ya ce, "Nayla kin yini Lafiya?." "Lafiya lau Yaya, Ina Anty Halisa?." "Taje Unguwa, Ya mijin naki?." Nayla ta ce, "lafiya lau." "Nayla ki yi ha uri da abinda Mama ta zo tayi kin ji?." Nayla cikin rashin jin da i ta ce, "kai Yaya ha uri kuma? Wallahi babu komai ni manta ma, na tabbatar ranta ne a ace shiyasa. Amma Mama t a fi kowa son na samu abinda nake so." Yaya Ahmad ya ce, "ki dai yi ha uri, shima mijin na ki zan kira shi na bashi ha uri." Nayla a sanyaye ta ce, "Don Allah Yaya ka daina fa ar haka bana so." Yayi murmushi ya ce, "Shikenan Nayla, yaushe zaki shigo Kaduna?." Nayla ta ce, "Na kusa in sha Allah." "Abiy ya ce min kin ajjiye aiki, na ce daman ai ke kika nace sai kin yi, waye ya fa a miki ha a aiki da aure yana da sau i?." Nayla ta yi dariya ta ce, "ai na ha ura yanzu kam Yaya, gobe ma nake so na je na kai letter, bazan iya wahala ba." Yaya ya ce, "Allah ya kaimu, iya shop in ku ya ishe ki, me zaki yi da ku i ne ma?." Nayla ta dinga dariya ta ce, "Yaya abinda ake yi da su mana." Hira suka cigaba da yi kafin ya kashe wayar. Kiran Jawad ya shigo, ta auka shima maganar farko ha urin ya bata, sai da ta fara kuka tana cewa ita a daina yi mata haka sannan ya canja maganar ya ce, "guess what.....yau birthday ki." Nayla ta wara idanu waje ta ce, "Lahh Ya J ni na manta ai, yanzu yau birthday na?." Jawad ya ce, "ai na san kin manta shiyasa na kira na fa a miki." "Kai amma na ji da i wallahi, sai ka shirya min gift in da zaka bani." Jawad yayi dariya ya ce, "gift in da zan baki shine zan auri awarki Salma, cikin week in nan ma su Abiy zasu zo kano." Nayla ta ce, "wai maganar har tayi nisa haka ban sani ba?." "Daman kin sani ne?." "Kaima ka san ta ya wannan ala a zata ullu ban sani ba?. Amma Salma munafuka ce, jiya ta zo muka gama hira bata ce komai ba. Kai amma na ji da i wallahi Ya J, Allah ya nuna mana lokacin. Wayyo Allah da i, gaskiya ka bani babbar kyauta." Murmushi ya yi suka cigaba da hira kafin ya kashe wayar. Kamar a jere suke kiran ta, sai ga kiran Jidda da ta auka bata bada damar bata ha uri ba ta fara yi mata hira da zancen birthday da kuma zancen Salma da Jawad. Tana kashewa wayar Mama ta kira amma Mama bata auka ba, sai ta kira Abiy ta fa a masa batun birthday ta, tana kashewa ba jimawa Salma ta kira suka cigaba da hira cikin nisha i da farin cikin da take ji a zuciyarta. A wannan yanayin Omar ya dawo ya tarar da ita, yana zama ta ce, "Rouhii ka san meye?." Ya girgiza kai alamun a'a ta ce, "ashe yau birthday na ban sani ba? Yau na cika shekara 25 a duniya. Yaya J ne ya yi min albishir." Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce, "Sannu da zuwa shekara ashirin da biyar." Ta kalle shi jin abinda ya ce suka ha a ido ta shagwa e fuska ta ce, "abinda zaka ce kenan?." an ta e baki ya ce, "to me ake cewa? Ban san me ake cewa ba. Duk lokacin da shekarar haihuwata tazo Didi tana cewa Allah ya arawa rayuwa albarka, kema Allah ya arawa rayuwarki albarka." Tayi murmushi mai sauti ta ce, "Amin. yaushe ne date in birthday na ka?." "Oho, waye ya sani? Tambayi Didi." Nayla tayi dariya ta ce, "Na fa awa Abiy dan ya tanadi gift in da zai bani, bara na yi tunani na ga me zan ce masa ina so? Uhummm sai dai na yi lissafi na gani." Shi dai kallon ta yake yi ganin tana magan ita ka ai dan bai saka mata baki ba. Calmly ya ce, "Har kyauta ake ha a miki?." Nayla ta kalle shi ta ce, "sosai ma kuwa. Last birthday na shine Abiy ya bani tsohuwar motata ta gida, Ya J ya canja min wayar da ka tsorata ni ta fashe a gidan Didi...." Ta arasa fa a tana ar dariya, ta kuma cewa, "Yaya kuma daman shine an I don't care, da na fa a masa sai ya ce to barka da ara shekara" ta fa a tana dariya ba tare da ta kalle shi ba. Girgiza kai ya yi yana murmushi amma bai ce komai ba, ta cigaba da lissafin ta yana ji amma bai ce mata kanzil ba. Tashi ya kuma yi ya fita bayan yace mata zai dawo anjima kar ta ce zata dafa abinci. Nayla ta zauna kawai tana aikin chat dan babu abinda take yi. Sai yamma ya dawo ya shigo ya same ta a zaune a aki tana video call da Jidda. Da ya shigo sai ta katse kiran ta kalle shi ta ce, "YaMar akwai abinda yake damunka ne?." Ya girgiza kai ya ce, "Babu komai, Me ki ka gani?." "Ka canja, ko magana baka yi sosai." "Hmmm! Kina ji...ki shirya in an idar sallar i'sha zamu je wani waje." Nayla ta ce, "Gidan Didi?." Ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "gidan Didi ne kawai wajan zuwan mu?." Ta yi dariya ta ce, "to na ga can mu ke zuwa ko?." Hararta ya yi ya ce, "ke dai ki shirya kawai." Nayla ta ce, "Tom." Kai ya aga kawai ya zauna yana kallonta. Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "idanunka suna sakawa na ji wani iri YaMar." Yayi murmushi ya ce, "zo ki ji." Ba musu ta tashi ta arasa inda yake, ta ri e hannunsa da ya mi a mata ya zaunar da ita a jikinsa ya ce, "meye a idon nawa?." "Suna da girma sosai, kuma ina ganin kamar wani abu kamar gold haka a ciki, in na kalla sai naga kamar abin na shiga idona. Kwarjini idonka yake min." Murmushi ya sake yi yana sauke numfashi, ya kulle ido ya bu e ya ce, "Haka dai ki ka ce." Nayla ganin baya son magana sai ta yi shiru tana jikinsa a zaune baya cewa komai, sai da aka kira sallah sannan ya yaleta ya fita sallah. Sai bayan i'sha ya dawo ya same ta ta shirya cikin black abaya ta yi rolling kanta ta yi matu ar kyau. Murmushi ya yi ya tako inda take ya yi mata peck a goshi ya ce, "kin yi kyau." Murmushi ta yi ta ce, "Kaima ka yi kyau." "Anya zamu yi fitar nan? Kyaun da ki ka yi yayi yawa." "Kuma dai ka ga abaya na saka." "Shigarki ta yi ai, kawai kyau ki ka yi kamar balarabiya." "Sai ka ce kai?." Murmushi ya yi kawai tare da ajiyar zuciya ya ce, "ina zuwa" ya fa a ya shiga aki ta zauna a inda take tsaye tana cigaba da danna wayarta. Bai jima ba ya dawo inda take zaune, ya canja kaya zuwa black in maroccon caftain mai matu ar kyau da laushi, ya saka hula kalar aikin jikin kayan ta zauna daram a kansa, kwantaccen gashin kansa da ya fito a bayan hular