Sashe 145
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rouhi!. Firgigit ya farka yana sauke numfashi zufa ya gama lullu e masa jiki kamar akin babu fanka. Jikinsa rawa yake yi sosai, tashin hankalin da bai ta a shiga ciki ba ya mamaye masa zuciyarsa da gangar jikinsa. Baya cikin nutsuwarsa ko ka an, jikinsa rawa yake yi gab gab gab yana zare ido yana kallon akin kamar mai son gano wani abun. Nayla tana tsaye tana kallon sa cikin tsoro, daga ban akinta ta ji yadda ya kira sunanta da arfi ba shiri ta auro towel ta fito, tana shigowa ta same shi jikinsa yana rawa yana juya kai gumi ya gama wanke masa jikinsa. Nayla ta zauna a kusa dashi ta ce, YaMar lafiya ka ke? Ta fa a a gigice tana kallonsa ganin kamar a firgice yake. Idanu ta ga ya zuba mata yana kallon ta, har lokacin bai dawo nutsuwarsa ba, a gigice yake kamar zararre. Ganin yadda yake kallon ta sai ta ora hannunta akan fuskarsa ta ce, lafiya ka ke?. Kamar ta tuna masa, ya zubura ya jawota jikinsa. Wata irin runguma ya yi mata har yana mi e guiwarsa akan gadon, yana sake jawota jikinsa yana sake matse ta yana wata irin ajiyar zuciya ya kasa furta komai. Nayla ta ce, YaMar ka matse ni ta fa a da yar jin numfashinta yana neman aukewa jin yadda ya matse ta. A hankali ya sake ta ya mi e tsaye ya ri e hannun ta yana kallon ko ina na jikinta. Nayla ta bishi da kallo ganin yana are mata kallo kamar bai santa ba. Towel in jikinta yake son kwancewa ta ce, YaMar lafiya ka ke? Me ya faru ne haka? Ta fa a tana ri e hannunsa ta hana shi kwance towel Bai saurare ta ba ya cire towel in, ya zubawa cikin ta ido yana kallo ganin yana nan yadda yake babu abinda ya same ta. Nayla ta auki towel in ta aura tana kallon yadda yake binta da kallo kamar zararre. arin barin wajan tayi da niyar samo masa ruwa ya ri o hannun ta ya ce, a Jidda, kar ki je ko ina, ki tsaya a tare dani ya fa a yana jawo hannunta da hanzari ya sake matse ta a jikinsa yana juya kai a jikinta ya rasa yadda zai sarrafa abinda yake nu usar zuciyarsa. Ganin kamar baya cikin hankalinsa sai Nayla ta saka hannunta a bayansa tana shafawa a hankali ta ce, Shikenan ina tare da kai, ka zauna na kawo maka ruwa ka sha. Bai iya sakinta ba tana irjinsa har lokacin yana sauke numfashi a wahale. A hankali ya ago kansa ya kalli fuskarta, ya ri e fuskarta da duka hannayensa yana girgiza mata kai. Nayla ta ce, Rouhi mafarki ka yi?.. Ya kasa bata amsa sai kallon ta da yake yi kawai, ta ri e hannunsa suka zauna a gefen gadon ta ora hannunta a fuskarsa ta ce, ka yi mummanan mafarki ne?. Bai bata masa ba ya kifa kansa a kafa arta ya ce, Kar ki tafi Jidda, kar ki je ko ina. Murmushi ta yi tana shafa kansa da taji yayi zafi tana arin samar masa nutsuwa. Sai da ta ga ya an nutsu har ya ago daga jikin ta sannan ta ce, ka taso ka yi wanka ka ci abinci. Naji kanka ya yi zafi, sai ka sha magani. Bai musa ba ta ri e hannunsa har ban akin, zata fito ya hanata dole ta tsaya har ya kammala suka fito, har ya shirya hannunsa yana cikin nata. Tare suka fito falo ta bashi tea ta zauna a kusa dashi ko kaya bata saka ba har lokacin towel ne a jikinta. A hankali yake shsn tea iin kamar mara lafiya, bayan ya gama ya kwantar da kansa a kan cinyarta yana jin zuciyarsa kamar zata fito waje saboda bugawar da take yi. Nayla tana shafa kansa a hankali ta ce, mafarkin me kayi da ya firgita min kai haka?. Ajiyar zuciya yayi yana kwance a jikinta ya ce, mafarki nayi sai ya kasa fa a, ya tashi zaune ya kalle ta ya ce, wai ana fa an daba an kashe su Bashir. Nayla ta ce, mafarki ba gaskiya bane Rouhi, duk yadda aka yi da zaka kwanta baka yi addu a ba kuma bayan sallar asuba baka yi azhkar ba ko?. Gudun kawar mata da zargi sai ya aga kai alamun eh, ta ce, kaga illar kwanciya babu addu a, sannan ka ga illar rashin yin azhkar. Ka kwantar da hankalin ka, babu abinda zai faru. Ya aga mata kai yana kallon idanunta kamar aramin yaro. Ta yi murmushi ta ce, arfin kiran sunana da naji kayi ina wanka na fito babu shiri, ni na auka ma ni kayi mafarki an kashe ta fa a tana dariya tana kallonsa. Wani irin bugawa irjinsa yake yi, tsoro da fargaba ya gama mamaye masa zuciya da ganganar jikinsa. Bashi da nutsuwa ko ka an, ari yake ya nutsu saboda itama ta nutsu, baya so ta ji maganar shiyasa ya oye mata dan lamarin ba abinda za a fa a bane, baya so ta dalilin aurensa ta dinga shiga tashin hankalin akan abinda bata ji ba bata gani ba, lokacin da ya aikata bai santa ba. Nayla tayi pecking insa a goshi ta mi e ta shiga aki. Da hanzari yabi bayanta, sai ganin sa tayi kamar an cillo shi ya shigo. Ta bishi da kallon tsoro ta ce , Anya Rouhi iya mafarki nan ne yake damunka? Gaba aya ka ru Bai ce komai ba ya sake jan hannunta ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya idanunsa a kulle. Nayla ta raba kanta daga jikinsa ya ri e hannunta har wajan kayanta, da kanta ta auko ta saka tana yi tana kallonsa kamar yadda yake kallon ta. Tana gamawa ya yi murmushin arfin hali ya ce, zo mu je ki ci abinci. Bata musa ba suka fito falo ta ci abinci tana ci tana kallonsa kamar yadda ya kafa mata idanu yana kallo. Fita yake so ya yi amma bazai iya tafiya ya bar ta ita ka ai ba, yana so ya je ya yiwa tufkar hanci, dan ya tabbatar mafarkinsa zai iya zama gaskiya. Dabara ta fa o masa ya ce, kwana biyu baki je gidan Yayarki ba. Nayla da mamaki ta ce, wace?. Mai sunanki. Wai Twiny?. Ya aga mata kai alamun eh. Nayla ta ce, nayi niyar zuwa, na san baka son ina fita shiyasa na ha ura. Da hanzari ya ce, tashi ki shirya na kai ki. Nayla ta bishi da kallo ta ce, haka kawai ka ji a ranka kana so ka kaini gidan Twiny?. Omar ya ce, ba dai kina son zuwa ba?. a bana so ta bashi amsa tana kallonsa. Omar ya ce, Fita zan yi, kuma bana so na bar ki ke ka Nayla zata yi magana ya ce, auko hijjab mu je na kai ki, in anjima zan dawo da kaina na auko ki. Nayla ta dinga kallonsa da mamaki a haka ta auko abinda zata auko ta fito, da kansa ya ri e hannunta har mota sannan suka tafi. Ko a motar hannunsa yana cikin nata, abu ka an ya kai hannunta bakinsa ya sumbaci hannun ko ya ora shi akan fuskarsa ko irjinsa. Ita dai kallonsa take yi har suka je ofar gate in Twiny. Ya tsayar da motar ya kalle ta ya ce, kar ki fito ko bakin gate sai lokacin da na ce miki nazo, sannan in kin shiga kina zama a falo ki kira ni ki ce kin shiga. Nayla ta ce, Rouhii anya lafiya? Kodai wasu ne suka sake arin Ya ora hannunsa a bakin ta ya ce, shiii! Ki yi abinda na ce kawai. Ta aga kai alamun to. Ya taso daga kan kujerar ya yi kissing bakin ta sannan ya bari ta fita. Shima fita ya yi har bakin gate in, mai gadin ya bu e mata ta shiga yana kallon ta yana tsaye a wajan. Sai da ta shiga ta kira shi kamar yadda yace sannan ya hau mota kai tsaye ya wuce gidan Didi. Sai da yaje ofar gidan sannan ya kira ta, sai da yaga ta bu e gate in sannan ya fito daga motar ya shiga ciki. Bayan sun zauna ta ce, nayi tunanin tare da Nayla ku ke. Ya yi shiru bai ce komai ba ta ce, Ya dai?. Ya an sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, ina Marmerh?. Bacci take yi, tana aki. Me ya faru ne?. Didi suna son kashe Jidda ya furta ba tare da ya kalle ta ba. Didi ta dafe irji ta ce, innalillahi wa inna ilaihir raji un! Kuma dai? Me ya kuma faruwa?. Bai oye mata ba ya fa a mata komai har mafarkin da yayi. Ya an yi shiru kafin ya ce, Hankalina ya tashi Didi, ban ta a jin tashin hankali kamar yadda nake ciki a yanzu. Tunda har abin ya kai ga mafarki mai munin wannan na tabbatar da akwai abinda yake shiryawa. Me cikin ya tsarewa aura? Meyasa bazai huce haushinsa a kaina ba sai a kan ciki jikinta?. Didi ta girgiza kai tana jinjina lamarin ta ce, To kai meyasa ka zubarwa da matarsa ciki?. Ya kalle ta ya ce, haka kawai sai na zubarwa da matarsa ciki? Ya akayi ma na san tana da ciki harda zan zubar?. Kawai an samu incident ne har cikin ya fita ta dalilina, amma ni a lokacin ko yatsan hannunta ban jiwa ciwo ba. Ya akayi ya san Nayla tana da ciki?. Abinda ya aure min kai kenan, na rasa ta inda ya san tana da ciki har yazo aukar fansa akan cikin ta. alamun ana bibiyar duk abinda ka ke yi kenan, ana bibiyarka itama ana bibiyarta. Babu lallai mutum aya ne, wata ila akwai masu da yawa Omar. Omar ya ce, na sani Didi, na san hakan zai iya faruwa. Ni na san masu bibiyata domin fansa suna da yawa wallahi. Didi ta sauke numfashi ta ce, illar cutar da wani kenan a rayuwa, da baka aikata ba da hakan bai faru ba. Didi tunda Wal iya ya saka a kashe Jidda nake nadamar rayuwar da nayi a