Sashe 34
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce, ban sani ba. Didi ta ce, ta ya zaka sani tunda baka so ka sani ba?. Ta sake kallon Nayla da take murmushi ta ce, Wai fa Yalla ai ne ya yi tafiya zai yi kwana biyu baya cikin gari, shine nazo ya bani key in gidan mu naje na zauna. Nayla ta an bu e ido ta ce, ke ka ai a gidan? Meyasa baza ki zauna a nan ba?. Didi ta kalli Omar da yake tsaye har lokacin, ta kalli Nayla ta ce, Nayla Omar fa anina ne, ke ma anwata ce, ta ya ina matsayin uwa a wajan ku zan auko afa na zo gidan nan na ce zan kwana don Allah?. Nayla tayi dariya ta ce, Didi to meye a ciki? Mahaifiyar Mama tana kwana gidan mu na Kaduna kafin ta rasu. Kuma ni ai ba ba uwa ba ce ba Didi, zaman ki a nan zai yi min da i fiye da yadda ki ke tunani, na tabbatar in ki ka zauna a ranar zan fara jin da in zaman gidan nan. Don girman Allah ki kwana a nan in, in kuma ba haka ba mu koma can gidan sai mu kwana tare. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, Ubana ma ai ya yi min dole, harda rantsuwa kuma yana fa a min baya karya masa rantsuwa, dole na amince ko bana so. Nayla tayi dariya jin da i ta ce, YaMar ya kyauta, ya yi daidai. Yanzu me zaki ci?. Didi da murmushi ta ce, e min kai zaku yi kenan? Shi yana tsaye am kamar soja. Nayla ta ce, ni dai yanzu ki fa a min me zaki ci?. Keda baki da lafiya ina ke ina girki? Ki bari in zan ci zan girka da kaina. Nayla ta zaro idanu ta ce, ki yi girki a gidan nan? Ai bazai yu ba Didi. Yanzu ki ka ce matsayin uwa kike a gare mu, kuma sai na bari ki yi girki? Lallai bani da kunya ta fa a tana dariya kafin ta ce, Ni fa ganin ki har ya saka na daina jin ciwon kan ta fa a tana tashi ta shiga ciki. Didi ta bita da kallo tana murmushi kafin ta kalle shi ta ce, yarinya bata da lafiya baka damu ka sani ba ko Omar? Yanzu in wani babban ciwon ne fa? In wani abun ya same ta wallahi kai kanka baza ka ji da i ba. Ka gyara zaman nan naku don Allah, ba dan komai ba ko dan saboda lafiyarta. Bai ce komai ba amma shi kansa bai ji da i ba a ransa, in ya tuna yadda ta dinga lalla a shi tana bashi tea hakan yana yi masa da i a lokacin, shima zai so ya kula da lafiyarta kamar yadda ta kula da tashi. Basarwa ya yi yana kallon Didin ya ce, nima ai bani da lafiyar yana gama fa ar hakan ya wuce zuwa aki. Didi tashi tayi ta bi Nayla kitchen ta same ta a tsaye kamar mai nazari, ganin Didin sai ta ce, Yauwa Didi, me zan girka miki?. Didi tayi murmushi ta ce, duk abinda ya yi miki. a, ina so na san abinda ki ke so, meye favorite in ki?. Ki dafa Omar s favorite, nima Ina so. Nayla tayi ar dariya ta ce, har na tuna lokaci da ki ke fa a min yana son jellof rice, pasta, indomie and awara. Yanzu ni me zan dafa?. Kafin Didi tayi magana ta ce, okay, let me prepare some delicious jellof rice for my Didi ta fa a tana aukar waya tana danne-danne. Ba jimawa ta ajjiye ta ce, kin ce jellof d in mai kifi ko?. Didi ta yi murmushi ta ce, ba sai kin saka ba, a ina za a samu yanzu?. Akwai inda nake order, yanzu zaki ga an kawo min. Didi ta bi kitchen in da kallo cikin burgewa, yana nan tsaf dashi sai hamshin turaren wuta yake yi ta ce, kitchen inki very neat Nayla. Murmushi tayi bata ce komai ba ta fara ha a kayan girki. Gyaran kayan miya ne bata auna, ta an yamutsa fuska ta ce, I hate this wallahi, a gida ko me zan dafa bana gyarawa sai dai a yi min. In ba haka ba sai dai na ha ura da cin ko meye. Sai ta bawa Didi tausayi, ta san Nayla ar gata ce ajin arshe, komai yi mata ake yi a gidansu amma gashi ta are rayuwarta a haka. A sanyaye Didi ta ce, kawo na gyara miki. Nayla ta wara ido ta ce, So ki ke unborn ya fara jin haushina tun yana ciki? A a bari zan yi da kaina. Waya aka yi mata sai ta kalli Didi ta ce, Kin gani, rider in ne yake kira yanzu zasu kawo. aukar wayar tayi tana bashi address, ba jimawa ya sake yi mata waya ta fita ta je ta kar a ta dawo. Didi ta kalle ta bayan ta ajjiye tana bu ewa ta ce, meyasa ki ke siya da ku in ki? Ai ha in Omar ne ya siya ba ke ba. Nayla ta ce, Didi ni ba siya nake yi ba fa, dan ni bai dame ni ba gaba aya. Kuma ni bana siyan abu sosai, da azumi ne akwai na siya kaji shima sai gab da azumin zai are sannan na siya. Duk da haka dai Nayla. Nayla tayi mumurshi bata ce komai ba, Didi ta kar i gyaran kifin ta dole ta ta bata ba dan ta so ba. Viniger ta bawa Didi ta kar a ta gyara kifin su na ta hira cikin nisha an ri e kai Nayla tayi alamun ciwo Didi ta ce, ciwo ko? Sannu Nayla. Na ce ki ji ki huta amma kin i, gaskiya ya kamata ki je asibiti a duba aga meye yake kawo miki wannan ciwon kan, kina yawan yinsa. Nayla ta ce, Ranar Mondy zan je in sha Allah, Ko ma azumi bazan auka ba ranar. Ai gwara haka, Allah ya ara Lafiya. Amin Didi. Kina da arin azumi Nayla, kina burge ni sosai saboda kina da ri o da ibada sosai. Bana jin wahalar azumi, na riga na saba in ba ban yi ba bana jin da i. Yanzu haka na gama sitta shawwal kuma har wanda ake bina na yi. Didi ta ce, kin yi ari sosai. Allah ya kar nan gaba Omar ya hana ki azumin litinin da Alhamis in nan, ko da yake ma ai kina wajan aiki ba yini ki ke a gida ba. Nayla da mamaki ta ce, Kawai sai ya hana ni ibada Didi?. Eh mana, baki san maza suna hana mata yin azumi ba?. Na sani, akwai cousin ina itama haka take kamar ni, amma da tayi aure ta daina. Har ta kan cemin tana so ta cigaba amma mijinta ya hanata Ashe ma kin sani Didi ta fa a tana ajjiye abinda yake hannunta. Nayla ta ce, To wai Didi meyasa suke hana azumi? Ba sa so ana yin ibadar ne ko me?. Didi tayi ar dariya ta ce, ba haka bane, kawai saboda shiga ha in su ne. Nayla ta an yi jim kafin ta ce, Kamar ya shiga ha i? Kawai dan mutum yana azumi sai ya shiga ha in wani?. Didi ta sake yin dariya ta ce, Zamu jira mu gani, in har Omar ya hana ki yi zaki fahimci me nake nufi, in ma bai hana ki in ba ma zaki gane. Nayla ta ce, no, ina so na sani yanzu. Zaki sani Nayla, faatana da burina Allah ya daidaita zaman ku. Nayla tayi ajiyar zuciya Didi ta cigaba da taya ta aiki tana murmushi. Zata so ganin ranar da Nayla da Omar zasu zama ma aurata kamar kowa, zata so ta ga irin so da aunar da Omar zai nuna mata, zata so ta ga tattali da riritawar da Omar zai gwadawa Nayla. Kuma zata iya rantsewa Omar yana daga cikin mazan da zasu iya hana Nayla yin azumi, ba dan komai ba sai dan za a shiga ha insu. Haka kawai take ji a ranta hakan zai faru, ba dan Omar in ya fa a mata ko wani dalili ba, haka kawai ta san da yar hakan bai faru ba. Nayla ta kalli Didi ganin tana murmushi ta ce, Didi wallahi you re so beautiful. Didi tayi dariya ta ce, Nayla ban da tsokana. Allah kuwa, Da na ga Anties in ku sai na tabbatar da gadon kyau ku ka yi dan dukkan su ma sha Allah. Ashe ma halfcast ne ku tunda dangin Mama an Chad ne, Shiyasa ku ke da kyau. Kin san anyi analysis babu wanda ya kai halfcast kyau a duniya. Diid tayi dariya ta ce, Omar dai yana da kyau amma ba ni ba. Ai kuna kama dashi sosai, ana ganin ki a san ke jinin shi ce. Kama ta jini ba, amma Omar da mahaifiyar mu yake kama completely. Manyan idanu kawai ya fita, idanunta na da girma sosai itama kawai na shi ya fi nata ne sosai. Tana da kyau sosai, tana da kyaun da ake kira kyau shiyasa Omar da ya gadota ake kallonsa in ya shiga waje. Zan nuna miki hotonta zaki gani. Nayla tayi murmushi ta ce, Allah ya gafarta musu. Didi ta amsa da amin suka cigaba da hira har suka gama girkin tsaf suka wanke kayan. Didi ta kalle ta ta ce, Tunda naga har wata apron ki ke sakawa a kitchen in, cire ta mu je mu ci abincin. Nayla tayi murmushi tana kwance igiyar apron in ta ce, bana son ata kayana ne. Didi ta ce, jeki ki shafa turare a jikinki da hannunki ki dawo. Nayla bata musa ba ta fita taje ta dawo. Tana dawowa hamshin turaren ya shiga hancin Didi tayi murmushi ta ce, turaren kam akwai hamshi, kin san kifi yanzu sai ya ma ale miki a jiki. Na kai abincin falo na ajjiye, na ji dawowar Omar daga masallaci ya shiga aki. Ki je ki ce masa ya zo mu ci abinci. Nayla ta wara idanu waje ta ce, na je ina Didi?. Didi ta ce, akinsa mana, ki je ki