Sashe 29
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayla ta kalle shi ta ce, "Sannu da zuwa." Bai amsa ba sai gyaran murya da ya yi ya ce, "Kin raina ni ko?." Gaban Nayla ya fa i ta kalle shi alamun me na yi kana ta ce, "me na yi?." "Kar na sake yi miki magana akan ku in nan, in na sake yi miki magana baza ki ji da i ba." Nayla tayi ajiyar zuciya dan tayi tunanin laifi tayi masa ta ce, "ai na yi lissafin, daman so nake ka zo na fa a maka." "Uhu hum" ya fa a alamun yana jiran cigaban maganarta ta ce, "dubu ari biyu ne" ta fa a kawai dan bata san ne zata ce ba, ta kashe ku i a kalla ya yi miliyan aya da wani abun, amma saboda kar ya ga kamar arya take in ta fa i asalin ku in, kuma tsakani da Allah ta yi masa shiyasa ta ce haka. Bai ce komai ba ya wuce zai bar wajan ta ce, "Akwai abinci." Ko kallon ta bai yi ba ya wuce cikin aki. Ta bishi da kallo ta ce, "wannan ka rasa gane kansa." Washe gari kasancewar an tafi sallah break babu batun zuwa aiki sai ta yi niyar zuw a gidan Didi da kuma gidan Mama Sa'adatu. Didi ce ta kira ta a waya ta ke sanar da ita kar ta ce zata je ta shigo cikin gari ita da AbdulHamid. Ranar gaba aya bata ganshi ba, ko motsinsa ma bata ji ba, duk ta damu tana so taji ko ciwon kan ne ya sake dawowa bata sani ba. Kuma ita bazata iya shiga akinsa ba, gwara ta zauna ta jira shi in y fito sai su ha Tana zaune gab da sallar azahar ita ka ai tana cin donut din ta na jiya aka yi knocking gate in gidan. Hijjabi ta saka akan atamfar jikinta ta fita ta bu e. Bin matan take yi da kallo kamar ta san fuskarsu amma bata gane su ba, suna yi mata kama da wanda ta ta a gani amma sai ta kasa tunawa saboda basu yi kama da hausawa ba ko a shigar su. aya daga ciki ta yi murmushi ta ce, "Sannu ata, Don Allah nan ne gidan Omar?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "eh nan ne." "Na san baki san mu ba, Mu dangin mahaifiyarsa ne." Nan da nan fuskar Nayla ta washe da annushuwa ta ce, "Lah sannun ku da zuwa, bismillah ku shigo." Suka shigo ta rufe gate in daya daga cikin mutane ukun ta ce, "Allah yasa baya nan." Nayla ta ce, "baya nan, mu shiga" ta fa a tana yin gaba suka biyo ta a baya. A falo ta sauke su da fara'ar ta kaso musu ruwa da drink harda ragowar cincin da donut, ta ha o da fruits kankana da apple harda aramar wu a ta yanka apple duk ta kawo musu ta ajjiye. Zama tayi ta ce, "Ina yini." Suka amsa da fara'a suna tambayarta anyi sallah lafiya, ta amsa da lafiya lau. aga daga cikin su wacce ta kasancr babba a cikin su ta ce, "Ni sunana Zainab ni Yayar mahaifiyarsa ce, dani da mahaifiyarsa uwa aya uba aya, ni take bi. Wannan anwar mahaifiyarsa ce sunan ta Aisha mai sunan Yayarsa kenan, wannan kuma sunan ta Saroot." Nayla ta yi murmushi cike da jin da i ta ce, "ina ta tunanin inda na san fuskar, ashe a bikin Didi ne na an ganku ka an.." murmushi suka yi wacce tayi magana ta ce, "Tun farkon auren ku muka so mu zo sai aka shiga azumi, shiyasa yau na ce tunda mun shigo cikin gari zamu zo mu gaisa. Na san duk baki san mu ba, baki san kuma labarin mu ba. Ganin da ki ka yi mana a bikin Aisha ai baki san su waye ba, kin an gan mu ne ka an kin wuce." Nayla ta girgiza kai cikin girmama su ta ce, "gaskiya na ji da i sosai." Saroot ta ce, "mu ma mun ji da in ganin ki, ko babu komai zamu dinga zumunci. In ba haka ba za a iya ha uwa a hanya kowa ya wuce bamu zan juna ba, hakan kuma babban abin kunya ne a gare mu." Nayla sai murmushi take yi Saroot ta ce, "ki saka min number ki a nan." Nayla ta kar i wayar ta saka mata number ita kuma ta kira ta dan Nayla ta ga number. Mama Zainab ta ce, "Ya sunan ki?." Nayla ta ce, "Hauwa, amma Nayla ake ce min." "Ma sha Allah, ga ki kyakykyawa kamar mijin naki, ina ta so na gano dake dashi waye ya fi kyau." Murmushi tayi tana sunkuyar da kai ita a lallai tana gaban sirikai. Mama Aisha ta ce, "An ce ar Kaduna ce ke ko?." Nayla ta ce, "eh a Kaduna nake, iyayena kowa yana can." "Ma sha Allah. Allah ya ba ku zaman lafiya ya baki ha urin zama da Omar." Ta amsa da amin tana murmushi tana mamakin kenan shi kowa ya san halin sa. Nayla ta mi e tana cewa, "bara na kawo abinci." Mama Zainab ta ce, "ki barshi Nayla, ki yi zaman ki yanzu zamu wuce." "Don Allah Mama ku tsaya ku ci." "Zamu ci wata rana, yanzu sauri mu ke yi." Nayla ta zauna ta ce, "to ga cincin ku ci don Allah Mama." Da i Mama Zainab nake ji jin matar Omar na ce mata Mama hakan ya shiga har zuciyart. Cincin in suke ci har da donut in sun an ta a, Umma Saroot ita duk tsorace take bata so Omar ya shigo ya yi musu abinda ya saba shiyasa ta agu su bar gidan duk da kirkin Nayla ya kwanta mata a rai. Tsarabar kayan hamshin gida dana jiki suka bata, Nayla ta kar a tana godiya dan da yawa kuma akwai hamshi sosai. ofa suka ji anyi tare da shigowa duk suka juya kalli wanda ya shigo. Nayla ta san shine kawai yake shigowa ba tare da ya buga gate ba, shiyasa tana jin an shigo ta san shine hakan ya saka ta kalle shi tana so ta ga wanne irin farin ciki zai shiga. Dangin mahaifiya ai ba wasa ba ne, ko ya ka ga naka sai ka ji da i zuciyarka; balle su ace a kaf dangin sa sune ziyarar farkoa gidan. Nan da nan ya aure fuska tamau ganin wanda suke zaune a falon, are musu kallo yake yi aya bayan aya kafin ya kalli Nayla da take kallon sa da murmushi. Wani irin acin rai ya ji ya mamaye masa zuciya, ya rufe ido ya sake bu ewa yana kallon su. Fuskar Zainab ya kalla nan take lokacin da suka kore su shida Didi ya dawo idanun sa, da yanayin wula ancin da suka dinga zazzaga musu kamar ba jinin su ba ya cigaba da yawo a idanunsa. "Omar barka da zuwa, da fatan an yi sallah lafiya." Mama Zainab ta fa a tana kallonsa da murmushi duk da ta san bazai amsa ba. Ai kuwa bai amsa in ba sai ma wucewa da ya yi ba tare da ya ce pim ba. Mama Aisha ta mi e ta ce, "Kun ga ku zo mu bar gidan nan tun kafin ayi abinda aka saba, gidan su ma in mun je ba wanyewa lafiya ake yi dashi ba balle kuma cikin gidansa. Nayla zamu dinga zumunci a waya" ta fa a tana fita. Nayla sai ta ji wani iri ganin irin abinda Omar in ya aikata, dangin mahaifiyarsa kuma yayar mahaifiyarsa ce ma tayi masa magana ya yi mata banza ya wuce. Sai ta ji sam bata ji da i ba kuma bai kyauta ba, da tana da iko dashi da ta nuna masa yayi kuskure babba. Mama Zainab ta kalli Nayla tayi murmushi ta ce, "A yanayin yadda auren ku ya zo babu lallai ki fahimci dalilin Omar na yin haka, amma ki tambayi Aisha zata baki labari. Matsayin ki na matarsa Ina ro onki da ki daidaita wannan gabar da Omar yake yi da mu, shekaru da yawa amma ya kasa manta baya, duk dai ba a kyauta ba. Mun gode da yadda ki ka kar e mu, Allah ya yi miki albarka" ta fa a tana fita. Tare suka fito da Nayla ta raka su har gate gaba aya jikinta ya gama yin sanyi. Tana dawowa falon yana fitowa kamar daman jiran shigowarta yake yi. Kallon ta ya tsaya yana yi ya ce, "waye ya baki iznin barin wa annan su shigo gidan nan? Waye ya fa a miki kowa na zuwa inda nake!?." Jin yadda yake maganar da tsawa yana bu e idanu sai ya koma mata sak Omar in gidan Didi mai ora mata wu a a wuyanta, ta tsorsta ta an ja baya ka an ta ce, "Cemin suka yi dangin Mamanka ne, kaga....." "In ki ka sake ki ka arasa sai yanke miki baki" ya fa a a fusace yana aukar aramar wu ar da take kan Apple a ajjiye. Nayla tayi if ganin za a mamaita abinda ya wuce, ya sake wara idanu ya ce, "dan na zo na zauna a nan ba hakan yana nufin zan auki ko wanne shirme daga gare ki ba, ki tsaya iya matsayinki, ki tsaya a inda na ajjiye ki kar ki tsallaka inda ban baki izini ba, sannan kar ki sake aikata wannan ganganci kin ji ko!?." Nayla ta zabura jin tsawar har tsakiyar kanta ta ce, "Na ji." Buga gate in da ake yi ne ya saka ta fita da sauri dan ta gujewa wannan tashin hankalin, tana bu ewa tayi ajiyar zuciya ganin Didi. Ganin ta ru e ya saka Diid tambayar lafiya amma bata iya bata amsa ba gidan kawai ta kulle suka shiga ciki. Dashi suka fara ha a ido yana tsaye idanunsa sun yi ja sosai, ta kalli Nayla da jikinta yake rawa ta kalli hannunsa ganin aramar wu a sai ta ce, "Omar Lafiya? Me ka ke yi da wu a a hannu?." "Ki fa awa an uwanki, kar wanda ya sake zuwa gidan nan. indai har ni da nake zaune a gidan nan zan amsa sunan gidan da