Sashe 64
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
o kuma? Yana Ina?." "Yana waje dan bai shigo gidan nan ba." Daddy ya ce, "ya sunansa?." Aminu ya ce, "ya ce sunan shi Omar, wani saurayi haka fari kyakykyawa." Daddy ya kalli Abba dan tashin farko Omar in Nayla ne ya zo zuciyarsa, ya kalli Aminu ya ce, "jeka ka shigo dashi, ka rako shi har falon nan." Aminu ya amsa ya fita da sauri. Daddy ya kalli Abba ya ce, "ka ga abinda nake fa a maka, mu bi komai a sannu gashi ya kawo kansa." Abba ya ce, "gwara da Allah ya sa ina nan, dan na san halin ka baza ka bu e masa wuta yadda ya kamata ba, tunda ya same ni kuwa ya ha u da daidai shi." Daddy ya yi murmushi a lokacin Aminu ya yi sallama suka shigo. Omar akan carpet ya zauna kamar yadda Didi tayi masa nasiha, Aminu da ya rako shi ya fita ya barsu su uku a zaune. Daddy ya kalli Omar da fara'a ya ce, "Malam Omar barka da zuwa." Omar kuwa tunda ya shigo falon nauyi da girmansu ya gama mamaye masa zuciya, ya rasa abinda zai yi balle ya iya magana. Da yar ya iya furta, "Barkan ku da yamma." Daddy ya mi a masa hannu ya ce, "bismillah ,mu gaisa." Hannu ya bayar kamar yadda Daddy in ya mi o masa hannu, suka gaisa harda Abba da yake ta kallonsa dan gani yake Omar ya canja masa. Daddy ya ce, "Ya aiki ya kuma Yayarka?." Omar ya ce, "Alhamdu lillah." "Ma sha Allah haka ake so." Omar ya yi shiru ya rasa ta inda zai fara, shi fa wallahi bai san ta inda zai fara bai ma san me zai ce ba, sunan da zai yi amfani dashi wajen kiran Daddyn ma bai sani ba hakan ya saka shi yin shiru. Abba ya kalle shi ya yi murmushi ya ce, "Malam Omar ka yi shiru baka ce komai ba." Omar ya an sauke numfashi ya ce, "Alhaji ayi ha uri da abinda ya faru." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Omar ai mu ba laifi aka yi mana ba, Nayla ta dawo ta ce ita ba fa a ku ka yi ba kawai tana so ka saketa ne ta gaji da zaman auren." Omar ya lumshe ido ya tsani kalmar sakin nan da ake fa a, in dai za a ambaceta sai yaji kamar an soka masa mashi a zuciyarsa. Ya bu e ido ya ce, "laifina ne duk abinda ya faru." Abba ya ce, "yanzu kana nufin kazo a baka ita a karo na biyu kenan?." Omar ya aga kai alamun eh kana ya ce, "abinda nake nufi kenan." Daddy ya ce, "Omar bamu san abinda ya saka Nayla ta ce haka ba, baza mu yi gaggawar cewa zata dawo wajanka ba dan wata ila tana da dalilin da baza ta iya fa a mana meye shi ba." Omar ya sauke numfashi ka an ya ce, "laifina ne kamar yadda na fa a, ni ba mutum ne mai arya ba zan sanar daku gaskiyar abinda ya faru. Da farko ban kar i aurenta ba gaskiya, a ranar da aka sanar dani in zaku tuna na furta bana so kafin yayata ta ce zamuyi magana a ke ance, itace tayi min dole har na amince da auren amma ba dan ina so ba. Itace ta yi min dole ta saka nayi mata al awarin bazan ta a rabuwa da ita ba koda mahaifinta ne zai kira ni ya ce na rabu da ita, hatta zama a gidan da nake yi Didi ce tayi min dole ba dan ina so ba. Ina da wahalar sabo, shiyasa abubuwa suka dinga faruwa har ta kai ga ta kasa jurewa ta ce zata dawo." Abba ya ce, "kace da gaskiyarta gwara ayi sakin a huta, meye amfanin zama da wanda baya sonka bai kar i aurenka ba?. Har gwara ace itace take zaune da kai bata sonka da ace kaine baka sonta, ka ga zaman da ku ka yi zaman cutuwa ne da acin rai da kuma ba in ciki." Daddy ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "gaskiya ne, tunda har abin ya zama haka yanzu ka rubuta mata takardar sakin kawai zai fi alkhairi." Omar ya oye ru aninsa ya nutsu sosai ya ce, "A'a Alhaji, bana tunanin ko duniya zata taru ta ce na saketa zan iya sakinta, ko meye zai faru a yanzu sai dai ya faru amma wallahil azim bazan iya rabuwa da ita ba. A yau na zo da kaina da cikin umarnin kaina ba dan umarnin yayata ba, na ji a raina in ban bata dawo gidana ba bazan sake yin farin ciki ba a duniya. Alhaji da gaske nake wannan zuwan na kaina ne ba na umarni ko dole ba, a shirye nake na zauna da ita zama na har abada. Na san mahimmacin da take dashi a rayuwata, a baya ma ban gama fahimta ba shiyasa har hakan ya faru, amma a yanzu na gane mahimmacin da take dashi a rayuwata bazan iya rabuwa da ita ba. Ina sonta, ina aunar zama da ita har abada." Daddy ya yi murmushi domin kalaman Omar sun burge shi sosai, kai tsaye yake magana babu ruwansa da wani kara ko kunyar surukai. Daddy ya ce, "in na fahimce ka yanzu ka amince da auren, sannan zaka zauna da ita a matsayin matarka?." Omar ya girgiza kai ya ce, "haka ne." Abba ya ce, "kuma ba umarnin ta sake baka ba kuwa? Anya ba dole aka sake yi ba?." Omar ya yi murmushi ya ce, "ko aya, itama ta san ta gama yi min dole a duniya. Da kaina nazo kuma saboda son raina ba dan ita ba, nakasa jurewa ne kawai, duk yadda na so na jure rashinta na kasa, duk yadda naso na aryata kaina akan ina aunata na kasa. In da dole tayi min da tare zamu zo da ita, kuma baza ta ta a bari nayi magana ba, kafin nayi magana aya tayi goma saboda tsoron kar na furta abinda bata so. Kamar yadda na ce ni ba mutum ne mai oye gaskiya ya fa arya ba, wallahil azim da ace bana ra'ayi labarina ma baza a sake ji ba balle har nazo da kaina. Wallahil azim ina sonta, babu halittar da nake so a duniya kamar yadda nake sonta." Abba ya yi murmushi mai sauti cikin jin da in kalaman Omar ya ce, "Haka ne Malam Omar, na amince da gaske yanzu kana son Nayla ba dole aka yi maka ba. Amma kamar yadda aka baka dama a wancan lokacin aka zauna dakai aka tambayeka ra'ayinka akan auren itama za a bata dama, a lokacin baya ba a tambayeta ba saboda muna ganin kaine ba a kyautawa ba an baka aureta ba tare da ka sani ba. Itama zamu bata dama kamar kai, in tana ganin zata iya cigaba da zama da kai shikenan, in baza ta cigaba da zama da kai ba Omar babu wanda zai yi mata dole, sai dai mu ce ka yi ha uri." KRB3P036 Omar ya ago a hankali ya kalli Abba, ya sake sauke kansa asa yana maimaita kalmar sai dai mu ce ka yi ha uri, bai san ko duniya ce zata taru a kansa ba bazai saki Nayla bane shiyasa yake fa ar haka. Ya yi ajiyar zuciya amma bai ce komai ba dan irjinsa bugawa yake yi in ya tuna su in iyayenta ne. Daddy ganin yanayin da ya shiga sai ya murmushi ya ce, "na amince a yanzu baza ka bar Nayla ta yi kuka ba Omar, tabbas a yanzu na amince a zuciyata Nayla tayi aure ta auri wanda yake aunarta. Amma kamar yadda anina Ali ya fa a maka za a bata dama kamar yadda aka baka, daman mahaifinta ne ya yanke hukunci a kwanakin baya shiyasa mu ka tambaye ka dan kaine ba a kyautawa ba, amma yanzu za mu tambayeta mu ji me zata ce." Omar ya girgiza kai cikin rauni ya ce, "To. Amma zamana da ita a wannan lokaci bazai ta a zama na cutarwar ba balle har ta kai ga dawowa gida ba, ko a baya ban ta a cutar da ita ba balle kuma yanzu da na san mahimmacinta. Sai ka rasa abu ka ke gane darajar da yake dashi da adadin aunarsa da ka ke yi masa, bazan sake bari hakan ta faru ba a yanzu ko a nan gaba." Suka yi dariya tare Abba ya ce, "Dakyau Omar! Haka nake son mutum mai fa ar asalin abinda yake zuciyarsa, bana son mutum bai oye gaskiya ya fa arya dan farantawa wani rai. Tabbas ba dan na san iyayenka ba da sai na ce ni na haife ka." Omar ya murmusa ka an amma bai ce komai ba. Daddy ya ce, "Tunda yanzu ka amince da auren naku za ka kar i shi hannu biyu, maganar gwajin jinin da mu kayi tun kwanakin baya yanzu muna da bu arta shi gaskiya." Omar ya sauke numfashi ka an ya ce, "in sha Allah za ayi." "Kasancewar ka mai gaskiya na baka dama ka je duk inda ka ke so ayi maka ka kawo min, na san baza ka oye min komai ba, dan na amince da kai ari bisa ari." Omar ya sake yin murmushi, sosai yake jin girman mutanen a idanunsa, yadda suka kar e shi hannu biyu, suka sakar masa fuska lamarin ya yi masa da Daddy ya ce, "Naylan tana gidan nan, sun zo duba ni ita da Mamanta saboda na an yi fama da mura. Yanzu zan turo maka ita ku gaisa kafin gobe in Allah ya nuna mana mu zauna da ita mu tattauna dan mu ji ra'ayinta." e baki yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Abba da ya kula da hakan sai ya ce, "kar ka damu Omar, fa i abinda yake bakinka." Omar ya ce, "in da dama a tambayeta a yau.....don Allah" ya arasa fa a murya a asa. Daddy ya yi murmushi haka Abban ma, gaba aya Omar in ya canja musu ya koma wani daban kuma ya basu nisha i matu Daddy ya ce, "ka kwantar da