Sashe 65
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hankalinka, mu jira gobe in Allah ya kaimu." Omar ya sauke kai asa bai ce komai ba amma ba haka ya so ba. Abba ya ce, "ka kwantar da hankalinka kaji Omar, Ina bayanka nima a yanzu, zan taya ka ya in dawo da Hauwa in sha Allah." Murmushi ya sake yi amma bai kuma magana ba. Daddy ya auki waya ya saka a kunne ya ce, "ki turo min Nayla parlour." Babu jimawa Nayla ta shigo da sallama, bata lura da Omar ba amma gabanta ya fa i sosai ba tare da san dalili ba. Kusa da Daddy ta je ta ce, "Daddy gani." Daddy ya kalle ta ya ce, "mijinki ne yazo, gashi a zaune ku gaisa" ya fa a yana tashi tsaye, Abba ma ya tashi suka fita zuwa harabar gidan. Nayla tsam tayi a inda take zaune irjinta ya buga sosai, lumshe ido tayi domin kuwa sai yanzu ta sha hamshin turarensa mai matu ar sanyi da kashe mata jiki a duk sanda ta sha e shi. irjinta bugawa yake yi da matu arfi, wani abu take ji yana shiga jijiyoyin jikinta kamar tafiyar ruwa. Kewarsa da kwarjininsa ya cika falon gaba aya, ta kasa koda motsin kirki ta yi shiru tana jin sautin bugun zuciyarta. Shiru ya ratsa parlour dan ta asan ido ta ga inda yake zaune, kanta yana asa bai ce komai ba itama kuma haka. Shi kam Omar kallonta yake yi kallon da bai ta a yi mata irin shi ba a duniya, kallon urilla yake yi mata yana kallon yadda idanunta yake iftawa kamar wacce wani abun ya fa a mata cikin idon, duk da hakan sabon ta ne amma sai ya ga na yau yafi aukar hankalinta. Lumshe ido ya yi ya bu e a kanta, sai a lokacin ya sake tabbatar da ba aramin kewarta ya yi ba, a karo na farko a rayuwarsa da yake ji yana son ha a jikinsa da mace, ji yake kamar ya tashi ya mi ar da ita tsaye ya sakata a irjinsa ya mayar da hannunsa ya rungumeta ko zai ji sau in bugun zuciyarsa take damun sa dashi. "Ba magana... an mata!" Ya furta cikin wata irin murya mai sanyi da da in saurare, a can asa ya yi maganar cikin wani sabon salon da bai san yana dashi ba. Nayla sai da ta sauke ajiyar zuciya jin yadda muryarsa ta daki zuciyarta ta ratsa jininta ta zaga ko ina a jikinta. Hawaye taji yana taruwa a idanunta, hawayen soyayyar da take masa da tsnatsar kewar ganin fuskarsa da jin muryarsa suna taruwa a idanunta. A hankali ta ago ido ta kalle shi daman shi kallonta yake karaf suka ha a ido, da sauri ta sunkuyar da kai dan bazata iya jure kallon fararen idanunsa da suke yawo a kan a fuskarta ba. Wani irin abu mai kaifi take hange a idanunsa a karo na farko, bata ta a ganin hakan a idanunsa ba sai a yanzu. "Ina yini" ta furta a sanyaye ba tare da ta kalle shi ba. Omar ya yi murmushi jin muryarta da yadda ta ratsa walwarsa ta kaiwa kunnensa ziyara. Bai ce komai ba sai kallon ta da yake yi kamar ya jawo ta jikinsa ya matse ta har sai ya samar mata da nutsuwa haka yake ji. Nayla jin shiru sai ta turo baki gaba tana mita a zuciyarta, daman ta san ba zai amsa ba tunda ya riga da ya saba yi mata haka. A hankali ya furta, "Kina lafiya?." Nayla ba ta amsa ba ta ce, "Ka bawa su Daddy takardar sakin ko yanzu zaka fa a min?." e baki ya yi tare da kallonta ya ce, "Daman ni na ce zan kawo wani abu ne?." ago kai tayi suka ha a idanun ya aga mata gira, hawaye suka sakko akan kuncinta amma bata ce komai ba. Omar kallon ta yake yi ganin hawaye yana sauka akan kuncinta. Sauke ido asa tayi sai ya ce, "ni ban ce zan kawo komai ba, kawai na zo na koma dake." Zuciyar Nayla bugawa take yi matu a, har a kunnenta tana jin yadda zuciyar ke bugawa sosai. Shi kam Omar gaba aya ya rasa abinda zai ce mata, shi ba iya magana ya yi da mace ba, sannan ba iya rarrashin mace ya yi ba, ko lokacin Narma itace take rarrashinsa ba shine yake rarrashinta ba, shiyasa ya rasa abinda zai ce mata. Tunawa ya yi Didi ta ce ya fa i duk abinda yazo zuciyarsa, hakan ya saka ya kulle ido ya bu e ya ce, "Jidda!." Wani irin dum Nayla taji a zuciyarta, a karo na farko an kira ta da Jidda, duk da ta san sunanta ne amma ba dashi ake kiranta ba. Bata san ta ago ta kalle shi sun sake ha a ido ba, tsayar da ido tayi a kansa na na wani lokaci kafin ta sauke ido asa. Omar ya sake tausasa murya ya ce, "Ki yi ha uri!." Ba Nayla ba, shi kansa da ya bada ha urin sai da ya ji sautin a zuciyarsa, fit ya ji kalmar ta fita ba tare da ya shirya ba. Bai ta a bawa wata halitta ha uri daga zuciyarsa ba sai ita, itace mace ta farko da yake furta mata kalamansa suke fitowa daga zuciyarsa har kan harshensa Nayla ta rufe ido ta bu e tana jin kamar ana aureta da igiya, ta kasa koda motsin kirki sanyin da take ji yana mamaye jikinta kamar mai zazza i. Omar ya sake cewa, "Na auka barinki a inda nake shine zai zama maganin matsalata, amma da na zauna bakya nan sai na fahimci kece maganin matsalar. Ina so ki dawo mu cigaba da rayuwa ba irin wacce mu ka yi a baya ba, Da gaske nake ina so ki dawo rayuwata Jidda! Nayla ta mugu a cikin sanyin murya ta ce, "Ba zan dawo ba, bayan kace dole aka yi maka ka zauna dani." Omar ya yi murmushin farin ciki, ji yake kamar ya jawo ta jikinsa amma bashi da wannan arfin guiwar. Ya kalli fuskarta da take a asa ya ce, "in ji waye ya ce haka?." ago kai tayi ta kalle shi ta shagwa e fuska ta ce, "kaine ka ce." Sake kashe masa zuciya tayi da salon maganarta, ya runtse ido da arfi yana murmushin da ya i barin fuskarsa ya ce, "a baya haka ne Jidda, amma a yanzu ba haka bane." Nayla ta kawar da kai cikin dakiya da dauriya ta ce, "ni bazan komai ba, Ina jiran sa on saki daga gare ka. Bazan iya cigaba da zama da kai a haka ba, bani da daraja a idanunka, bani da ko wanne mahimmaci a gare ka. Ko lamarinka na shiga cewa ka ke yi baka saka ni ba na tsaya a iya matsayina. Ka kalle ni ka ce baka sona baka son zama dani, ka ce ka tsane ni, ka tsani aurena, babu abinda zai saka ka so auren. Gwara a ha ura kawai, bazan iya zama da wanda baya sona....baya son aurena ba. Na san ba da sanin ka aka aura maka ni bani, sadakata aka baka shiyasa ka samu damar fa ar duk abinda ya zo bakinka......" ta kasa arasa maganar saboda kukan da ya taso mata. Ta share hawaye ta ce, "Ka bawa su Daddy takardar sakin, ni bazan sake zama da kai ba" ta fa a tana tashi tsaye zata tafi. ewa tsaye shima ya yi, rauni yake ji a zuciyarsa saboda jin kukan ta har cikin ruhinsa, in da a baya ne take fa a masa wannan maganar tsaf zai iya sakinta amma a yanzu bazai iya ba, sakinta daidai yake da barazana ga numfashinsa. Omar murya a sanyaye ya ce, "Bazan iya sakin ki ba Jidda! Yanzu na fara rayuwa dake in sha Allah. Bana tunanin ko duniyar nan zata taru akan na sake zan sake ki, bazan iya ba!.." Cak ta tsaya daga shiga cikin gidan da take yi, ta juyo ta kalle shi ya aga mata kai alamun abinda ya ce kenan. Ta girgiza kai ta ce, "maganar farko da ita ake amfani, ka ce baza ka ta a sona ba har abada?." Ya sauke numfashi ka an ya tako yazo daf da ita tana jin saukar numfashinsa, idanunsa yana kallon na ta ya ce, "Maganar farko ba gaskiya ba ce, maganar yanzu itace gaskiya. Jidda ko za a raba ni da numfashina wallahi bazan sake ki ba!." Janye ido tayi daga kallonsa, ta kawar da kai tana jan numfashi. Da sauri ta juya ta shiga gidan dan tsaf zai iya karya mata zuciya, ita kuma tayi udirin bazata koma ba sai dai son da take yi masa ya kasheta. Omar sai ya ji daamuwa ta mamaye masa zuciya a karo na babu adadi. Kalamanta basu tsaya masa a rai ba kamar yadda ganin hawayenta ya tsaya masa a rai, da alama abinda ya fa a mata ya yi mata ciwo sosai a wancan lokacin. Dafe kai ya yi a bayyane ya ce, "meyasa ka ce haka Omar?." Dan aramin tsaki ya yi ya sauke ajiyar zuciya ya fita harabar gidan ya tarar da Daddy yana niyar shigowa. A nan suka yi sallama da Daddy cikin girmamawa ya fita ya bar gidan. KRB3P037 Arewabooks@nanahaleema11. Nayla a guje ta shige falo da mutan gidan suke zaune, ta shiga aki ta fa a kan gado tana kuka mai sauti. Kuka take yi da zuciyarta da gangar jikinta ba tare da ta san dalilin kukan ba. Jikinta har rawa yake yi saboda yadda take kuka mai matu ar sauti kamar ranta zai fita. Wai Omar inta ne fa yazo yana so ta koma gidansa, shine yake cewa bazai iya sakinta ba, kenan sonta yake yi ko me?. Wannan tunanin shine yake sake karya mata zuciya take kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa. Daddy da ya shigo falon da suke ya ga Mama da Mummy sun mi e tsaye suna cewa, "Me ya samu Nayla take wannan kukan?." Daddy ya kalle su ya ce, "Ku yaleta, Mijinta ne yazo." Mummy ta dafe irji ta ce, "sakin na ta in ya yi?." Daddy ya girgiza kai ya ce, "ya ce bazai sake