Sashe 150
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyauta nake so na yi miki kawai." Nayla ta yi shiru tana tunanin abinda zata ce tana so, to me zata ce? Ku i ko mota ko gida?. Tana nan da ku i a account inta na business insu ita da Tiwny babu abinda take yi dashi. Tana da mota balle ta ce mota take so, tana da gidaje ba gida ba ma balle ta ce gida take so. Ita sam bata ga abinda zata ce tana da bu ata ba, shi kansa Omar in ya wadata da komai in ta ce tana bu atar wani abun ta yi arya. "Ina jinki." Jin maganarsa sai ta kalle shi ta ce, "Rouhii ni na rasa abinda zan ce ne, a ganina farin cikin da ka ke bani is enough to me." "A'a bai isa ba, ina so ki fa a Jidda." "Abinda nake ganin zan samu farin ciki in ka yi min bai wuce a small trip with you ba. Zan so a ce mun yi tafiya ni da kai." Ya kalle ta ya ce, "kin san kina so meyasa baki ta a fa a min ba?." Ta mi e ta matsa jikinsa sosai ya ri e kafa arta ta ce, "Rouhii lokacin na fa in ne bai yi ba sai yanzu." "To fa i min ina ki ke so mu je? Wacce ki ke so?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "in zan tuna akwai wani lokaci da muka yi tafiya, mu ka cewa Yaya muna so mu je Maldives sai ya ce amare ne suke zuwa maldives for honeymoon. Shine nake so na ga what is so special about this country da ya saka ta zama the best country for honeymoon." Murmushi ya yi ya ce, "Maldives! Ban ta a jin sunan ba sai yau." Dariya tayi kafin ta yi magana ya ce, "in sha Allah zaki je, amma honeymoon ba yana nufin hutawar ma'arauta ba? Kamar su samu lokaci su yi abinda suke so ko? Kamar dai a hotel in nan." Nayla ta yi dariya ta daga masa kai alamun eh, ya bu e idanu ya ce, "da cikin nawa? Kar ki manta kina da ciki kar a wahalar min ana. Ni tunda na ji wani likita ya ce aljanun daren nan in suka yi arfi da yawa suna saka ciki ya fita na daina bari su tashi sosai." Ta yi dariya mai sauti tana oye fuskarta a jikinsa. Ya ce, "magana zaki yi ai, ba dariya ba." Murmushi ta yi ta ce, "Babu abinda zai faru." Ya girgiza kai yana murmushi ya ce, "Zamu je in sha Allah, zan iya arar da koma me nake dashi saboda ki yi farin ciki kawai. Bayan wannan sai ina?." "Bara mu gama da nan in sai nayi tunani." Ya shafa kanta ya ce, "shikenan, yadda ki ka ce." "Na gode Rouhi." Bai ce komai ba ya kalle ta yana sauke numfashi ya ce, "Didi fa? Nayi tunani yafi sau babu adadi, da farko na yi tunanin siya mata mota, sai naga ina so na ara mata wani abun da zata shiga cikin farin ciki sosai, sai na yi tunanin ko na kaita saudia?." Nayla da fara'a ta ce, "end of discussion! Ka gama magana tunda ka ce saudia, zata fi farin ciki da zuwa saudia akan motar ma." Ya girgiza kai ya ce, "to ya za a yi? Mijinta fa?." "Yaushe zata je?." "ina tunanin zuwa azumi in muna rai." "A'a Rouhi, kana da tabbacin zamu kai azumin ne? Kawai ta je yanzu ka sani ko ta koma da azumin?." Ya an kalle ta kafin ya ce, "Haka ne, Ya za a yi da mijinta?." Nayla ta ce, "a fa a masa mana." Bai yi asa a guiwa ba ya auki waya ya kira AbdulHamid ya saka a speaker, suka gaisa sannan Omar ya ce, "Ina so zan yiwa Yayata bazata ne ta ban mamaki, ina so zan kaita umra nan kusa shine na ce bara na tambaye ka ko zaka bar ta zuwa?." AbdulHamid ya ce, "Omar mai zai hana? A guje ma zan ce a dawo lafiya. Kamar ka sani nima wani satin zan tafi in sha Allah." Ya kalli Nayla ya yi murmushi ya ce, "Kaga sai a shirya tafiyar ta zama lokaci aya ko?." AbdulHamid ya ce, "Za a iya yin hakan." "na gode sosai." "Allah ya bar zumunci Omar, Allah ya saka da alkhairi ya cigaba da dafa maka." "Amin ya rabbi. Amma don Allah kar ka fa a mata, ina so na bata mamaki ne." Murmushi ya yi ya ce, "in sha Allah." Daga nan suka yi sallama ta kashe wayar. Nayla ta ce, "ka ga ikon Allah ko Rouhi? Kaga in ta tafi tare dashi babu wani damuwa ko?." Ya girgiza kai ya ce, "naji da in hakan sosai, yanzu ya za a yi da yi mata international passport ita da Marmerh?." Nayla ta ce, "Abu ne mai sau i, ka ce mata China ne suka nemi international passport na mutane uku da suka kasance makusantanka, sai ka basu nawa, sannan zaka bada nata da na Marmerh shiyasa za a yi mata. Didi ko rayuwarta zata iya bayarwa a kanka." "Zata iya Ashiq, Didi zata iya yin komai saboda ni, shawararki tayi sosai. Gobe sai a kai ki ku je tare ayi musu emergency a bayar." "Allah ya kaimu." Ganin tana murmushi cikin jin da i ya saka ya kalle ta ya ce, "Kamata ya yi a ha a dake a tafiyar nan." Ta yi dariya ta ce, "Zaka kashe ku i da yawa fa Rouhi, ga gida kana ginawa ana daf da kammala shi ko na ce an gama ma, ga aikin company da ake planing za ayi, ga tafiyar Didi, ga tafiyar da zamu yi. Kar a fara kashe ku i masu yawa tun yanzu, mu bari mu fi haka tukunna." "A'a Jidda, ku i fa sai na kashe su, tunda Allah ya bani sai na wadata wanda nake tare dashi. Na san zan samu ne? Ai ban sani ba, tunda na samu zan sadaukar dasu domin farin cikinku. Tafiyar mu daban wannan daban, dan haka dake za a je." Nayla ta yi murmushi tana kallonsa cikin farin ciki ta ce, "Na gode sosai Rouhi, kana shagwa a ni da yawa wallahi. Komai ni,komai ni, kana sakawa na ji babu wata macen da ta kai ni dacen miji a duniya." Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce, "kin cancanci fiye da haka ne ai Jiddass." "Amma ya kamata ayi tafiyar nan da kai." Ya kalle ta ya ce, "Akwai aiki sosai a asa, in bana nan suna abinda suka ga dama suke yi basa mayar da hankali yadda ya kamata. Amma nima ina so na je, kodan na godewa Allah da ni'imar da ya yi min a gaban akinsa, sannan na ro i afuwar laifukan da na aikata a baya. Za dai gani kawai." Nayla ta koma jikinsa ta kwanta yana ri e da ita yana tunanin yadda rayuwa ta canja masa. Kamar yadda suka tsara haka aka fa awa Didi, bata kawo komai a ranta suka je aka yi aka bawa Nayla ta kawowa Omar, ya saka Nayla ta turawa wanda yake musu visa cikin kwana aya visa ta wata uku ta fito a har da Omar. Ranar da mijin Didi ya tafi su kuma bayan kwana biyu zasu tafi amma ta Abuja zasu tashi saboda zai je bu e shagon da za a yi a can. Waya ya yiwa Didi akan ta zo gidansa ta kwana zasu je Abuja a washe gari. Duk yadda ta so ta turje ya ce sai ta zo haka ta zo duk bata san me yake faruwa ba. Nayla tana ha an mata kayan tafiya komai sabo, hijjab da dogayen riguna da komai sabo ta ha a a jakar Didi. Kayan Marmerh da diapers da komai ta ha a dan ba a so Didi ta fahimta. A ranar talata suka tashi zuwa Abuja, suka sauka a hotel gab aya jikin Didi ya yi sanyi tana tunawa da zuwan ta Abuja lokacin Sanata. A ranar aka bu e shagon, duk sun je wajan har Didi. Bayan an gama suka dawo hotel har lokacin Didi bata san me yake faruwa ba dan basa yin maganar a gabanta. Washe gari da arfe uku jirgin Saudia airline zai auke su zuwa Madina, Nayla ta bawa Didi aya daga cikin dogayen rigunan da ta ha a mata Didi ta saka, Nayla a ranar ta yi order baby pusher ta saka Marmerh a ciki suka tafi har airport. Suna zaune bayan sun gama boarding suna jiran jirgi, Nayla tana kusa da Omar Didi na kusa da Nayla a zaune. "Faruk!" Aka fa a daga gefen su. Omar ya runtse ido ya kalli Nayla da take kusa dashi a zaune itama shi take kallo. Narma ta juya kallon ta ga mahaifinta ta ce, "Dad ka ce arya nake yi, yanzu ai zaka tabbatar da shi ne dai Faruk in. Didi!" ta fa a tana kallon babanta kafin ta kalli Didi. Didi ta kalle ta ta ce, "Narma!." Narma ta tawo da gudu zuwa wajan Didi ta rungumeta ta ce, "Didi don Allah wannan ba Faruk ina ba ne?." Didi ta kalli Omar da bai ago ba sai ma ri e hannun matarsa da ya yi, ta kalli Narma ta ce, "OmarFaruk ne Narma. Tabbas shine wanda ki ka sani a baya." Narma ta kalli Dad ta ce, "Ka ji ko Dad, ni na fa a maka shine, amma ku ke aukata kamar mahaukaciya. Ta ya ya zan iya mantawa dashi a rayuwata? Har abada bazan ta a mantawa da fuskarsa ba balle maganarsa. Tun last time na ce maka na ganshi a cikin airport in nan, kuma koda ya ce min ba shi bane na san ya fa a ne kawai, amma wallahi shine. Dad ina son shi wallahi, zan iya mutuwa saboda shi." Sen ya kalli Omar da bai ago ba har lokacin, ya kalli Didi dan ita ya gane ta ya kuma tabbatar itace Yayarsa. Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Da gaske wannan Tiger ne?." Didi tayi murmushi cikin alhafari da jin da i da Allah ya ha u su a lokacin da zai ga banbanci tsakanin