Sashe 88
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga matarsa kuma?. Omar ya kalli Didi da take kallonsu ya ce, "haka zata fita babu mayafi?." Didi ta ce, "A haka muka fito ai." Wani kallo ya yi mata mai cike da harara ya ce, "Sai kuma ta fita a haka?." "Ba a haka ta zo ba? Ko fita zan yi na siyo mata mayafi Omar?." "Kuma sai aka ce miki zata fita a haka?." "To a ina zaka samo?." "Ki bata naki." Didi ta bu e baki cike da mamakin abinda ya ce ta ce, "Lallai Omar! kai ga mai kishin matarka ko? To nima nawa mijina yana kishina. Wallahi ka raina min hankali wallahi" ta fa a tana dariya, ta bu e ledar da ta zo da ita ta bashi showel aukar Marmerh ta ce, "Gashi ta yafa." Hararar showel in ya yi ya harareta ya ce, "wannan meye amfaninsa?." Didi ta ce, "Sai ta fita a haka" ta fa a tana niyar mayarwa. Tsaki ya yi ba yadda zai yi haka ya kar a ya yafa mata yana hararar Didi. Tana kallonsa yana harararta tayi murmushi ta ce, "Harare ni dakyau, sai ka harare ni zan tabbatar Omar ya dawo daidai dole hali ya dawo, an rainin hankali kawai. Ka ri eta ku je, zan taho da kayan nan." ugunta ya ri e ta runtse ido dan ita bata son abinda zai kai hannunsa jikinta, bata so ya auke ta shiyasa take takawa a hankali tana runtse ido saboda zafin da yake ji. Bata so ta yi abinda zai gane bazata iya ba, a haka ta daure tana tafiya tana hawaye har cikin mota. A baya ya saka ta har afarta ya auka ya saka a cikin motar, a lokacin Didi ta zo wajan ta saka abincin da ta tawo dashi a motar, ta kalli Umma Saroot ta ce, "Umma ki shiga baya kusa da ita." Umma Saroot ta kalle shi amma sai ta ga ba ma ita yake kallo ba, ta yi murmushi ko babu komai ta ji da i zata zauna a motar Omar. Shiga gaba Didi ta yi da ledar maganinsu a hannunta ya shiga motar ya ja yana tafiya a hankali kamar baya so. Didi ta kalle shi ta ce, "Ka an tafi da sauri mana, ina so mu je ta huta ne." Ya kalli Nayla ta madubi ya ganta a jingine idanunta a rufe, ya kalli Didi ya ce, "bakya ganin a yadda ta ke? In na tafi da gudu bazai mata da i ba." Didi ta murmusa kawai bata ce komai ba suka cigaba da tafiya. KRB3P051 Arewabooks@nanahaleema11. Suna cikin tafiya Didi ta ce, "Yauwa tsaya a nan na sauka zan araso, ku arasa." Ya kalle ta ya ce, "me zaki yi a nan in?." Ta ce, "zaka gani, Tsaya." Bai musa ba ya tsaya ta sauka su kuma suka tafi. Koda suka je gidan sai da ya shigar da motar ya fito ya bu e mata ya fito da ita ta hanyar ri o hannunta. Umma Saroot dai Marmerh na hannunta shi kuma ba ta ita yake yi ba, ta matar sa yake yi dan ya manta da ita a motar. Sai da ya kai Nayla aramin falon da take zama sannan ya nutsu. Babu jimawa Didi ta shigo da atuwar roba irin wacce masu sana'ar wanki suke amfani da ita, Omar ya bita kallon mamaki ya ce, "Wannan fa?." Didi ta ce, "zaka gani." Ta fa a tana wucewa akin Nayla. Robar ta kai ban aki ta dawo kitchen ta samu babbar tukunya a cikin tukwanen Nayla ta ora akan wuta bayan ta cika ta da ruwa. Falon ta dawo inda take zaune ta kalli Umma ta ce, "Sannu Umma, na barki da aikin ri e Marmerh." Umma tayi murmushi ta ce, "kece da sannu Aisha, Allah ya bar zumunci yayi miki albarka. In ba ke in ba waye zai yi wannan aiki? Ko kwana arba'in baki yi da haihuwa ba amma kina ta kazar-kazar, Allah ya baki lada." Murmushi ta yi ta amsa da amin, ta kalli Omar da yake ta le a fuskar Nayla a lallai sai tayi magana, ita kuma kunya take ji bata so yana zama a kusa da ita ga Didi ga Umma a wajan. Didi tayi an tsaki dan ya fara bata haushi, za ewarsa ta fara yawa. Kallon Didi yayi a sanyaye ya ce, "meye abu na gaba?." Didi ta ce, "zaka gani ai, Nayla taso mu je aki" ta fa a tana mi a mata hannu, ta ri e hannunta ta tayar da ita tsaye. Ganin ta an cize baki tare da kwa e fuska ya saka Omar ya yi tsaki kawai ya uka ya auta cak ya wuce akin da ita bai ce komai ba. Umma Saroot ta yi dariya ta ce, "yau muna ganin film in india a zahiri, ko da yake jinin larabawan Chadi ne." Didi dai dariya ta yi kawai ta bi bayansa bata ce komai ba. A gefen gadon ta tarar ya ajjiyeta, ya tsuguna a gabanta yana magana. Ruwan ta je kitchen ta auko ta shigo akin ta wuce ban akin ta juye sannan ta sirka da na sanyi, ta sake fita ta koma kitchen in ta sake ora wani. Dawowa ta yi ta kalle shi kafin ta yi magana ya ce, "Didi meyasa bata yin magana ne?." Didi ta harare shi ta ce, "har yanzu bata warware ba, ka bari zuwa anjima zata yi maganar." Kallon ta ya yi ya ago da kanta ya kalli idanunta da suke rufe ya ce, "Baza ki ce komai ba? Fushi ki ke yi?." Nayla ta wace kanta ta sunkuyar bata ce komai ba. Didi tayi tsaki tana girgiza kai cike da mamakin Omar, shi ko kunyarta ma ba ya ji sai za ewa yake yi a gabanta. Ta an murmusa ka an ta ce, "Nayla ta so mu je ki shiga ruwan zafin, in kuma tsarkin zaki yi da shi to." Nayla kamar jira take yi ta mi awa Didi hannuta, Didi ta ri eta mi ar da ita tsaye, shima ya mi e da yar saboda bayansa da ya ri e sosai, ya kalli Didi ya ce, "wannan ruwan zafin da ki ka juye ki ke nufi?." Didi ta ce, "Eh, likita ta ce ta dinga shiga ruwan zafi shine zai taimaka mata." "Tsabar rashin hankali na likitan? Wannan ruwan zata shiga ciki?." Didi ta harare shi ta ce, "to sai na ce maka haka zata shiga ciki ba a sirka ba?. Ka ga Malam! ka yale ni nayi abinda zanyi, nima na san abinda nake yi ai. Mai mata." e hannun Nayla tayi suka fara takawa a hankali. Omar ya bi su da kallo cikin tausayin matarsa kana ya ce, "Didi." Tayi masa banza bata amsa ba, ya sake kiranta ta sake share shi. A ganinta ya san yana son Nayla da tausayinta ya yi mata wannan muguntar? Sai bayan ya aikata zai dawo yana marairaicewa a lallai tausayi take bashi, shiyasa ta yi masa banza ta i bashi amsa. Gab da zasu shiga ban akin ya kuma cewa, "Didi!." Bata juyo ba ta ce, "wai meye?" Ta fa a a fusace. "Amma da in kika rakata ban akin zaki fito ki barta a ciki ko?." Didi ta kalle shi a kaikaice ta ce, "A'a, a ciki zan zauna sai ta gama zamu fito." Ya ha e rai tare da girgiza cikin bada umarni ya ce, "Gaskiya a'a, in kin rakata ki dawo ki same ni a nan, ban yarje miki ki tsaya a ciki ba, kar ma ki yi wannan gangancin." Didi ta bishi da kallon mamaki tana dariya a zuciyarta amma fuskarta a aure ta ce, "Ikon Allah! Meye dan na tsaya in? Ba anwata ba ce?." Kai tsaye ya ce, "Sirikarki ce ba anwa ba, bana son kara ta arya. Ki rakata ki dawo ki same ni." Didi ta yi dariya ta girgiza kai ta ce, "Sai ka fito dani" ta fa a tana arasawa ban akin bata sake ce masa komai ba amma ya bata dariya wallahi, shi lallai ga mai matar so. Nayla ta kalla bayan sun shiga ban akin cikin kulawa ta ce, "ki daure ki shiga cikin ruwan nan ki zauna har ya huce, in ya huce ki yi min magana za a sake ha a wani. Amma sai kin daure akwai ciwo Nayla, shine ka ai zai taimakeki." Nayla tana jin ta dai bata ce komai ba Didi ta fito ta bata waje. Daman ko bai ce ba bata yi niyar tsayawa ba ta san dole Naylan ma zata ji nauyi, itama kuma baza ta iya tsayarwa ba. A tsaye ta same shi ya dafe kai idanunsa a lumshe, ta bi shi da kallo ganin fuskarsa ta rame ta ce, "akwai abinci a motarka wanda na zo dashi, mu je ka ci kafin ta fito." A sanyaye ya ce, "bana jin yunwa, kaina yayi nauyi sosai." "Kana jin yunwa Omar, mu je ka ci sai ka sha magani." "Don Allah ki yale ni." "Bazan yale ka ba." "To bazan ci ba sai na tabbatar ta samu lafiya" ya fa a yana fita daga akin ta girgiza kai kawai bata ce komai ba. Ta jima a zaune tana jiran Nayla kafin ta mi e ta wasa ofar ban akin ta ce, "Nayla ki aura towel zan kawo wani ruwan." Fita tayi ta auko wanda ta dafa ta dawo ta wasa ta ce, "Nayla kin gama?." Nayla murya a sha e ta ce, "Didi ki shigo." A hankali ta tura ban akin ta shiga, Didi ta zubar da ruwan ta sake zuba wani ta ce, "ki kuma shiga Nayla." Nayla ta fashe kuka ta ce, "Didi bazan iya ba, akwai ciwo sosai, na gaji." Didi tace, "yi ha uri, shi zai saka ki daina jin ciwon, ki yi ha uri ki shiga. Gashi nan na raba miki biyu, ga wani nan a bokiti sai ki yi wanka" ta fa a tana sake fitowa ta barta. Lokacin da Didi ta fita key in motar Omar ta auka ta je ta auko abincin ta kawowa Umma dan ta ci. A kusa da Umman ta zauna kafin ta koma wajan Nayla ta same ta ta fito tana zaune akan stool akin