Sashe 50
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayla ta mi e ta ce, "Sannu Didi, babu abinda ki ke so?." Kai ta girgiza alamun babu Nayla ta ce, "Ina zuwa" ta fa a tana fita daga gidan. Motar ta koma ta nufi gidan kai tsaye, ta tsayar da motar a ofar gidan ta tarar da an kulle gate in ta bu ofar ta shiga. Yana nan inda yake a zaune ya dafe kai yana wani irin huci har sautin sa tana ji. Wuce shi tayi bata ce komai ba ta shiga akinta ta jawo trolly bag tana zuba abinda ta san zata iya zubawa wanda zai yi mata amfani, ta auki laptop inta da tap inta, ta jawo jakar tan ri e da sauran kayan a hannu ta fito. arasowa ta yi inda yake, ta kalle shi ta ha iye yawu acin rai ta ce, "Na gode da kar ar aurena da ka yi saboda Didi, yanzu ina so ka rabu da aurena saboda nima na ce bana so, ina so ka rabu dani saboda bana so ba dan wani ya yi maka dole ba, bana son zaman auren kamar yadda baka so. Na gode da zaman da muka yi da kai matsayin mata da miji. Zaka iya kar ar number wayata a wajan Didi ka tura min saki ba sai ka wahalar da kanka ka rubuta ba! Sai wata rana" ta fa a tana jan jakarta fita daga falon, ta saka jakar a bayan mota ta ajjiye komai na hannunta ta shiga gaban motar taja motar ta fita daga unguwar gaba aya. KRB3P026 Arewabooks@nanahaleema11. Usman Umar shine sunan mahaifin su Omar, asalin kakanin su an garin Gombe ne amma iyayen su da shi kansa a Kano aka haife su. Yana da an uwa guda hu u har shi biyar kuma dukkan su maza ne dan mahaifiyarsu bata ta a haihuwar mace ba. Matarsa mai suna Saudat ita kuma asalin su buzaye ne haihuwar asar Chad, iyayen su dukkan su a can aka haife su, kana ganin kammanin su ka san ba an nigeria bane saboda kyau da gashi. Kasancewar mahafiyar su ta yi aure a nigeria hakan ya saka duk aka haife su a Kano suke kuma zaune a Kano. Su hu u ne mata, sai yayan su namiji guda aya wanda ya kasance shine babba a cikin su. Tun farkon ha uwar Usman da Saudat Allah ya ulla ala auna da soyayya a tsakanin su cikin lokaci ka an, har ta kai ga ta gabatar dashi a matsayin wanda take so kuma zata aura. Dangin Saudat kowa ya nuna sam baya son Usman, dan kallo aya zaka yi masa ka fassara shi a mutum mara kirki, sannan a kammani da zubin sa ya nuna hakan. Saudat ta nuna ita dai shi take so kuma shi zata aura, an uwanta da kowa nata ya nuna baya son auren amma ita ta nuna shi take so kuma shi zata aura. Kasancewar inda mahaifiyarta ta fito ba daga nigeria bane da ta ga ta dage akan shi take so bata takura ba ta saki maganar. Dagewar da tayi a kai ya saka dole aka daura musu aure ba dan wani nata yana son wannan aure ba sai dan babu yaddda za su yi da ita ne. A gidan gado Saudat ta tare, gida ne da dukka su uku suke aure a ciki, harda space in sauran biyun da ba su yi aure ba. Gida ne mai akuna da yawa amma ban aki biyu ne kacal a gidan kuma a tsakar gida yake. Kasancewar iyayen Saudat suna da rufin asiri sam basu ji da in wannan gida da arsu ta tare a ciki ba. Bayan auren Saudat da Usman sai asalin halinsa ya fara bayyana, mutum ne mai shaye-shaye, kaf danginsa haushinsa suke ji dan lokacin da aka bashi Saudat har mamaki abin ya basu saboda sun san ba a kintse yake ba. Saudat ta fara shiga damuwa matu a, dan baya tashi dawowa sai dare kuma a daren da yar in bai mata duka ba, garin dukan ta da yake yi ta yi arin cikin ta ne farko. Bayan wani lokacin iyayen Saudat suka rasu nasa iyayen su ma suka rasu ya rage basu da kowa sai an uwa. A wannan lokacin Saudat ta haifi Aisha wacce akyar aka iya rainon cikin ta saboda wahala, duk da bata rasa ci da sha a gidan ba amma ta rasa farin ciki mai yawa. Bayan haihuwar Aisha kamar ya nutsu ya daina komai, amma sai aikin yiwa yaran mutane ba'a da jafa'i, ko wanne yaro an iska yake kiransa kuma mara tarbiyya. Matarsa Saudat sam bata jin da in wannan kalaman na sa, amma ya riga da ya saba ko magana zai yi sai ya ha a da an iska ko tsinanne. Ita kuma tana gujewa Aisha da ta haifa, kar bakin da yake yiwa yaran wasu ya fa a kanta. A cikin wannan yanayi Aisha ta taso kasancewar yana matu ar son Aisha babu abinda baya yi mata, komai yana siya mata na yara da duk abinda zata bu ata. A haka ta fara tasawa cikin kula da tarbiyyar mahaifiya. Sai dai kyara da hantarar mutanen gidan, dan zuwa lokacin sauran mazan duk sun yi aure. Matan gidan sai suka ha ewa Saudat kai, saboda ta fi su kyau da jiki mai kyau sai suke ba in ciki da haka. Babu damar Aisha ta fito tsakar gida koda rarrafe ne sai tsawa da duka. A haka aka cigaba da rayuwa, Aisha da shekara hu u a duniya Allah ya kawo cikin Omar a lokacin da ba a yi tunanin zuwan sa ba. Da yake Saudat tana fama da rashin lafiya mai tsanani wacce take tashi a kai a kai ba a yi tunanin zata iya sake haihuwa a wannan yanayi da take ciki ba. Bayan ta haihu aka sakawa yaro suna Omar, sunan mahaifin Usman kenan. Da kanta ta kaiwa an uwata shi amma babu wanda ya iya aukarsa, har gwara anwar ta Saroot a lokacin bata yi aure ba yarinya ce, ta nuna ya burge ta saboda ya yi kama da an Chad gaba aya. Gaba aya ba sa son yaranta, Saroot in ce kawai ke iya yiwa Aisha wasa har ta auki Omar. Haka take zaune cikin yanayi na damuqa kala-kala, ga damuwar miji, ga damuwar zaman gidan yawa, ga damuwar basa sonta, ga damuwa an uwanta. Tana matu ar son Omar, tana aunar Omar saboda yana kama da ita, aunar da take masa ya saka take kiransa da Ashiq ko ta ce Habibi saboda son da take yi masa. A haka ta cigaba da rayuwa yau da lafiya gobe babu. Tun bayan ta yaye Omar ciwo ya matsa mata, yau lafiya gobe babu lafiya haka ta dinga rayuwa kamar baza ta tayi rai ba. A haka har Omar ya kai shekara biyar zuwa lokacin Aisha tana primary school dan ta girma tayi tsaho sosai. Omar yana da shekara shida a duniya mahaifiyarsu ta bar duniya, an uwanta sun ji mutuwarta sosai, sun kuma sake tsanar mahaifinsu Aisha saboda a ganin su shine silar raba su da ar uwarsu. Kafin rasuwarta ta barwa Aisha amanar aninta, duk da yarinya ce amma maganar ta ratsa ta sosai tana ta kuka tana ri e da hannun mahaifiyarta. Kaf gidan babu mai kula da lamarin Omar da Aisha sai shi mahaifin na su, babu wanda yake damuwa da maraicin su kowa sabgarsa yake yi dan zuwa lokacin mutum biyu sun tashi gidan ya zama saura mutum uku. Hakan ya saka Aisha take rayuwa cikin ka aici ba uwa kuma babu dangin da zasu ja ta a jiki su nuna mata auna da soyayya. Ita ka ai ke nunawa ananinta soyayya, gashi da rigima ita ka ai take iya rarrashinsa tana kuka yana kuka. Wani lokacin baya daina kuka har sai mahaifinsu ya dawo. Zaman gidan gaba aya baya yi musu da i, ga abi'ar mahaifinsu har lokacin tana nan bai daina ba hakan ya saka suka zama marayu na asali wanda basu da wani gata sai na Allah. A haka suke cigaba da rayuwa, Aisha tun tana arama ta iya dafa abinci saboda babu mai damuwa da sun ci ko ba su ci ba, dole ita zata yi ko dan Omar. A haka suka cigaba da rayuwa har Omar ya shiga primary school da kuma islamiyya. A cikin wannan yanayi ciwo ya kwantar da Baba saboda shan tabar da yake ta ta a masa hunhu, daga nan bai sake samun lafiya ba har ya bar duniya. Rasuwar su sai ta sake zamar musu sabon maraici domin kuwa babu wanda yake kula dasu duk da lokacin sun girma ba kamar Aisha. Aisha tana da shekara goma sha biyar, Omar yana da shekara goma da an watanni. A lokacin ne Kawu Sulaima kasancewar shi ne na tsakiya a cikin su ya ce zai aurar da Aisha dan bazai iya kula da ita ba, ta dinga kuka tana bata so, a lokacin sai ya ce bazai sake mata magana ba ta zauna a haka har arshen rayuwarta. Haka suka cigaba da zaman gidan babu da i ko ka an, abinci ma wahalar samu yake musu saboda sai anga dama za a basu abinci, wani lokacin ragowar da an uwan su suka rage za a basu. Rashin wannan jigogi da suka yi a rayuwarsu da rashin mai nuna musu soyayya sai tarbiyyar Omar ta fara gur acewa, ga yanayin gidan da suka tashi zagi kamar gidan maguzawa, yara da manya dan su yi ashar aramin abu ne a wajan su. Omar sai ya zama in aka tura shi makaranta ba makarantar yake zuwa ba yawo kawai yake tafiya. A haka ya fara shiga cikin yaran unguwa ata gari yana zama, in Didi tana nemansa ma kai tsaye can zata je kuma zata ganshi. Omar sai ya zama yana ara shekaru yana girma baka iya ka tan wara shi ba, duk dukan da zaka yi masa ba zai bu e baki yayi magana ba. Ya sha duka a wajan an uwan mahaifinsa da matar Kawu Babba wanda ya kasance shine babba. Abu ka an zai yi su yi masa dukan tsiya. Baya magana da kowa sai Aisha kawai wacce ya yiwa la abi da Didi.