Sashe 100
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akinsa kamar ko yaushe. Bai dawo ba har magriba, tana zaune a falo ta ji ana buga gate in gidan. Ta yi tunanin Salma ce dan sun yi da ita zata shigo, dan yanzu ta fara aikin asibiti ba ko yaushe take zama a gida ba. Tana bu e gate in ta ga Mama da Jalila, cikin farin ciki ta rungume Mama ta ce, "Mama sannu da zuwa, yaushe ki ka zo Kano? Jalila sannu da zuwa" ta fa a cikin tsananin murnar da ta kasa oyewa. Tare suka shiga falon Nayla tana ta murna. Mama sai kallon Nayla take yi ganin ta canja ta sake yin haske, ga wani shegen hamshi da take yi kana kallon ta zaka ga suffar amare sabon aure a tare da ita. Ruwa ta kawo musu da lemo ta zauna ta ce, "Mama ban san zaku zo ba, yaushe ku ka zo Kano Sis?." Jalila ta ce, "jiya mu ka zo, tun safe muka so mu zo nan in sai mu ka je unguwa." "Ina Jalil kuma?." "Yana kaduna wajan Ya Jawad." Nayla ta kalli Mama da ta ke binta da kallo ta ce, "Mama baki ce min komai ba." Mama ta an yatsine fuska ta ce, "to gani nayi duk kin canja, kin rame, anya kina jin da in zaman gidan nan?." Nayla da mamaki ta ce, "Rama kuma Mama? Ni ce na rame in?." Jalila ta ce, "gaskiya dai nima ban ga rama ba, sai wani kyau da naga kin yi, mai Yaya Omar in yake baki?." Mama ta ce, "Ku dai ba ku gani ba, amma ni tabbas na ga kin rame, kuma bazan juri ganin ki cikin wahala ba. Tunda baya son zama dake ya sake ki mana, kema ai ba son shi ki ke yi ba, tunda bazai iya kula dake ba ya sake ki ki auri wanda suke sonki!" Ta fa a cikin murya mai amo a lokacin Omar ya shigo falon da sallama ya ji duk abinda ta ce. Nayla ta amsa sallamarsa jikinta a sanyaye, suka ha a ido dashi ya auke kai ya kalli Mama, bai san Mama ba amma a yadda ya ganta ya san danginsu Nayla ce, kuma yana ganin Jalila ya san anwarta ce dan suna an kama ka an. Nayla tayi hanzari ta ce, "YaMar ga Mamana, ga kuma Jalila anwata mai bina." Kafin ya yi magana Mama ta ce, "tsabar lalacewa wai mijin ata ne ma bai sanni ba bai san anwarta ba, wannan wanne irin aure ne? Aure ko auren addara" ta mi e tsaye tana kallon Omar da ya ke tsaye yana jira ta gama fa ar abinda yake bakinta. Ta bishi da kallon wula anci ta ce, "Kai! in baka son Nayla ka saketa mana ana dole ne? Duk ka bi ka lalata min yarinya, a haka ka aureta? Kalli yadda ta rame ta lalace saboda banzan addararren aurenka da yake kanta. Ta saba kwana a gida mai ac da kayan more rayuwa, ka duba kangon da aka ajjiyeta. A haka ta ha ura tana zama da kai saboda dalilin mahaifinta duk da ita ba tsarar ka ba ce, kaima ka san Nayla tafi arfinka, ko a mai gadin gidan ta....." Cikin aga murya Nayla ta ce, "Mama me ki ke fa a haka?." Mama ta juya ta kalli Nayla ta ce, "dakata! Ki bari na nuna masa matsayin da yake dashi kodan ya daina ji da kansa, dan an bashi aurenki rana tsaka ya daina ganin kamar auren sadaka aka bashi" ta dawo da kallon ta ga Omar da yake kallon ta idanunsa yam a kanta ta ce, "Nayla bata sonka, bata son rayuwa da kai, tana zaune da kai ne saboda mahaifinta. Ka sake ta kawai tunda baka sonta, daman rayuwar gidan ka bata dace da ita ba, Nayla ba kalar matan da zaka mallaka bane, Nayla ta fi arfin ka ta wuce ajinka. Matu ar ina da rai sai na raba wannan aure, sai na tabbatar....." Nayla ta katse Mama cikin kuka ta ce, "Mama ki bari, ki bari Mama don Allah. Bana so! Don Allah ki daina fa ar wannan maganar, Don Allah ki daina, bana son ji!" Ta fa a cikin kuka mai tsuma zuciyaa. "Sai na fa a, ya dace dake in ne? Auren an daban har wani farin ciki zai bayar? Farin ciki ko takaici?. Kinga Nayla, ki daina yi masa kara, ki bu e baki ki fa a masa bakya sonsa! Ya rabu dake ki auri wanda ki ke so yake sonki, amma ba wannan bolar ba." Nayla ta rasa abinda zata ce kawai ta zube a wajan ta fashe da kuka. Jalila ta ce, "Mama meye haka? Me ki ke fa a ne Mama?." Mama ta tsinke Jalila da mari, ta nuna ta da yatsa cikin fusata ta ce, "ba da ke nake magana ba, kar ki sake saka min baki." Juyowa tayi zata sake masa magana amma sai ta kasa furta komai ganin yadda Omar ya canja lokaci guda, idanunsa sun canja launi zuwa ja lokaci aya, fuskarsa kamar an saka abu an tsuketa waje aya haka ta koma, har ja ta yi kuma ya zuba mata ido yana jira ya ji abinda zata sake cewa. Kasa magana Mama ta yi ta auke kai daga kallonsa, ya girgiza kai ya bu e baki zai yi magana Jalila ta katse shi ta ce, "Don Allah Yaya Omar ka yi ha uri..." ta juya ta kalli Mama ta ce, "Mama don Allah ki daina fa ar haka.." Motsawa ya yi ka an zai yi magana suka ha a ido da Nayla da take kuka, sai ya fasa maganar dan in ya bu e baki bai san abinda zai ce mata ba. Sai ya wuce kawai bai ce komai ba ya shiga aki ba tare da ya sake waiwayonsu ba. Nayla ta mi e ta araso kusa da Mama tana kuka ta ce, "Mama meyasa zaki ce haka? Mama meyasa zaki yi min haka!?." Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "na yi ne dan ya tabbatar da matsayinki da nashi ba aya bane, kuma sai ya sake ki wallahi, baza ki cigaba da rayu wa dashi ba." "Ina son shi Mama, babu inda zan je, zan cigaba da rayuwa dashi koda zai dinga yankar naman jikina kullum. Kuma Mama ban ji da in abinda ki ka yi ba, ban ji da i ba ko ka an" ta fa a tana kuka sosai. Mama ta ce, "ko kukan jini zaki yi sai ya sake ki, in kinga auren nan naki ya ore to mutuwa nayi Nayla. Duk son da kike masa bai saka ya raga miki ba, wula anta ki yake yi kamar ya samu baiwa. Ai ba gajiya muka yi dake ba, ka ara ce ta kai ki zama a wannan gida kamar gidan kaji. Lokaci ya are wallahi, dole a raba auren nan!" Ta fa a da arfi tana kallon Nayla. Nayla ta kasa magana, sai girgiza kai take yi hawaye yana zuba daga idonta. A guje ta juya ta bar falon zuwa aki tana kuka. Jalila cikin damuwa ta ce, "Haba Mama, meye haka kika aikata don Allah?." Mama ta harare ta suka fita daga gidan bata sake magana ba. Dan wallahi baza ta ta a bari auren Nayla da Omar ya je ko ina ba, ta bada goyan bayan auren ne saboda Nayla ta sha wahala, to akan me zata zo ta ga tana jin da i har ta yi ki a tayi kyau haka? Ina ai bata isa ba, ba kyau ta kawo ta tayi ba, ba haske da iba ta kawo ta tayi a gidan Omar ba. Nayla tana shiga aki wayarta tayi ara, da ta duba ta ga sunan Abiy sai ta auki wayar tana kuka ta ce, "Hello Abiy." Abiy ya ce, "Mamana kukan me kika yi? Mamanki ta zo gidanki?." Nayla ta ce, "Abiy ina yini." "Lafiya lau, Ki amsa min mana." "Yanzu ta fita." "Wani abun ya faru ne?." "Babu komai Abiy." "Ita da wa suka zo?." "Jalila." Abiy bai sake magana ba ya katse kiran. KRB3P059 Nayla haka ta cigaba da kuka har aka yi sallar i'sha, ta fito falon ta tarar ya ajjiye mata abincin da ya saba siyowa ko yaushe. Ko kallon abincin bata iya yi ba, ta shiga akinsa da sallama ta same shi a zaune a gefen gado ya yi shiru yana kallon asa. Amsa sallamar ya yi ba tare da ya ago ba, ta arasa a hankali cikin sanyin jiki ta zauna a gefensa. Shiru ta yi bata ce komai ba kafin ta sauke numfashi ta ce, "YaMar ka yi ha uri da abinda Mama ta yi maka azu don Allah, ban san meyasa Mama ta ce haka ba, amma don Allah ka yi ha uri." Idanunsa ya ago ya kalle ta, Nayla ganin idanunsa sun yi ja ta san ransa a ace yake sai ta ji babu da i, ta san Mama ce kawo wannan acin ran ba tare da ta san dalilinta na yin haka ba. Cikin sha ewar murya Omar ya ce, "kin ji na yi magana ne?." A sanyaye ta ce, "A'a ban ji ba." "To meye na bani ha uri? A cikin kalamanta akwai kuskure ne?..." Nayla ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Omar ya ce, "Duk abinda ta ce gaskiya ne, ban cancanci zama dake ba, kuma sona ki ke yi ba." Nayla ta girgiza kai a raunane ta ce, "Allah ina sonka, wallahi ina sonka sosai." Ya girgiza kai shima yana kallon ta ya ce, " azu ma kin fa a da kan ki Jidda, azu da bakin ki kin fa a bakya sona. Dah na yi tunanin zamu iya rayuwa ko da bakya sona saboda ni ina sonki, ban auka abin yayi girman haka ba." Nayla ta ru e tana girgiza kai ta ce, "Wallahil azim in sonka, ina sonka YaMar, ina aunarka. Na so ka tun kafin ka soni, na so ka tun daga ranar da ka fara yin murmushi a kan idanuna, na sonka son da ban san adadinsa ba, na so ka son da ban san yawansa ba, kuma har gobe ina sonka. Allah shine shaidata, Jidda da Salma sune shaida,