Sashe 10
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bata da mahaifiya, ga mahaifi ta ma ya yi mata nisa tunda ta bar asalin garin su. Don Allah ka zamar mata uwa da uba, yayanta kuma mijinta. Don Allah Omar kar ka bar Nayla ta zubar da hawaye a zaman ku da ita. Ka bata dukkan kulawar da ka san zaka iya. Shiru ya yi bai ce komai ba amma yana mamakin kalmar marainiya in nan da Didi take fa a, shi ba maraya bane kenan ko kuma iyaye sun fi iyaye ne? Ko mutuwa tafi mutuwa ne da zata dinga maimaita masa marainiya ce?. Didi jin ya yi shiru bai tanka ba sai ta ji da i a zuciyarta dan bata so ya yi abinda rai zai aci. Didi ta ce, Allah ya baku zaman lafiya ya orar da zamanku har aljanna. Da ita da AbdulHamid da salma suka amsa da amin ban da Omar. Didi ta ce, to zamu wuce mu dare yana yi. Salma mu tafi sai mu sauke ki gidan Hajja? Ta fa a da sigar tambaya. Salma ta ce, Eh Didi, bara na auko kayana ta fa a tana tashi ta shiga bedroom. Jim ka an ta dawo Didi ta mi e AbdulHamid ma ya mi e tsaye suna yiwa Nayla sallama. Didi ta kalli Omar da bai motsa ba ta ce, ka zo mu je ka kulle gidan. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, zan zo. Ka taso Omar, nan ba gida ba ne. ewa ya yi ya bi bayan ta Salma da take tsaye tana su bayan sun fita ta kalli Nayla ta ce, amarya naga angon na ki ya an yi hankali babu laifi. Ta amma Ina tausaya miki shiga hannun wannan mutumin, wannan ai sai ya alla ki g da biyu. Nayla ta ago ido ta kalle ta, Salma ta yale da dariya ta ce, Amaryar Ango mai zuwa gidan amarya da ananun kaya. Nayla sai tayi murmushi kawai Salma ta ce, Sai mun yi waya ta fa a tana fita da sauri. Nayla ajiyar zuciya tayi gaba aya zuciyarta babu da i haka take jin jikinta. Tayi shiru tana jinjina girman iko na Allah, wato daman ya addara zata auri Omar shiyasa ya saka mata sonsa a zuciyarta, sai gashi auren ya zo a lokacin da babu wanda ya yi zato babu wanda kuma ya shirya zuwan sa. Motsinsa ta ji bata ago ba ta sake saukar da kai kasa, shi kuwa chakewa ya yi daga gefe yana kallonta yana maimaita kalmar matarsa a zuciyarsa. Nayla bata san yana tsaye ba sai ta ago ido suka ha a ido tayi saurin sauke kai asa, Omar ya ta e baki yana sake girgiza kai. Indai ya kalle ta babu abinda yake zuwa ransa sai fa an da Didi tayi masa a gabanta, yana kallonta abinda yake zuwa zuciyarsa kenan hakan ya saka yake an jin haushinta ka Kallon ofar da take bayan sa ya yi yaga akin yayi daidai da wanda Didi ta ce masa shine na sa, ya mur a handle akin ya bu e yana kallonsa ba tare da ya shiga ba. Sake arewa akin kallo yake yi zuciyarsa gaba aya babu da i bai san abinda yake damunsa ba. Warning yake so ya yiwa Nayla amma kuma ya kasa ko motsawa yana kallon akin, zuciyarsa tana fa a masa yaje ya yi mata warning akan zaman sa tare da ita a gida aya, kar ta shiga harkarsa shima bazai shiga ta ta ba. Samun kansa ya yi da shiga akin yana jin wani iri wai shine ya yi aure ya tare da matarsa a gida aya. Bai ta a kwana a wani waje tare da wata ba, ya zauna a gida aya ma na wani an lokaci shida mace bai ta a ba sai lokacin Narma da ya ta a zama a gidan da take. Amma kwana dai in ba Didi ba bai ta a yi ba shiyasa yake jinsa gaba aya wani iri. Lamarin yazo masa ba o ya kasa sakewa gaba aya. Nayla tana ganin ya shiga bai mata magana ba daman bata kawo a ranta ma zai mata magana ba, ta tashi ta shiga aki tana sauke numfashi. Ita har yanzu tsoronsa take ji sosai, dan da ya yi mata magana lokacin da ya shigo zata iya firgicewa. Ita kanta akwai rashin sabo na ke ancewa a gida aya ita da wani namijin a duniya, sai take ji gidan ya yi mata girma sosai. Numfashi ta sauke ta arasa ta zauna akan gadon tana mamaki wai itace matar Omar. Shima a angarensa hakan take, gaba aya ya kasa sakewa sai kalle-kallen akin yake yi. Ban akin da in ya bu e yana kallo kafin ya bar wajan ya zauna ya har e hannayensa ya rasa abinda zai yi. Haka gidan ya zauna shiru kowa yana nasa akin yana na sa tunanin da ya damu zuciyarsa a hakan har dare ya yi. Nayla tayi bacci amma shi ya kasa bacci sai juyi ya ke yi saboda gaba aya shi in ba gidan su ba bai saba kwana a wani waje ba. Da yar shima bacci ya auke shi. Washe gari Nayla ko da ta farka bata ji motsinsa ba gaba aya, bata sani ba ko yana nan ko baya nan bata sani ba. Wayarta ce tayi ara ta duba ganin sunan Salma sai ta auka a nan take shaida mata an aiko abinci daga gidan Hajja ta bu e ta kar a. Fita tayi ta bu e gate in ta kar a ta kulle ta kuma koma ciki. A kan dining ta ajjiye tana kallon akin na sa zuciyarta na wani irin bugawa a hankali. Ajiyar zuciya tayi ta koma aki ta yi wanka ta shirya cikin shigar doguwar riga ta fito ta shiga kitchen ta dafa ruwan tea ta zuba ta fito tana sha. Abiy ne ya fa o mata a zuciyarta, ta auki waya a sanyaye ta kira shi amma bai auka ba, Ta sake kira ba a auka ba sai ta ajjiye tare da ajiyar zuciya. Rashin aukar da Abiy bai yi ba sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abinda yake yi mata da i, tana kallon wayarta ko kiran Abiy zai shigo amma bai shigo ba. ofar ta ji anyi an shigo babban falon da mamaki take tunanin daman baya nan kenan, kuma waye ya bu e masa gidan yanzu?. Tana jin motsi da alama ba shi ka ai bane dan taji yana magana cikin bada umarni. Sai da yazo shiga akin da ya kwana sannan ta ji ya ce, Didi ce ta saka ku wannan aikin?. Muryar Bash taji yana ce, itace. Tsaki ya yi ya ce, na rasa meyasa Didi ta raina ni wallahi ya fa a yana bu akin ya shiga suka bi bayan sa da kaya masu yawan gaske. Ba jimawa suka fito, Bash ya kalli inda Nayla take zaune dan bai kula da ita ba ya ce, Antyn mu barka da safiya. Nayla sai ta ji wani iri, wai Antynsu bayan tana da tabbaci ya girme mata. Ta daure ta ce, barka. Fita Bashir ya yi shi kuma ya fito da waya a kunnensa yana cewa, meyasa ki ke kin haka? Meyasa ko yaushe sai kin yi min dole?. Yanzu meye na saka su Bashir su shiga gida har akina su ha a kaya su kawo min? Na saka ki ne? Ko nace ina da bu atar hakan?. Shiru ya yi alamun tana bashi amsa kafin ya ce, Ya dai isa haka, na gaji da kawar da kai. Dan kin ga Ina yalewa ne ma ya saka ki ke yi min abinda ki ke so. Shiru ya sake yi kafin ya ce, yana fa a ya yanke wayar ya saka a aljihu yana kallon wani wajan daban. Yana juyowa suka ha a ido da Nayla da take kallonsa tana mamakin shi wannan Didin ma bai bari ba a fannin masifa. Suna ha a ido ta ji gabanta ya fa i, da yar ta daure ta ce, Ina kwana. Kallonta yake yi kamar bai santa ba, ya tsayar da idanunsa yam a kanta yana kallo, shi kansa bai san meyasa yake son kallonta ba kawai ya samu kansa a kallon nata. Tsaki ya yi kafin ya janye idanuasa ya yi banza bai amsa ba. Nayla ta ji babu da i a zuciyarta ta kawar da kai hawaye na cikowa idanunta. Juya spoon in take yi a cikin mug in hannunta jikinta ya yi sanyi akan abinda ya yi mata. Sake kallon ta Omar ya yi kamar mai tunanin wani abu sai ya fita daga wajan gaba aya. A bayyane ta ce, matar cushe bata ta a daraja ta fa a hawaye na sakkowa daga idanunta. Kallon abincin ta yi da aka kawo daga gidan Hajja a bayyane ta ce, gaisuwa ma bai amsa ba balle na ce ga abinci, nima karanbani ne irin nawa na san bazan amsa ba ta fa a tana goge idanunta cike da tausayin kanta. Wayar ta ce taji tana ara ta kalla ganin Salma ce sai ta auka cike da tsokana Salma ta ce, Amarya, bani labarin first night in mana, ya komai dai normal?. Nayla ta sauke numfashi ta ce, ki daina wannan batu don Allah Salma. Salma jin muryarta na rawa sai ta ce, Nayla lafiya ki ke kuka?. Babu komai Salma. Ya Hajja? Bata mu gaisa. Muryar ta ki tana rawa zan bawa Hajja? Ki daidaita muryarki sai ku gaisa. Bata. Da aka bawa Hajja wayar ta ce, Hauwa u kin yini Lafiya?. Hajja Ina kwana. Lafiya lau amarya. Ya kwanan ba on waje?. Alhamdu lillah Hajja. Ma sha Allah. Allah ya baku zaman lafiya mai orewa. Ki yi ha uri da duk abinda zaki fuskanta, kin san halin mijin da kika aure tun kafin ki aure shi. Ki daure ki yi masa biyayya kar wani tunani na banza ya shiga ranki, zaman aure ibada ne sai kin daure zaki kai ga nasara. Nayla da take hawaye ta ce, to Hajja. hajja ta ce, yauwa, ko gaishe shi ki ke yi in bai amsa ba ki sake gaishe shi, shima in bai amsa ba gobe ma sake gaishe shi, in bai amsa ba sake gaishe