Sashe 21
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce, "kina bada mata Nayla, Allah rashin sakewa nan da baya yi da laifin ki. Amma bara ayi sallah zan zo mu tattauna." Nayla ta ce, "Didi ai marmari daga nesa ne." Suka yi dariya a tare kafin Didi ta kashe wayar Nayla ta cigaba da kallon kayan. Sai a lokacin taga ku i a cikin kaya har dubu hamsin. Nayla ta wara ido tana irga ku in ta ce, "Lallai su Damisa manya, an san a bada kayan sallah da ku inki." Salma ta kira a waya aka yi sa'a suna tare da Twiny hira ta bar e a tsakaninsu tana basu labari da nisha i su kuma suna ta tsokanarta. Dawowarsa da taji ya saka ta kashe wayar ta tashi ta saka hijjabi ta fita da niyar yi masa godiya. A zaune ta same shi yana cin Apple da take hannunsa. Zama tayi a arare ta ce, "Na ga sa o na gode Allah ya saka da alkhairi." Bata ji ya amsa ba daman ta san baza ta ji ba ta mi e tsaye a lokacin Bashir ya shigo da kaya masu yawa. Ajjiye kayan ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Antyn mu an sha ruwa lafiya." Tayi murmushi ta ce, "Lafiya lau, ya ka ke?." "Lafiya lau." Daga haka bata sake cewa komai ba ta wuce zuwa kitchen. Bash ya kalli Boss in nasa sai ya ga kamar harararsa yake yi ya auke kai ya ce, "Tiger an kai kayan Abuja." Omar ya ce, "ya sanar da ni." Bash ya ce, "Damisa muna ta samun alkhairi cikin kwanakin nan sosai, wani abokina ya ce ya kamata mu yiwa companyn register saboda ba a san inda zai je gaba ba." Omar ya kalle shi ya ce, "nayi wannan tunanin nima, amma ban san ya abin yake ba." "Nima ban san a ina ake yi ba, amma in na tambaye shi zan sanar da kai, tunda har an fara kar ar kaya ana sakawa a store gwara mu dinga yiwa takalman kwali da Rc number da komai." Omar ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "in ka s amu ka sanar da ni." Nayla da take tsaye ta fito daga kitchen ta ji abinda aka ce ta araso ta ce, "Zan iya magana?." Kallon ta ya yi kafin ya ce wani abu ta ce, "Rc number a nasan wani ma'aikatan da suke aiki a ashin CAC inda ake yin number kenan, zan iya sakawa ayi number ba sai an nemi wani ba." Bash ya ce, "shikenan fa uwa tazo daidai da zama Antyn mu, abu ya zo har gida." Kallon da Omar ya yi masa ne ya saka shi ya mi e ya ce, "Damisa na koma company, sai ka shigo. Antyn mu sai da safe." Bai jira ta amsa ba ya fita saboda kallon da yake yi masa ya san ba kyau. Bai motsa ba kamar bai ji ma abinda ta ce ba, ganin haka sai ta koma tana mamakin hali na wannan bawan Allah. Shi kuwa Omar gaba aya haushi ta bashi, meye dalilin ta na zuwa yana tare da wani tana magana?, Ya saka ta ne ko kuma dole sai tayi magana Bashir yana wajan?. Tsaki ya yi yana nan zaune har goma na dare sannan ya mi e ya shiga aki. Kaya ya canja sannan ya sake fitowa ya same ta a tsaye tana aukar ruwa a fridge har lokacin hijjabin yana jikinta. Kamar zai yi magana sai ya fasa kawai ya fita dan ba a gidan zai kwana ba zai je ya saka su a gaba dole ayi aikin ko ba so. Har zai fita kuma sai ya da fasa ya dawo ya kalle ga ya ce, "ki rufe ofa." Abinda ya ce kanan ya fita. Nayla gabanta ya fa i a bayyane ta ce, "ba dai ba a nan zai kwana ba?." Sai kuma ta ce, "wata ila zai dawo sai dare." Maimakon ta je ta rufe sai ta koma ciki ta kwanta saboda kanta na ciwo sosai. Omar kuwa aiki ya saka ana yi sosai a company saboda sun kar i ku i mutane kuma babu kaya sosai a asa ga sallah na zuwa. Ganin idanunsa dole ya saka ake yi ko ba a so, ya bada ku i aka siyo abinci kar ma wani ya ce yunwa yake ji. Da yake daren azumi ne kuma goman arshe mutane suna ta kai kawo ana tafiya masallaci baza ka ce dare ya yi ba. A lokacin Goje ya shiga shagon ya kalli Omar da yake zaune yana ka afarsa. Goje ya ce, "Damisa akwai matsala." Ya kalle shi alamun me ya faru. Ya ce, "Wannan yaron Kb wanda ka yi silar zuwan sa prison ya fito, ya kuma yi alwashi a akan ka ko matarka. Ya samu labarin auren ka yanzu haka an sanar dani sun taro mutane zasu tunkari gidan." Omar kallon sa yake yi kawai jin abinda aka fa a masa, a hankali ya ce, "Meye sahihancin maganar?." "Darr Damisa, bazan kawo abinda ban tabbatar ba. Na fa a ne dan mu kwashi kayan aiki mu je mu nuna musu zaren ba kalar yadin bane." Omar ya mi e tsaye sai Tk da Bash ma suka mi e ya aga musu hannu yana kallon su ya ce, "a tabbatar da an gama aikin nan a daren nan, kar wanda ya biyo ni." Goje ya ce, "Amma Damisa zuwan mu yana da mahimmaci." "Kar wanda ya biyo ni!" ya fa a yana nuna su da yatsa tare fita kai tsaye ya nufi gidan. Nayla tana kwance a aki ta ji wata ara mai arfi da hanzari ta mi e zaune tana raba idanu, ta sake jin ar alamun ana arin bu e gate in gidan da arfin gaske. Gabanta ya fa i ta dafe irji ta ce, "Lafiya ake dukan gate in nan haka? Kai ashe na manta ban kulle ba" ta fa a tana mi ewa da yar saboda ciwon kai ta fito a hankali kamar munafuka. Tana zuwa falon aka sake dukan ofar da arfin har lock in ya cire tunda iya shi ka ai ne a jiki bata saka key ta kulle ba. Shigowar mutane take ji ana cewa, "Wallahi yau ko shi ko matarsa sai aya ya ba unci lahira. Ya yi silar zuwa mu prison shi ya zo yana zaune ya ma yi aure yana jin da in rayuwa, na rantse da Allah bai isa ba yau sai ya ba unci lahira." Nayla ta zaro ido gabanta ya fa i jikinta ya hau rawa a lokacin ta ji ana ta ofar falon. Tsalle tayi ta koma da baya cikin matu ar tsoro ta gudu ciki ta shiga aki ta shige can arshe jikinta na matu ar rawa tana hawaye. Motsi da ta ji a akin ne ya saka ta agowa a razane irjinta ya buga ta sake zabura cikin tsananin tsoro kamar wacce ta zauce. KRB3P011 Nayla a gigice take matu a hakan ya saka suna ha a ido da Omar da ya shigo akin a karo na farko ta diro daga kan gadon a hanzarce, cikin sacannin da bai wuce biyu ba ta zo inda yake ta ri e shi jikinta na rawa tana fa in, Tsoro nake ji, tsoro nake ji ka taimaka min zasu kashe ni. Yadda jikinta yake rawa zai tabbatar da gaske a tsorace take bata cikin nutsuwarta. Ta ri e masa riga gam hannunta sai rawa yake yi sosai. A karo na farko da hannunta yazo jikinsa shima na sa hannun ya je jikinta, duk da shima baya cikin nutsuwa hankalinsa a tashe yake yana tunanin ko wani abun ya same ta ya dawo gidan, sai da yaji ha uwar hannunsu a waje aya a jikinsa da zuciyarsa, duk da hannun nata rawa yake yi amma hakan bai hana shi jin ba on yanayi a tare dashi ba. Babu abinda zai same ki, ki nutsu ya furta a tausashe yana kallon yadda take kuka sosai kanta ko ankwali babu. Gashin ta yana cure a tsakiyar kanta ta aure shi da ribbon. Kamar ma bata ji me yake fa a ba har lokacin bata cikin nutsuwarta saboda tashin hankalin da taji yana arin tunkaro ta, kasheta fa taji ana zancen za a yi, to ba dole hankalin ta ya bar jikinta na wani lokaci ba. Nayla har lokacin hawaye ta ke yi tana ri e dashi ta ce, Tsoro nake ji, zasu kashe ni. Sun alla gate sun shigo, Ka taimaka min ta sake fa a a tsorace sosai tana ri e hannayensa duka biyun tana waige-waige. Abinda ya ji ya ratsa hannunsa mai kama da jan wuta shine ya saka shi yi mata tsawa ya ce, ba na ce ki nutsu ba! Ki saurara da wannan shirmen! Ya fa a da arfi ba tare da ya sani ba saboda shock in da ya ji ya ratsa hannayensa ya shiga har cikin jininsa ya zaga sa on ya tafi har walwarsa lokaci guda. Firgigit Nayla tayi ta tsaya cak tana kallonsa har lokacin jikinta bai daina rawa ba amma ta saki hannunsa babu shiri. Kallon ta yake yi kamar yadda take kallon sa tana share hawaye ya ce, babu abinda zai same ki, ki nutsu ki daina yi min shirme ya fa a yana fita ya bar ta a wajan jiki na karkarwa. A gefen gadon ta zauna tana ajiyar zuciya, tsoron da take ji ya ragu ganin Omar in yana nan amma har lokacin a tsorace take ta kasa sakewa gani take kamar zasu dawo su kashe ta in. Shi kuwa harabar gidan ya fita zuciyarsa na yi masa zafi akan abinda aka yi masa, yana fitowa harabar gidan ya tarar da Bash da Goje da Tk suna jiran fitowarsa. Yana ganin su ya ce, bana ce ku zauna kar ku fito ba?. Goje ya ce, Haba Damisa, an shigo har gonar mu kuma mu zauna muna kallo?. Tsaki ya yi ya ce, to da ku ka zo me zaku yi?. Umarnin ka mu ke jira, wallahi yau baza su kwana lafiya ba. Azumin gobe sai dai su yi shi a kabari. Hayaniya yake jiyo daga waje ya ce, su waye a waje?. Bash ya ce, masoya ne, sun ebo