Sashe 86
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a sanyaye ta ce, "Shi kuma me ya kawo nasa ciwon?." Dr ta ce, "Ana samun irin haka musamman ga saurayin da ya an kwana biyu bai yi aure ba kuma bai ta a sanin mace ba, su kan tsinci kansu a yanayi na zazza i da ciwon kai, ciwon ga i da jiri saboda kasancewar su ba i a wannan angare. Wannan shine ya jawo masa na sa ciwo, dan zazza i ya kama shi sosai har zafin jikinsa har ya fi nata. Shi ake kira da samartaka in ji manyan mu." Didi ta girgiza kai cike da gamsuwa Dr ta ce, "in sun warware ta koma gidan a ara mata hutu na at least kwana biyar zuwa sati aya haka." Didi ta girgiza kai cikin gamsuwa ta ce, "Yanzu tana Lafiya?." "Lafiya take, ta yi bacci. Shima kuma rashin sabo ne da zarar ya farka zai iya dawowa daidai sai dai rashin arfin jikin kawai, itace zata an yi jinya ka an." Didi ta ce, "na gode sosai." Dr ta ce, "babu komai aikina ne" ta fa a suna wucewa suka fita daga wajan. Didi ta dawo a sanyaye ta zauna cikin kunyar mijinta kamar ita ce ta aikata abinda aka ce. Tunanin halin da aka fa a mata suke take yi, Allah ya sani tunda Nayla ta dawo gidan Omar take tunanin wahalar da zata sha a hannunsa, haka kawai take ji a jikinta Nayla zata sha matu ar wahala a hannunsa dan Omar bai yi kama da ragon namiji ba. Babban abinda ya saka ta ji da i a zuciyarta tunawa da bayanin likita, godiya take ga Allah ya kasance Omar bai ta a aikata zina ba, ya gujewa sa awa Allah ya ri e kansa har sai da aka gama fa an zamansa da Nayla har ya amince da ita ya fara sanin a mace a kanta. Hakan ya yi mata da i sosai, dan yadda zamani ya lalace samarin yanzu ka an ne basu ta a aikata zina ba, an mayar da ita ado kamar ba ita Allah ya ce kar a kusanceta ba. Amma tausayin Nayla ya gama mamaye mata zuciya, daman ko shakka bata yi akan Nayla, ta san ita iyar warai ce da ta samu tarbiyya mai kyau. Ajiyar zuciya tayi, a lokacin gari ya yi haske sosai ma'aikata na shigowa asibitin wanda suka kwana kuma duk sun tafi. AbdulHamid ya kalle ta ya ce, "ko zan mayar dake gida ne kin bar Marmerh a hannun Umma, in ta farka ya za a yi da ita?." Didi ta ce, "to in na tafi waye zai kula dasu gaba aya? Da ace ma ya farka sai na tafi, amma bai farka ba shima bacci yake yi." "To yanzu haka za a bar jaririya a gida ba tare da mahaifiyarta ba? Ai sai da na ce ki taho da ita ko?." "Ban auka zamu jima haka ba, bara mu gani zuwa anjima in bai farka ba sai mu je ka kaini na dawo anjima." Bai ce mata komai ba ya yi shiru itama ta yi shiru cikin tausayin Nayla mai yawan gaske. Ganin arfe takwas na safe tayi Didi ta tashi ta shiga akin ta same su dukkan su suna bacci dan akin mai gado biyu ne. Ajiyar zuciya tayi ta arasa inda Nayla take ta dafa goshin ta taji babu zazza i a jikinta, ta dawo wajan Omar ta tsaya yana kallonsa. Dariya ce ta kubce mata ba tare da ta san dallin yinta ba, haka kawai ya bata dariya har sai da ta dara ta dafa goshinsa, a bayyane ta ce, "Bana tunanin Omar ya ta a kwanciya asibiti, kai bai ta a ba ma, amma gashi yau ya kwanta. Alhaji Omar manya, komai na su na manya ne" ta fa a tana dariyar da bata san dalilin ta ba ta fita daga akin. Kallon AbdulHamid tayi tana murmushi ta ce, "Ka yi ha uri Yalla ai, mu je ko?." Ya kalle ta ya ce, "da wa ki ka barsu?." "Zan dawo anjima sai na taho da Marmerh in." "Bai kamata ba, ya kamata ko gidan Hajja ki yi waya yarinyar nan awarta ta zo." "Ka san abinda ya faru na san ka ji me suka ce, bana son kiran mutane azo ana tambayar me ya same su, hakan babu da i kamar fallasa sirrinsu ne." AbdulHamid ya ce, "lalura ce ai ba wani abun damuwa ba, babu wanda ya wuce addara dan an sani ai ba komai bane. Haramci suka aikata ko me?." Didi ta ce, "mu je dai kawai, ance ai zasu jima suna baccin." Bai ce mata komai ba suka fita daga wajan tare. Didi koda ta koma a gaggauce ta yi wanka ta yi girki mai sau i da shayi da sauran abinda ta san zasu bu ata. Bata fi awa biyu da komawa ba ta dawo ita da Umma Saroot, dan itama hankalinta bai kwanta ba dan Didin bata ce mata ga abinda ya faru ba ta ce kawai basu da lafiya. Har lokacin da suka dawo dukkansu bacci suke yi, suka basu waje suka dawo wajen akin suka zauna akan kujera. Omar sai arfe biyu na rana ya bu e ido yana kallon akin yana so ya gane a inda yake a kwance. Mi ewa zaune ya yi cikin rashin wari amma ya ji da in jikinsa zazza in ya sauka sai dai rashin arfin jiki da bashi da ita. Kallon gefensa ya yi ya ganta a kwance idanunta a rufe da alama bacci take yi. Sakkowa ya yi daga kan gadon ya mi e tsaye a hankali yana yamutsa fuska, sai yanzu ya lura a asibiti suke ya an ja tsaki ka an, a rayuwarsa bai ta a kwanciya a asibiti ma amma saboda tonan asiri Didi ta kama ta kawo shi asibiti. arasawa ya yi wajan Nayla ya dafa kanta ya ji babu zafi a jikinta gaba aya, ya ta a wuyanta nan ma babu zafi ko ka an. Kanta ya shafa da gashin ta yake baje a kan gadon yana kallon fuskarta. Kiss ya yi mata a goshi yana shafa fuskarta yana ganin yadda take a kumbure har lokacin, ya sauke ajiyar zuciya yana kallon ta. Bu akin aka yi ya kalli wacce ta shigo, ganin Didi ce sai ya an yi tsaki ya ce, "Wai daman asibiti mu ka zo? Ni na ce miki asibiti zaki kawo mu?." Didi ta ce, "ikon Allah, kai ka tashi daga ciwon ma baza ka daina masifa ba? Da ba mu zo asibitin ba ya ka ke so nayi da ku gaba aya?." auke kai ya yi daga kallonta a lokacin Umma Saroot ta shigo jin maganar Omar. a ido suka yi da ita Marmerh na hannunta ta ce, "Omar ya jiki?." Ransa ya ji ya aci matu a, ya kalli Didi ya girgiza kai kawai bai ce komai ba amma haushinta yake ji, daga kiranta dan ta taimakawa Nayla sai kawai ta yi masa gayya? Ya tsani rashin sirri a rayuwarsa, yana girmama sirri sosai a rayuwa, wannan dalilin ya saka bai ta a tunanin aikata zina ba, saboda gani yake duk yarinyar da ya kwana da ita ba tare da aure ba kamar arshen rashin sirri kenan. Shiyasa ko sha'awar auren mata biyu ba ya yi, gani yake in yana raba kansa ga mata biyu kamar babu sirri a ciki. Amma daga kiran Didi ta taimaka masa ta kama ta yi masa gayya harda zuwa asibitu. Kallon Didi ya yi ganin tana kallonsa alamun ya amsawa Umma sai ya an yi aramin tsaki ya ce, "lafiya...." Kafin ta amsa ya kalli Didi ya ce, "Ya jikinta?." Didi ta ce, "har yanzu ita bata farka ba." an dafe kai ya yi jin yana sara masa Didi ta ce, "ka zauna ka daina tsayawa, zata farka itama in sha Allah." Zama yayi akan farar kujerar da take gaban gadon da Nayla ta ke, ya ri e hannunta ya kulle ido bai ce komai ba. Didi ta ce, "bara na fa awa likitan ka farka, daman sun ce in ka farka na sanar da su." Fita Didi ta yi ba jimawa ta dawo ita ka jim ka an sai ga likita namiji ya shigo ya kalli Omar ya ce, "Sannu ya jiki?." Omar ya aga kai kawai bai ce komai ba. Likitan ya ce, "Abinda ya kamata ka yi yanzu shine; ka samu ka yi wanka, ka ci abinci, ka huta zaka fi jin da in jikinka." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ita fa?." Likitan ya kalle shi ya ce, "itama muna jiran ta farka, in ta farka sai mu san abinda ya kamata mu yi." Omar ya yi shiru bai ce komai ba likitan ya matsa kusa da Nayla yana duba ruwan da saka mata dan likitan da ta kar e su tayi masa bayanin komai kafin ta tafi. Omar kallonsa yake yi ta asan ido yana jin kishi na mamaye masa zuciya, gaba aya haushin Didi yake ji, ko meye na kawo su asibiti oho, haka kawai yanzu ga wani banza kusa da matarsa har yana maganar wai zata samu sau i. Tsakin da ya yi a bayyane ya saka Didi ta kalle shi a lokacin likitan ya fita daga akin. KRB03P50 Bayan fitar likitan Didi ta bishi da kallo tana oye dariyarta ta ce, "ko zaka kira Bashir ya zo ku tafi gida ka je ka yi wanka? Ko kuma zaka fara cin abinci?, gashi na kawo." Kallon ta ya yi baice komai ba. Didi ta ce, "ko tea ne ka sha ka ga yanayinka har yanzu bai dawo normal ba, ga toothpaste na tawo maka dashi na san zaka ce baza ka ci abinci ba saboda baka wanke baki ba, gashi don Allah ka wanke ka sha koda tea ne in yaso sai na kira Bashir ya zo ya kai ka gida, zuwa anjima sai ka dawo lokacin ta farka." "Kawai sai na tafi na barta a nan a kwance?" Ya fa a muryarsa a can asa dan kana ji ka san bashi da lafiya kamar mai mura. Didi ta ce, "ai ni ina nan, kuma ba jimawa zaka yi ba" ta fa a tana auko kayan wanke bakin ta