← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 205

Sashe 30

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nake biyan ku in haya to kar na sake ganin wata ko wani sun zo, in ba haka ba baza a zauna lafiya ba ke kin sani!." Didi ta ce, "Sai masifa ka ke yi, su waye suka zo?." "Oho" ya fa a yana cillar da wu ar ya ce, "ki ja mata kunne, in ba haka ba wata ran zaki zo ki tarar na karya ta gida biyu" ya fa a yana nuna Nayla ya fita daga gidan. Nayla ta ce, "Wallahi Didi ban san baya so su shigo ba, kuma Don Allah ba i sun zo zan ce kar su shigo ne?." Didi ta ce, "su waye?." "Mama Zainab ne." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Share shi ki zo ki zauna." Suka zauna tare Didi ta ce, "shegiyar zuciya ce da Omar, baya mantuwa ga shegen ri o kamar mutanen farko. Abin nan ya wuce, sun nemi yafiya tun shekarun baya amma ya kasa daina kallon su matsayin masu laifi. Ki gode Allah ma dangin Mama ne, inda dangin Baba ne suka zo musmaman matar Kawu, Innalillahi! Ai kaf unguwar nan sai an ji amon muryarsa." Nayla ta ce, "ikon Allah." Didi ta ce, "Allah ya shirya shi kawai. Kin san me ya faru ai ko?." Nayla ta ce, "Hajja ta ta a bani labari." "To don Allah Nayla tunda komai ya wuce ba sai ya manta ba? Me ya rasa yanzu a rayuwarsa?." "Babu, Kuma musulmi da yafiya aka san shi." "To banda Omar, babu shi a ciki. Ya kasa mantawa tsaf yana zuciyarsa, nayi fa an, nayi nasihar amma a banza." "Allah ne ya taimake ni kika buga gidan nan, da Ina jin yanka min baki zai yi." Didi ta ce, "ke ce zaki saka ya yafe musu Nayla." Nayla ta wara idanu ta ce, "ni a suwa Didi?." Didi ta ce, "ke a matarsa." Nayla ta ce, "rufa min asiri, ba da ni ba wallahi." Didi tayi dariya ta ce, "Allah kuwa. Ke ce ka ai maganinsa, kuma ke nake so ki dawo dashi hanya madaidaiciya." "Hmm Didi kenan, kina magana kamar ni na haife shi." "Ba ke kika haife shi ba, amma matarsa ce ke." "Mata ta suna ba." Didi ta ce, "zata zama ta aikace Nayla, ke dai ki cigaba da ha uri kawai." Nayla ta yi murmushi ta ce, "na barki a zaune ko ruwa ban baki ba, ga rana ana yi." Didi ta ce, "Kamar wata ba uwa?. Kuma kin san da bazan zo ba ma wallahi, amma nace bara na shigo, zuwa yamma sai na je gidan su Kawu mu gaisa na yi musu barka da sallah." Nayla ta ce, "zan raka ki." Didi ta ce, "to Shikenan, Allah ya kaimu." Nayla ruwa ta kawo mata da lemo kana tsaye, "me zan dafa miki? Kin san ba girki nake yi ba." Didi bata amsar tambayar ba ta ce, "ni ya tura min ku i fa azu, na ce masa na meye wai na tura miki. Na ce masa kai baka da hannu sai kawai ya kashe wayar." Nayla tayi dariya ta ce, "wai fa advert in nan da ya gani shine ya tsare ni da ido wai ya saka ni ne, na ce masa bai saka ni ba, na yi ne kawai, shine ya ce ban san ko ke bakya yi masa shishshigi ba sai da izinin sa. Na ce masa nayi ne saboda cigaban kamfanin Yayana wai shi ba yayana bane, keda shi ka ai aka haifa bashi da anwa a duniya, dan haka bai ce min yana so ba, kar na sake wannan gangancin." Didi tayi dariya sosai ta ce, "Omar! Omar!! Allah ka shirya min wannan anin nawa." Dariya itama Nayla in tayi ta amsa da amin suka cigaba da hira cikin nisha i da walwala. KRB3P015 Arewabooks@nanahaleema11. Didi tare suka yini har akayi la sar sannan Nayla ta shirya cikin atampa da tayi mata matu ar kyau. Ta kalli Didi ta ce, mu je ko Didi. Didi ta ce, baki tambayi mai gidan ba. Nayla ta turo baki gaba ta ce, ya ce duk inda zan je babu ruwansa, ko da wasa kar na ce zan tambaye shi, shiyasa ma bana tambaya. Didi tayi dariya ta ce, amma yadda ya aga hankalinsa da azumi da baki dawo ba bai ce miki kar ki sake fita baki fa a masa ba?. Nayla ta ce, bai ce ba, cewa ya yi ma to ina ruwansa. Didi tayi dariya ta ce, Allah ya shirya Omar, tunda ya baki permit mu je. Kin yi daidai ta haka zamu fahimci yanayinsa. Nayla ta yi ar dariya bata ce komai ba. Didi ta ce, ki ce har yanzu ko abinci baya ci? Har aka gama azumi bai ci abinci a gidan nan ba ko?. wallahi Didi bai ci ba, in na yi masa magana akai ma banza yake yi min shiyasa na daina. Ana e gobe sallah dai da yana fama da ciwon kai ya sha tea, shima sha uku kawai ya yi ya ajjiye. Zan iya cewa kofin tea in shine abu na farko da ya fara amfani dashi a gidan nan. Didi ta yi dariya bata ce komai ba suka fito tare Nayla ta fito tana dubawa ko zata su Bashir. Sai kuwa taga Tk, ya bu e mata gate in ta fita da motar suka fita. Sun sha yawo da Didi har bayan sallar i sha basa nan, haka ya yi mata da i sosai ko babu komai ta rage kewa. Sai da suka yi sallar i sha a gidan an uwa sannan suka taho dan Abdulhamid yana ofar gidan Omar yana jiranta. Nayla tayi mamakin dangin su Omar, mutane masu kirki da karamci, gasu duk masu arzu i dan babu gidan da suka je wanda za a ce gidan talakwa ne, sai dai manya gidaje da madaidaita. A ofar gidan suka yi sallama da Didi da al awarin zata je gidan Didi, Didi bata shiga gidan ba ta shiga motar mijinta suka wuce. Nayla kuma a waje ta ajjiye motarta, dan ba ita take shiga da ita ba su Bashir ne. Babu wanda ta gani a cikin su hakan ya saka ta shiga ta bar motar a wajen dan ta san zasu zo su shigar mata da ita in suka zo. Babu jimawa sosai ya shigo, bai kalle ta ba key in motar ya auka ya fita ba jimawa sai ga shi ya kawo mata ta ajjiye. Yanayin fuskarsa ma baza ta bata damar yin magana ba, ko kallonta bai yi ba, a ransa kuwa haushinta yake ji tana take fita tana kaiwa dare ba tare da ya san inda take zuwa ba. Shi kuma bashi da lokacin da zai tambayeta da ya ji da izininwa take fita, sanin bazai iya tambaya ba ya saka ya share ta kawai ya shiga ciki. Haka zaman na su ya cigaba da tafiya har hutun sallah ya are ta koma aiki kamar ko yaushe tun safe sai yamma. A haka ta fara azumin sitta shawwal kamar yadda ta saba kafin wata ya yi nisa take farawa. Su Hajja suna gab da dawowa dan Salma ta sanar da ita a satin zasu dawo haka su Abiy ma. Ranar laraba da yamma ta dawo daga aiki tana zaune tana danna waya taga kiran Twiny ya shigo, abin ya bata mamaki tana tambayar kanta kenan ta dawo nigeria ko labari. Da zumu i ta auka a nan take sanar da ita ai tana ofar gidanta. Da sauri Nayla ta mi e ta je ta bu e mata tun daga nan suka rungume juna cikin farin ciki suka shiga ciki. Jidda ta kalli Nayla tace, Ma sha Allah, matar Omar kin yi kyau kuma duk da har yanzu da wannan shegiyar ramar, Amma wallahi kin fes dake. Nayla ta ce, Aiki ne fa yake saka ni ramar nan, ga aikin gidan nan yayi min yawa sosai. So nake su Hajja su dawo a kawo min maid in da zata dinga taimaka min, in yaso ko gidan Hajja sai ta dinga zuwa tana kwana. To ke aikin gidan naki ai sai yamma tunda da safe kin fita. Daman sai dai ta dinga zuwa da yamma. Jidda ta ce, Amma duk da haka kin yi kyau, na ji da i da ki ka cire damuwa ki ka kar addara. Nayla tayi murmushi ta ce, Hakan ya zama kamar dole ai Twiny. Ya ki ka baro su Mama? Kowa Lafiya?. Lafiya kowa ya ke, su ma jibi zasu dawo in sha Allah. Allah ya dawo dasu Lafiya. Amin. Mama ta ce nan zata fara zuwa ta ga ya yanayin ki yake, Tunda akace an kawo miki harin nan shikenan hankalinta ya kasa kwnaciya, ta ce ko a Abuja suka sauka sai ta siyi ticket ta zo Kano daga na ta wuce a mota Nayla ta ce, Allah sarki uwa ta gari, Allah ya dawo dasu Lafiya. Ta amsa da amin tana fito mata da tsaraba Nayla ta ce, KFC muka yi dake ko Albaik?. Jidda taja tsaki ta ce, kawai sai na rasa abinda zan kawo miki sai kaza? Kawai ki saka ni dakon kaza? To ban shiryawa haakan ba. Nidai babu abinda na siyo, naga Salma dai ta ce zata siya miki ita Yaya J. Nayla tayi dariya ta ce, Ke da baki siyo ba ai kin huta. To haka kawai na rasa me zan siyo miki sai fried chicken dan lalacewa? Ba ga KFC in nan a nigeria ba, mu je ki siya mana. Dallah can, tunda dai baki siyo ba kin kyauta. Zaki ha a KFC in nigeria da ta can ne?. Jidda tayi mata banza ta mi a mata ledar ta kar a tana fito abin ciki. Abaya ce rantsatstsiya mai shegen kyau da tsada kalar ba a, sai wani oil perfume a kwalba mai an girma, sai cross slippers, sai kuma misk tahara a babbar tasa. Nayla ta ce, Kai Twiny wannan abayar ta yi kyau sosai wallahi. Jidda ta ce, ga kuma turare nan ba, wannan turaren duk ranar da zaki amarce zaki shafa, wannan taurin kan da Tiger yake ji dashi ko lion ne shi duk sai ya sauke shi wallahi. Nayla ta yale da dariya mai sauti ta
Chapter 30 · 0% Book details