← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 205

Sashe 54

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaki yi akansa. Yanzu da ki ka sako zancen aurensa kuma ki ka mare shi kin samu mafita yaje gaisuwar?." Ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "A gaban idon Nayla ya fara dawo da maganar da ta wuce, shi ba sonta ya ke ba, ba son auren ta ya ke yi ba. Kuma ka san a yanayin da zai yi maganar, inda ace a hankali yake maganarsa fa sau i, to cikin hargagin da ya saba yake magana. Yana nuna ta da yatsa yana cewa baya sonta baya aunar zama da ita. Harda rantsuwa duk abinda ya fito daga hannunsu baya so ciki harda auren da ita kanta Naylan. Ya juya kalle ta fa, idomta ya kalla ya ce ke bana sonki, bana son zama dake, alfarmar Didi ki ke ci kuma yanzu komai zai are. Ba dole raina ya aci na mare shi ba Yalla ai?." "Subahanallah! Bai dai furta sakin ba ko?." "Ciwon arya na fara yalla ai, zama na yi na fara rawar jiki na arya ina juya kai shine ya dakatar da shi. Baiwar Allah, itace ta saka ni a mota ta kai ni har gidanmu ta bani ruwa tana tambayata abinda nake so." Ya ce, "Ai dole ki yi rawar jikin arya, da kin saka ya furta kalmar saki da ke kika jawo komai, alhakin sakin yana wuyanki. Kin fi kowa sanim halinsa bai kamata ki yi masa haka ba, yadda ki ka san halinsa kamata ya yi ki ci maganin zama dashi ba ta hanyar mari ba Aisha. Da dabara ya kamata ki yi masa magana ya je gaisuwar ba ta wannan hanyar ba. Tunda kin san shi kamar jariri yake sai da lalla awa, carbin wai ne sai kin nutsu zaki iya jansa lafiya ba tare da ya fashe a hannunki ba." Didi ta dafe kai ta ce, "ni ban san ma ya suka are da Nayla ba, kunyarta nake ji shiyasa da ta fita ko wayarta ban kira ba. Amma na san duk inda take yanzu kuka take yi. Nayla tana matu aunarsa, kai ko bata sonsa furta mata kalaman da ya yi amfani dasu a azu zai ta a zuciyar ko wacce mace balle ita, wallahi Allah kunyarta nake ji matu "Ya kamata ki kira ta kuwa." Didi ta auko waya ta kira wayar Nayla har sau biyu amma bata auka ba. Ya kalle ta ya ce, "Ki bari zuwa anjima sai ki sake kira. Shi kuma Omar ki yale shi ya sakko da kansa zai zo har gidan nan, baya iya dogon fushi da ke. Amma kema kar ki sake kuskuren marinsa, yadda ranki ya aci kika mare shi shima acin rai zai saka ya bugeki, bugewa aya zai miki ki sume wallahi" ya fa a yana dariya. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Rigamar Omar tafi shekarunsa yawa, babban tashin hankalina ranar Omar ya san a gidan wanda yake zaune. Hmmm in Omar ya san gidan da yake ciki ga daga wajan wanda ya fito ai ina jin sai an yi aramin ya i, fetur zai zazzaga min ya banka min wuta na one." AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "ku in haya ma kin ce kin biya ya dawo miki da ku inki." Didi ta ce, "Dariya ma abin ya baka? Hmmm baka san tashin hankalinsa ba ne shiyasa. Tun yana shekara sha bakwai yake walagigi dani, har yanzu ban huta ba." Ya sake yin dariya ya ce, "Yanzu dai ki kwantar da hankalinki, wannan damuwar ce bana so, ki nutsu komai zai wuce in sha Allah." Didi ta ce, "Allah yasa, Allah yasa kuma bai yiwa ar mutane komai ba. Babban tashin hankalina kar ya furta sakin nan wannan wallahi, ban san zuciyar wa Omar ya gada ba, ba haka iyayen mu suke ba wallahi, ha uri ne dasu da kuma saurin yafiya." "Bazai aikata ba in sha Allah." "Allah ya sa." "Amin. Ta so mu je ki kwanta" ya fa a yaka ri eta zuwa ciki saboda damuwar ce baya so ya ganta a ciki gaba aya. KRB3P029 Arewabooks@nanahaleema11. Nayla arfe tara na dare ta farka, tana jiyo hayaniyarsu a falo ta shiga ban aki, da yake ta san ba sallah zata yi bata damu lokaci ya wuce ba. Tana fitowa daga ban akin Mama ta shigo kamar yadda take shigowa dubata akai-akai, ta bita da kallo ta ce, "Nayla kin tashi? Taho falo cikin yayyenki ki ci abinci." Ba musu ta ri e hannun Mama suka fito falon duk suka bita da kallo. Zama Mama tayi itama ta zauna Mama ta ce, "Ummimi samo mata abinci." Nayla a sanyaye tavce, "A'a Mama bana ci." Mama ta ce, "baki da lafiya fa Nayla, yana da kyau ki ci abinci." "zan sha tea kawai." Mama ta saka a kawo mata aka kawo mata. Mama ta ri e shayin a hannunta tana jira ya yi sanyi ta bata. Babu wanda ya yi magana Mama ta fara bata da kanta tana sha har ta sha rabi kafin Nayla ta ce, "ya isa Mama" ta fa a tana sake kwantar da kanta a kafa ar Maman. Mama ta ajjiye shayin ta ce, "ciwon kan ne?." Ta girgiza kai alamun A'a. Mama ta ce, "babu abinda yake damunki yanzu?." "Jiri nake ji" ta sake fa a a hankali ba tare da ta ago ba. Mama ta ce, "Ko dai kina da ciki ne Nayla?." Duk da halin da take ciki sai da ta ago da sauri ta kalli Mama da take kallonta tana jiran amsarta, kallon mutanen falon ta yi taga yaran Maman maza guda uku sai Ummimi, ta sunkuyar da kai ta girgiza kai alamun A'a. Mama ta ce, "to me yake damunki? Ko mu je asibiti?." Nan ma ta girgiza kai alamun A'a. Mama ta ce, "to ki saki jikinki." Ta aga kai alamun to ta sake kwanciya a jikin Maman. Mama ta sake kallonta ganin hawaye ya sakko daga idonta ta ce, "Hauwa wai ne ya faru ne? Yanzu kika farfa o daga ciwon kai fa, kukan na meye haka?." Bata ce komai ba sai hawaye da take gogewa Mama ta ce, "meye ya faru?." Bata iya magana ba ta share hawayenta ta ce, "bana jin da in a zuciyata Mama, zuciyata zafi take yi min, ki rarrashe ni ta daina" ta fa a tana zaga hannayenta bayan Mama ta rungumeta tsam. Mama ta ri e ta itama tana jin bugun zuciyarta a jikinta tace, "to ki daina kuka, ki nutsu ki fa a min damuwarki Nayla." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba kuma ba ta ago daga jikin Maman ba. Mama ta rasa abinda zata ce mata sai tayi shiru kawai ta yaleta, Nayla ta sake gyara kwanciya a jikin Mama, itama ta ri eta dan ta san tana jin umin mahaifiyarta ne a jikinta shiyasa duk inda Nayla ta ganta sai ta kwanta a jikinta. A hankali ta tsayar da kukan kuma ba ta ago ba tana jikin Maman har lokacin. Mama ce ta ago da ita ta share mata hawaye ta ri e hannayenta duka biyun ta ce, "Fa a min damuwarki Nayla. Me ya same ki? Daga ija ki ke kika taho nan?." Shiru ta yi bata ce komai ba, Mama ta kalli su Abbas da dukkansu jira su ke su ji damuwarta ta kalli Nayla ta ce, "Ko su Yayyenki su ba mu waje ki fa a min?." Jin haka sai Abbas ya mi e ya ce, "Sai da safe Mama, Nayla Allah ya ara lafiya." Mama ta amsa duk sai suka suka fita Ummimi ta hau sama. Mama ta ce, "taso" ta fa a tana ri o hannun Nayla suka hau sama har akin Mama, Mama ta rufe ofa ta zauna a kusa da ita ta ce, "daga ni sai ke sai Allah, Fa a min me ya faru? Omar ya sake ki ne?." Kai ta girgiza alamun A'a Mama ta ce, "to meye?." Cikin muryar kuka ta ce, "Mama ni na bar aurensa, ki fa awa Daddy a raba auren" ta fa a hawaye yana sakkowa daga idonta. Mama ta wara ido waje cike da mamaki ta ce, "a raba auren Nayla? Omar in ne baki so yanzu?." Nayla ta ce, "ni dai a raba auren kawai." "To Nayla ana raba aure ne ba tare da a san dalilin da ya kawo hakan ba? Ko shi Daddyn su Salman in na fa a masa sai ya ce meya faru ki ke so a raba auren, in kuwa ki ka fa a min sai na fa a masa gaba aya, ai babu wanda zai miki dole, abinda ki ke so shi za a yi." Nayla ta ce, "Mama ba ya son zama da ni, gwara a raba auren a huta." Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Shikenan dalilin?." Nayla ta aga kai alamun eh, Mama ta bita da kallo tana hango damuwa sosai a tare da Naylan, sannan tana hango soyayyar Omar har gobe a idanunta. Amma tunda har ta bu e baki da kanta ta ce a raba auren tabbas duk abinda ya yi mata ya ta a mata zuciya sosai. Mama ta ce, "Ina shi Omar in ya ke?." "Ban sani ba." "Ya san kin taho nan?." Ta aga kai alamun e Mama ta ce, "shikenan. Ki kwantar da hankalinki, gobe zan je na samu Daddyn sai na yi masa bayani. Yanzu ki ta shi ki yi wanka zaki ji da in jikinki." Nayla ta aga kai ta ri e hannun Mama ta ce, "Mama a raba auren da wuri kin ji?." Mama ta ri e hannunta itama ta ce, "kar ki damu, Tashi ki yi wanka zan saka Ummimi ta kawo miki kaya sai ki saka." Nayla ta ce, "Mama na taho da kaya suna mota." Mama ta ce, "to bara na saka a auko miki" ta fa a tana fita daga akin. Ba jimawa sai ga Ummimi ta shigo da wayar Nayla da laptop da sauran kayan ta ajjiye ta fita. Nayla tana wanka tana kuka, ta dole ta iya furta a raba ta da masoyinta ba dan tana so ba, ta kai zuciya nesa ta ga kuma abinda ya kamata tayi kenan shiyasa ta aikata. Gwara ta bashi space tunda har ya
Chapter 54 · 0% Book details