← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 205

Sashe 78

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi shiru bata ce komai ba ya ce, "juyo." Nayla murya na rawa ta ce, "to ka saka kaya." Murmushi ya yi ya lumshe ido yana jin nisha i a zuciyarsa, yana tunanin tunda ya mallaki hankalinsa ko Didi bata ta a ganinsa a hakan ba, amma yau ga wata yarinya wacce ya raina ta ganshi a hakan kuma bai damu ba, har yana tunanin nan gaba ma ganin da zata yi masa zai zarce hakan. "Ki juyo." A hankali ta juyo ta ce, "kyankyaso na gani a akina, kuma na neme shi na rasa...." Ta langwa ar da kai ta ce, "in ba a kashe shi ba bazan iya bacci ba." Shiru ya yi ta ago ta ga ita yake kallo yana are mata kallo, ta sunkuyar da kai da sauri . Sai a sannan ya ce, "mu je na gani." Gaba ta yi yana binta a baya, har suka je ofar akin. Nayla ta a ja ta tsaya ya shiga yana kalle-kalle, kafin ta ga ya arasa ya kulle window ya ja net in ya rufe ya ce, "ni ban ga komai ba, ki daina barin window a bu Nayla ta ce, "wallahi yana cikin akin nan ni na ganshi." "Ni ban ganshi ba." "Na shiga uku, wallahi bazan iya bacci a ciki ba." Fitowa ya yi daga akin ya ri e hannunta har akinsa ya mayar da ofar ya rufe ya ce, "zaki iya bacci a nan?." Kallonsa ta yi suka ha a ido ya ce, "in baza ki iya ba...." Ya fa a yana nuna mata ofa. Nayla bata da yadda zata yi dole ta samu waje ta zauna gashi ko hijjab bata auko ba, kuma rigar jikinta bata sauka asa ba kuma aramin hannun ne da ita. Shima yana zaune amma shi aiki yake yi ba kallon ta yake yi ba, Nayla kallonsa take yi ta ga ya jawo littafin da take yawan ganinsa a hannunsa yana rubutu alamun ba bacci ma zai yi ba. Tashi tayi a hankali ta je ta kwanta a inda ta kwanta wancan lokacin, kafin ta ce wani abun ta ga ya kashe hasken akin sannan ya koma ya zauna yana danan wayarsa. Ba jimawa ta ga ya ajjiye wayar ya fita daga akin, jim ka an ya dawo kai tsaye kan gadon ya nufa. Sai da ya zauna ya kalle ta ya yi murmushi yana jin nisha i a zuciyarsa sosai. Kwanciya ya yi kamar yadda take a kwance ita dai tana jinsa amma ta kasa motsawa. Yana kallon ta ya san bata yi bacci ba bai ce mata komai ba ta ji saukar hannunsa a kafa unta. Idanu ta wara zata yi magana ya jawo ta gaba aya ta dawo jikinsa ya ce, "shiiii sai da safe." Nayla zuciyarta bugawa take yi, ita tunda ta ganshi babu riga ta ga yadda Allah ya era shi ta tsorata da shi, ta ru e da yanayinsa sosai irjinta sai bugawa yake yi. Abinda ya bata mamaki sai ta ga shi ya sake da ita kamar ba shi ba, dan in ba dan ya sake da ita in ba da bazai jawota jikinsa haka ba. Bugun zuciyarsa take ji a kunnenta kamar azu, ta lumshe ido a hankali bacci ya auketa. Shi kam sake zagawa da hannunsa ya yi ya ri e ta sosai yana jin sabon farin ciki da nisha i a haka ya yi bacci shima. Ko da ya farka ya kalle ta ta baje gaba aya a jikinsa tana bacci, hular kanta ya zame gashinta ya baje a irjinsa. Rigar jiki ta daga sama ta zame ana ganin saman irjin ta da yake cikin half vest. Duk da akin da duhu yana iya ganin komai, tsigar jikinsa ta tashi a kawo na farko da ya ga wannan halittta a bayyane a idanunsa. A hankali ya janyeta ya tashi ya shiga ban aki ya yi alwala ya fito. Ya lura bata sallah, a iya zaman da yayi da ita ya san tana da matu ar ibada, rashin ganin bata yi sallah a Kaduna ba da kuma da suka dawo ya tabbatar da bata yi. Bai tashe ta ba ya fita har ya je ya dawo Nayla bacci take yi. Kusa da ita ya koma ya kwanta ya sake ago kanta a hankali ya ora a kan irjinsa yana lumshe idanu. Shafa kanta yake yi a hankali a haka bacci ya auke shi. arfe bakwai na safe fitsari ya tashe ta, ta bu e ido ta kalli a inda take kwance ta ganta a kwance are- are a irjin Omar da idanunsa suke a kulle. Kallon fuskarsa take yi tana murmushi, ta kai hannu a hankali ta shafa gashin fuskarsa har zuwa gashin da ya zagaye bakinsa. an jan gashin tayi ka an a bayyane ta ce, "Damisa tana bacci kenan, in ta farka ba ka san me zata tashi ba, a haka dai kamar ba shi ba." Hannunta ta janye ta mike zaune ta ta a wayarta da take gefe ta ce, "kai lokaci ya tafi" Ta fa a tana tashi da sauri ta shiga ban aki ba jimawa ta fito, ta tsaya a tsakiyar akin ta ce, "kenan wai ya san bana sallah kenan? To in ba dan ya sani ba ya akayi bai tashe ni ba?." Ta fa a tana kallonsa idanunsa a kulle su ke alamun bacci yake yi. Komawa ta yi ta kwanta a hankali dan kar motsinta ya tashe shi, ta zubawa fuskarsa ido tana kallonsa. Omar yana da kyau sosai, kallo aya zaka yi masa ka hango tsantsar kyakykyawar halittar da Allah ya yi masa, babu abinda yake burgeta a fuskarsa kamar bakinsa da idanunsa, yana da manyan ido masu ban tsoro, idanunsa zagayayyu ne wanda suka fito waje sosai. Yana da aramin baki mai kyaun kallo ban sha'awa. Hannu ta sake kaiwa kan fuskarsa tana murmushi kawai ta ga ya bu e ido. Da sauri ta janye hannunta ta koma ta kwanta ta rufe fuska saboda kunya sosai. Murmushi ya yi akwai bai ce mata komai ba ya sake rufe idanunsa. Ya riga ta tashi daga baccin, har ya shirya ya fita bacci take yi bai tashe ta ba. Lokacin da ta farka bata ganshi ba, ta gyara kan gadon ya yi kyau, ta share akin kafin ta yi mopping sannan ta shiga ban akin. Shima wanke shi ta yi ta fito ta auko bunner ta kunna turaren wuta ta kulle akin ta fito zuwa na ta akin. Sai kuma tuna da kyankyason jiya ta dafe irji ta le a amma bata ga komai ba. Cikin rashin nutsuwa ta yi wanka ta fito ta shirya ta fito, ta auki waya ta kira mai aikinta ta ce tazo. Kitchen ta shiga tana tunanin abinda zata yi na breakfast, a hankali ta fara ha awa ta gama ta fito dashi ta ajjiye akan dining table. Ta shiga aki ya shigo falon da sallama ya shiga akinsa. Yadda ya tarar da akin ya burge shi sosai, sai hamshin yake yi mai da i, ya auki abinda zai auka ya fito itama ta fito daga aramin falon. "Ina kwana" ta furta a hankali tana kallon asa. Takowa ya yi zuwa inda take ya saka yatsu biyu ya ago fuskarta ya ce, "meyasa ki ke kallon asa?." Nayla ta rufe ido ya bi kyakykyawar fuskarta da kallo har ta bu e idon a hankali suka ha a ido. Sake sauke ido ta yi asa bata ce komai ba tana wasa da hannunta. Hannunta ya ri e guda aya ya matso da ita kusa da jikinsa sannan ya ce, "kin tashi lafiya?." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba saboda kusancin nasu ya yi yawa sosai, irjinta sai hawa da sauka yake yi. Kallon fuskarta yake yi yana yin asa da idanunsa a hankali har irjinta da yake up and down. Hannunsa ya kai bayanta a hankali ya kwantar da ita a jikinsa, ya saka hannayensa ya zaga dasu bayanta ya lumshe ido yana jin hamshin turarenta na neman illata masa sauran kuzarin da ya rage masa. Nayla ta yi ajiyar zuciya tana kasa kunne tana sauraren abinda ya fi mata da in saurare sama da komai a duniya. Shafa bayanta yake yi gently har lokacin idanunsa a kulle suke. A hankali ya sassauta ri on da ya yi mata ya cire ta daga jikinsa ya ri e fuskarta da hannayensa duka biyun ya ce, "baki amsa min ba." Nayla ta kulle da hannayenta dan wallahi kunya yake bata da kuma mamaki. Wai shima daman ya iya irin wannan soyayayr? Ita ta auka ai babu abinda ya iya, sai dai ya koya a hankali ashe shima shege ne. e ido tayi ta ce, "na ha a breakfsat" Bai ce komai ba hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "Kar ka ce baza ka ci ba, In akwai abinda ya saka baka son cin abinci a gidan nan ka fa a min sai na daina." Omar ya juya idanu ya ce, "In ma akwai na gyara matsalar ai." "me cece ita?." "Na saka an kwashe kayan abincin an kawo wasu, baki gani ba?" Ya fa a yana fitowa falo ri e da hannunta. Nayla ta ce, "na gani." "To babu wani dalili yanzu." "Da saboda an kawo abincin daga gidanmu ne baza ka ci ba?." Omar ya kalle ta ya ce, "in a yanzu aka kawo zan kar a har na ci, amma a lokacin baya da aka kawo ina ganin kamar bazan iya ciyar da ke bane shiyasa aka ha o ki da abinci. Amma a yanzu ko me za a kawo ina maraba dashi." Nayla ta girgiza kai tana mamakin wannan hali na Omar kamar basarake. Ta ce, "to tunda haka ne gashi ka ci" ta fa a tana jan kujerar dining alamun ya zauna. Kallon ta ya yi, ya kalli kujerar ya sake kallonta ya ce, "Ni ba an gayu bane, bazan iya zama a nan ba." Nayla ta ata fuska ta ce, "Don Allah...!." Ya yi shiru bai motsa daga inda yake ta ce, "YaMar?!." Lumshe ido ya yi ya bu e akan fuskarta, ya rasa meye a cikin sunan da yake yi masa da i fiye da tunaninsa. Ta shagwa e fuska
Chapter 78 · 0% Book details