Sashe 89
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana mayar da numfashi. Didi ta bita da kallon tausayi dan ta san ba aramar wahala aninta ya bata ba, ta ce, "Sannu kin ji, ki saka kaya ki yi sallah." Nayla ta nuna mata gashin kanta ta ce, "bana son gashi a ji e, damuna yake yi" ta fa a a shagwa e tana hawaye. Didi ta ce, "ko na goge miki?." Nayla ta aga kai alamun eh. Didi ta goge mata kan, ta auko mata doguwar riga da duk abinda zata yi amfani dashi ta ce, "ki saka sai ki yi sallah." Nayla ta ce, " arfe nawa?." "Biyar na yamma." Nayla ta an bu e jajayen idonta ta ce, "ban yi sallar asuba ba Didi." Didi ta ce, "ki daina kuka mana, ki saka kaya sai ki ha a duka, Allah yana gani ai." Didi ta bata dan ta shirya, Nayla kamar mara laka a haka take shiryawa kamar zata shekara tana yi saboda sanyin jiki, ta saka kaya ta an zauna tana hutawa sannan ta hau kan sallaya ta zauna tayi sallolin a zaune dan bazata iya tsayawa ba, bayan ta idar ta koma gefen gado ta zauna. A lokacin Didi ta dawo da bowl a hannunta ta zauna a kusa da ita ta ce, "Maza ki ci, na san yunwa ki ke ki." Nayla ta ce, "bakina babu da "Ki ci zaki ji da i, sai ki sha magani." Kar a Nayla tayi ta kalli abincin ta ga irish ne da liver mai ruwa ya ji albasa da carrot. A hankali take ci tana kuma shan romon dankalin har ta cinye. Didi ta fita ta kawo mata magani ta bata ta sha ta ce, "ya ki ke jin jikin na ki?." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "da sau i ka an." "To kullum likita ta ce ki dinga shiga ruwan zafi har sai kin warke. Amma ta ce ba a son shiga yanzu in an yi inki, zaki iya yin tsarki ba lallai sai kin shiga ba. Kema an bada damar ki shiga in ne saboda ciwon da ki ka ji, amma in zaki iya cigaba da kula ds kan ki ba sai kin shiga in ba." Sai kawai Nayla ta fashe da kuka ta ora kanta a kafa ar Didi. Didi ta ce, "ki daina kuka mana Nayla, kin ga baki da lafiya." Nayla ta ce, "Didi ni ki tafi dani ko na koma wajan Hajja, bazan iya zama a nan ba Didi, baya sona shiyasa yake so ya kashe ni. Dan na yi masa laifi shine zai yi min wannan hukuncin? Ni bazan iya ba Didi." Didi a tausashe ta ce, "Nayla ba rashin so ba ne, ko wacce mace irin ki tana fuskantar irin wannan yanayin a daren ta na farko. Ke ya zo miki da tsautsayi ne shiyasa aka samu matsala sosai, amma kar ki damu komai ai ya wuce." Nayla ta yi shiru kawai bata ce komai ba. Didi ta dinga rarrashinta har ta daina kuka ta koma ta jingina da bangon gadon tana tuna irin kalar azabar da ta sha a daren jiya. Sallamarsa da ta ji sai da gabanta ya yanke ya fa i, Didi ta amsa tana mi ewa ta ce, "bara na je wajan Umma na barta ita ka ai" ta fa a tana fita ta barsu su biyu. A inda Didi ta tashi ya zauna yana kallo ta amma ita ba shi take kallo ba dan irjinta bugawa kawai yake yi. Hannunta ya ri e guda aya, aya hannun kuma ya saka ya shafa fuskarta ya ce, "ya jikinki Ashiq?." Nayla a tsorace take dashi matu a, gani take ko amsar tambayarsa ta bashi za a iya sake samun matsala, ta yi shiru bata ce komai ba. "Jidda baza ki ce komai ba? Bakya son magana dani?." Ta sake yin shiru bata ce komai ba. Shima ya yi shiru yana kallon ta yana sauke ajiyar zuciya. Mamakin kansa yake yi, in akace masa zai iya rarrashi wata mace bayan Didi zai ce arya ne, sai gashi a zaune a gaban mace yana rarrashinta tana yi masa banza. A tausashe ya ce, "ki kalle ni ki ga yadda na rame saboda rashin lafiyarki, ki yi ha uri ki yafe min. Ni kaina ban kawo faruwar komai a wannan lokacin ba, ban san abinda ya faru ba, ban yi dan na cutar dake ba." Shiru ya ga tayi bata motsa ba ya sake matsawa kusa da ita ya ce, "Ashiq!." Bata ago ba ya ce, "fushi ki ke yi ko? Fa a min me zaki yi ki huce. Na san na cancanci ki yi fushi dani, na aikata abinda ban sani da ilimi akan abinda zai biyo baya bayan faruwarsa. Na kai kaina gabaga i ba tare da na san abinda faruwar hakan zai haifar ba, amma ki yi ha uri kin ji?." A hankali ta ago ido ta kalle shi suka ha a ido, ta yi saurin saukar da kanta asa cikin jin matu ar kunyarsa. Omar murya a can asa ma ogwaro yake magana ya ce, "fa a min ya jikinki? Akwai ciwo har yanzu?." Ta aga kai alamun eh ya ce, "ki yi ha uri, bazan sake cutar dake ba in sha Allah, kin yi ha urin?." Bata motsa ba ya matso kusa da ita ya yi mata peck a goshinta da kumatunta ya ce, "Ina sonki, Ina sonki, Ina sonki! Da so ki zan rayu, da sonki zan bar duniya. Allah ya halicce ni dan na so ki ke ka ai, zan cigaba da sonki har a cikin aljanna. Ki yafe min!." KRB3P052 Shiru ya ratsa akun, Nayla bata ce komai ba shima bai cigaba da magana ba sai hannunta da yake murzawa a hankali yana kallonta. Nayla ta lumshe ido tana jin kalamansa na ratsa cikin zuciyarta duk da ciwon da take ji bai hanata jin kalamansa a ranta ba. Ya sake yin shiru yana kallon ta, kafin ya ce, "ki ago ki kalle ni ko da sau aya ne, na yi kewar idanunki.." a hankali ta ago idonta, suna ha a ido ta rufe idanunta da hannunta. Ya yi murmushin farin ciki ya ce, "Dan ke ka ai Allah ya halicci Omar, ke ka ai Allah ya rubuta zaki zauna a cikin zuciyar Omar. Ina sonki Jidda, Ina sonki Ashiq" ya fa a ya yiwa hannunta peck yana shafa gashinta. Nayla duk da halin da take ciki bai hanata jin farin ciki na mamaye mata zuciya ba, ta yi murmushin da bata san ta yi ba, ya sake ago da kanta da hannunsa yana kallon fuskarta ya ce, "Murmushi yana awata fuskarki, ki cigaba da murmushi yana samun masauki mai kyau a kyakykyawar fuskarki" ya fa a yana yiwa bakinta light kiss. Murmushi ta sake yi bata kalle shi ba ya ce, "Yanzu me ki ke so?." Ta girgiza kai alamun babu komai ya ce, "A'a, ina so ki fa a min in akwai." Nayla ta girgiza kai alamun babu ya ce, "kinga banbancin dake tsakanina dake. Ni bana rasa damata, a duk lokacin da aka tambaye ni me nake so ina fa ar duk abinda yazo raina ko da na san mutum dashi da abinda zan tambaya. Bana losing opportunity, in ji turawa irin ku." Murmushi tayi mai sauti dan kalmarsa ta arshe ta bata dariya, ganin tana murmushi ya shafa kumatunta ya ce, "eh, in da ni kika tambaya kin san ne zan ce?." Ta girgiza kai alamun a'a zuciyarta ta cika taf da mamakin sababbin abi'unsa da take gani, ya ce, "zan ce ina so ki cigaba da sona har arshen rayuwarki. A farkon rayuwarki da arshenta ki cigaba da sona har mu rayu a aljanna ina zuciyarki. Kar ki yi min soyayyar mutu ka raba, in na mutu soyayyar ta mutu ya kenan? Soyayyar har abadan abada nake so ki yi min Ashiq!." Murmushi ta sake yi mai sauti tana mamakinsa, ina rashin maganar tasa ta tafi? Ina harare-hararen? Ina tsawa? Ina tsaki? Ina muryasa mai sakawa gabanta ya fa i saboda kaushinta?. Duk ta neme su ta rasa, ya fito da sabbabin halaye fil wanda bata yi zato daga gare shi ba, shiyasa zuciyarta ta cika taf da mamakinsa. Shi kam bai san tunanin da take yi ba, ganin ta yi murmushi sai ya ji da in hakan a zuciyarsa, hakan ya saka shi sake gyara zama dan son wanke laifinsa. A tausahe ya ce, "kin san meye Ashiq? Kin san me sunan yake nufi?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "Ku turawa ne kun fi gane sunayen turanci...." Ya fa a yana kallon ta muryasa a can asa ya ce, "Lokaci da mahaifiyata take da rai Didi ta ce tana kirana da Ashiq! Kalmar tana nufin masoyi ko wanda ka ke so. Ni kuma na yi miki kyautar wannan sunan Jidda. Ke ce wacce nake so, sannan duk lokacin da na kira ki dashi zan tuna da mahaifiyata haka take kirana. Ke ka ai ki ka cancanci suna, Ashiqaty!." Ganin tana ta murmushi sai ya ri e hannunta yana murmushi yana kallon fuskarta. "Na gode!" Ta furta a hankali ba tare da ta kalle shi ba. Ya ora yatsunsa akan goshinsa kamar yadda ya saba, ya an shafa ka an ya aga gira guda aya yana kallonta ya ce, "in ki ka gode min ni me zan yi mikikenan?." Bata ce komai ba ya ce, "ke kika cancanci a gode miki Jidda, Omar bai cancanci godiya ba." Kai ya an dafe jin ya an sara masa lokaci aya, ta kalle shi ta ce, "kanka yana ciwo?." Ya kalle ta yana lumshe ido ya ce, "ba sosai ba." A sanyaye ta ce, "Didi ta ce baka ci abinci ba, ka ci abinci." Ya an murmusa ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "ta ya zan iya cin abinci bayan na zama silar shigarki halin da baki ta a shiga ba Ashiq? Bana tunanin zan iya cin komai in dai ba lafiya na ga kin samu ba" ya fa a yana juyowa yana kallon ta. "Ai na ji sau i, ka je ka ci abincin." "Zan ci Jidda." "To ka je." Ya yi murmushi ya ce, "Zan ci, amma sai kin kalle ni."