← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 205

Sashe 181

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wallahi sai na shigar da ara akan asibitin nan, babu abinda ku ka sani baku san aikin ku ba!" Omar ya fa a cikin tsawa yana kallon wanda ya yi maganar. aya likitan ya kalli AbdulHamid da ya ga kamar ya an fi Omar nustuwa ya ce, "Bawan Allah duk inda zaku je abinda aka fa a muku shi zamu fa a muku, ku yi ha uri ku kar addara Allah ya yi mata cikawa. Ku daina kokwanto cikin ikon Allah, Allah yana kashewa a duk da da ya so, ni da nake maganar nan a tsaye a gabanku ba abin mamaki bane na fa i matacce a wajan nan. Ku nutsu ku kar addara, Allah ya yi mata cikawa!" Ya fa a cikin nutsuwa yana kallon AbdulHamid. Nayla ta ora Musliha a kusa da Didi ta ce, "likita kalli hannunta fa, yana cikin nawa. Ta ya zaka ce Didi ta mutu? Ruwa ta ce na bata ta sha na bata, ta ce min bacci take ji kuma ka ce ta mutu? Meye wannan ku ke zance ne wai?." A hankali likitan ya tako ya bu e hannun Didi da yake cikin na Nayla ya ora mata hannunta a irjinta. Omar ya kasa koda motsin kirki ya kalli AbdulHamid da yake kuka yana ri e da hannun Didi yana cewa, "Aisha da gaske kece a kwance babu rai? Da gaske ke ce kika bar duniya Aisha?. Aisha da gaske kin mutu kenan!?" Ya fa a cikin kuka mai nuni da tsantsar ru anin da zuciyarsa ke ciki. Omar cikin wata irin murya mai auke da rauni da sanyi ya ce, "Didi bata mutu ba, ka daina fa ar wannan kalmar!." Kallon Omar ya yi ya ce, "Omar ba a wasa da mutuwa, da gaske Aisha ta bar duniya, da gaske ta mutu!." Nayla jikinta ya fara rawa ta ce, Yaya AbdulHamid yanzu muka gama magana da ita fa, itace ta ri e min hannu. Kaga....kaga......Kaga.....ruwan da ta shanye, itace ta shanye wannan ta ce min zafi take ji" Nayla ta fa a a rikice tana aukar robar da Didi ta sha ruwa. AbdulHamid bai iya magana ba saboda kukan da ya ci arfinsa sosai kamar mace, ya du a a wajan tana kuka sosai cikin rashin mafita. Omar kam kallon Didi ya yi ya bu e fuskarta yaga idanunta a rufe ya runtse ido ya ce, "Kana neman ka wartsawa min zuciya, Didi bacci take yi ba mutuwa tayi ba. Didi bacci ki ke yi ko? Wai mijinki ya ce kin mutu ni kuma ban yarda ba, likitoci ma arya suke yi, ki yi magana su fahimci da ranki, ki tashi dan su tabbatar idanunki biyu Didi!" Ya fada cikin wani irin rauni da mutuwar jiki wanda bai ta a jin irinsa ba a duniya. Nayla kuwa wani irin bugawa zuciyar take yi, kanta ya yi bala'in sarawa, mararta ta aure tamau. Didi ta mutu shine abinda take maimaitawa a zuciyarta, ta kalli Marmerh da take zaune tana shan alawar da Omar ya bata, sai kawai Nayla ta zube a wajan a sume jini ya fara fita daga jikinta. Likitan da yake tsaye a guje ya fita aka kira nurses mata uku aka auki Nayla aka fita daga ita daga akin cikin gaggawa. Omar dai ya ji fa uwar abu amma bai san meye ba, sannan ya ji kukan Musliha amma bai san daga ina kukan yake zuwa ba, sannan ya ji an kira shi da Daddy bai san a inda ya ji maganar ba. Hannun Didi ya ri e a kasalance da rauni ya ce, "Didi da gaske ne wai? Kin mutu in?." Sai kuma ya zabura ya kalli AbdulHamid ya ce, "Zan kaita wani asibitin, ban amince da abinda aka ce a nan ba." AbdulHamid ya aro nutsuwa da jarumtar ya mi e tsaye ya goge idanunsa ya dafa Omar ya ce, "Omar mutuwa aya ce tak a duniya, tunda aka furta ta tabbata ne. Yayarka ta amsa kiran wanda ya halicceta, ka dawo nutsuwarka!." Omar ya tsayar da ido kawai yana kallon AbdulHamid jin abinda ya ce, wai Yayarsa ta amsa kiran mahaliccinta, jin maganar yake kamar saukar arabu a cikin kansa da zuciyarsa. Jikinsa rawa ya fara yi, ya yi baya kamar zai fa i AbdulHamid ya yi saurin ri e shi, Omar ya mi e tsaye sosai ya kalli Didi, ya kalli AbdulHamid, ya kalli Musliha da take kuka a kusa da gawar Didi, ya kalli Marmerh da take gefe tana kallonsa tana kiran sunansa. "AbdulHamid....!" Ya fa a cikin wata irin murya jikinsa na rawa sosai." AbdulHamid ya ce, "Ta mutu Omar, maganar da muka da ita a azu maganar arshe ce. Ta mutu!" Ya fa a hawaye na sakko masa. Wata irin ajiyar zuciya Omar ya yi, ya sake komawa kusa da Didi yana kallon fuskarta, ya ora hannunsa a goshinta ya ce, "Didi...!" Sai ya kasa arasa maganar saboda wani abu da ya taso daga zuciyarsa ya tokare ma ogwaronsa ya hana maganar fitowa. Kansa ya yi bala'in sarawa amma ya dake ya saka hannunsa a daidai ofar hancinta ko zai ji tana numfashi amma bai ji komai ba. A irjinta ya kifa kansa yana juya kai ya rasa abinda zai yi, ya kasa banbance a wacce duniyar yake, ya kasa banbance abinda yake ji a cikin zuciyarsa. Kalmar ta mutu shine abinda yake ji a kunnensa cikin murya mai amo. AbdulHamid ya dafa shi daga baya ya ce, "A azu da ta bar gidanka ta dawo gida, ta sanar dani kana ta yi mata gorin rashin kwana a inda ka gina mata. Cikin wasa da dariya ta ce in ta mutu a kaita gidan a shirya....." sai ya kasa fa a saboda kukan da ya taho masa ya fashe da kuka yana rufe fuskarsa da hannayensa. Marmerh ce ta zo inda yake tana kallonsa sai ta nuna amsa Didi ta ce, "Abba Ummi" ta fa a tana nuna Didi da fuskar ta take a bu e. Ri e Marmerh ya yi rauni na sake mamaye masa zuciya yana kuka sosai. Likitan da suka fita da Nayla ne ya shigo a nurse ya ce, "Ku yi ha uri, mun san an ta a ku, yau an saka muku rauni da ciwo a zuciyarku, ku kar i jarabawa ku amince da addara. Ku nutsu ku auke ta ku kaita gida ku yi mata gatan da ko wanne mamaci yake nema, kuka dole, amma ku jure addu'ar ku ita take da bu ata a yanzu." Sai a lokacin Omar ya ago idanunsa da suka ance sun koma jajaye, shi so yake ma ya yi kukan amma ya kasa sai wani abu da yake ji na sukar zuciyarsa, ga wani abu mai yaji da ya mamaye masa jiki har idanunsa yake jin yajin. Magana yake so ya yi amma kamar an rufe masa baki ya kasa furta komai. AbdulHamid ya mi e ya goge ido yana ri e da Marmerh ya ce, "Haka ne, mun gode sosai, Yanzu zamu tafi da ita." "Allah ya gafarta mata, ya sa aljanna ce makomarta ya bata ikon amsa tanbayar kabari." Wani hawayen ne ya sakoowa AbdulHamid ya girgiza kai yana amsawa da amin. Likitan ya ce, "akwai patient kun bari, tana kwance a sume har yanzu." Kai ya aga kawai bai iya cewa komai ba. Omar ya kalla ya ce, "Ka yi ha uri Omar, zamu je da ita zuwa gidan ka kamar yadda ta sanar da ni. Bara na kira su Kawu" ya fa a murya na rawa hannunsa na rawa yana laluben waya y auko ya fara sanar da an uwa. Shi dai Omar yana tsaye kawai har lokacin hannunsa na cikin nata ya rasa abinda ya kamata ya yi. Yana tsaye ya zuba mata ido yana kallo yana mamaki wai ta mutu, ya kasa yarda da maganar balle ya amince ta bar duniya. A haka su Kawu da Baba Adamu suka zo cikin tashin hankali da ru ani. Omar yana ji yana gani aka gama abinda za a gama aka basu gawar Didi. Kawu Mamman ne a gefensa dan ya lura baya cikin hankalinsa duk inda afarsa ta kai kawai jefa ta ya ke yi. Baba Adamu kuwa Musliha na hannunsa sai kuka take yi, da yar aka samu number Mama Sa'adatu aka sanar da ita halin da ake ciki. Kafin wani lokaci a cikin daren mutuwar ta ratsa ko wanne sashe na dangi, dangin Nayla kowa ya sani duk sun shiga ru ani saboda mutuwar ta zo babu zato babu tsammani. Mama Sa'adatu tana kuka ta wuce asibiti wajan Nayla tunda ance tana can a kwance. Gidan Omar ya cika da dangi musmanan dangin su Didi da kuma dangin AbdulHamid. Kafin gawar ta isa mutane sun cika gida tunda kowa ya tambaya sai ace a gidan za a yi jana'izarta. Aka shiga da gawarta falon gidan aka kwantar da ita.. Omar dai kallon ikon Allah kawai ya ke yi amma bakinsa ya rufe ruf ya kasa magana sai kallo da ido. Danginsa sai aikin bashi baki suke yi amma sai dai ya kalle su kawai dan ya zama kurma ya kasa cewa komai. A Daren shi da AbudlHamid ne suka yi mata wanka, yana yi yana le a fuskarta ko zai ga ta bu e ido amma ko motsa idon nata baya yi balle ta bu e. Ya ta a zuciyarta wai ko zai ji tana bugawa ya ji shiru babu abinda yake motsi a jikinta. A haka suka shirya Didi, arfin shiryata in ma AbdulHamid ne Kawu Mamman da yake ta ya su. Aka gama shirya ta ya zauna a gefen ta ya zuba mata ido kawai yana kallonta cikin farin kaya tana kwance a mi e sam al. Ko motsa ido baya yi a kanta, sai Kawu ya ta a shi sannan ya yi ajiyar zuciya. Kawu ya ce, "Ka maimaita Innalillahi wa'inna ilahir raji'un a zuciyarka." Ya bi kawu da ido kafin ya auke idon ya sake kallon Didi. A haka Omar ya kwana cir a kusa da ita, tunda ya zauna a wajan sallar asuba ce kawai ta saka shi ya motsa, shima sai da suka mi ar dashi ya tafi zai kifa suka ri e shi yana dafe kai
Chapter 181 · 0% Book details