Sashe 167
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da ka ke ganin shi ba kowa ba ne, ka wula anta shi, ka nuna masa bashi da wata daraja tunda bashi da ilimi kuma ga yanayin da yake rayuwa a lokacin. Ba ka hango abinda zai iya faruwa a rayuwarsa ta yanzu ba, baka hango zai iya zuwa ya wuce matakin da ka ke kai a rayuwa ba. Ai ilimi ba shine cigaban rayuwa, mutane nawa mu ke dasu wanda basu da ilimin amma sun fi masu ilimin capacity?. Yanzu shi ka duba shi, iyakacinsa secondary school, amma a yanzu haka akwai masu Digree da masters a ashinsa wanda yake biya salary da aljihunsa. To a nan waye ya yi nasara kenan? Masu ilimi ko kuma wanda Allah ya sakawa albarka a lamarinsa?." Dad ya yi shiru bai ce komai ba Abiy ya ce, "ita rayuwa ta duniya a duk yadda ka samu kan ka baka raina mutum, dani, da kai, da kowa ba mu san me zai faru gobe ba, dan haka baza mu yanke hukunci akan abinda zai faru a rayuwar wani ta gaba ba. Inda a lokacin ka amince ka bashi aurenta a lokacin kana da damar da zaka mayar dashi yadda ka ke so, kana da ku i, kana da iko, zaka iya saka shi ya zama daidai da ra'ayinka. Kuma inda ka yi hakan a lokacin da siyasarka ka sake gyarata, tunda ku an siyasa a ko yaushe kuna neman abinda mutune zasu gani su yaba koda ku bai mu ku ba. Yanzu koda yana son Narma bazai kar i aurenta ba, saboda zai ga da da yake a yadda yake baka bashi aurenta ba, sai yanzu da ya taka wani matsayi a rayuwarsa. Da mutuwa, da aure, da arzu i, da rabo ai ba a yiwa wani gorin rashinsu, domin kuwa lokaci kowa yake jira, in dai akwai rai bazai tsallakeka ba." Dad ya sauke numfashi ya ce, "Wannan ya wuce Captain, yanzu zamu kalla." "Na fa a maka abinda baka sani ba....a lokacin da na kar e shi a hannunka suka zo har gida suka yi min godiya da sauran abinda ya biyo baya. Ashe nima yarinyata Nayla ta shiga irin abinda Narma ta shiga a kansa, ma'ana tana yi masa tsananin son da bana tunanin Narma ta yi masa irin shi." Dad ya kalle shi da mamaki ya ce, "Nayla dai?." Abiy ya ce, "tabbas ita." "Kaga kenan asiri yake yi musu ko?." Abiy ya ce, "har yanzu kana kan batun asiri ashe? Har yanzu baka amimce Allah ne yake sakawa bawansa soyayyar wani a duk lokacin da ya so hakan ba?." Sen ya yi shiru bai ce komai ba, Abiy ya ce, "Babu asiri, ha uwar jini ce kamar yadda na fa a maka a baya. Su mata suna son namiji irinsa mai kyau a zahiri da halitta irin ta sa. Sannan yanayinsa da komai su ya burge su, baka isa ka canja musu zuciya ba, Allah ne ya saka musu babu yadda zasu yi. Su kansu kasa sarrafa kansu suke yi balle wani ya sarrafasu." Abiy ya kuma cewa, "Duk da a lokacin raina ya aci akan abinda Nayla ta yi, amma daga baya na zauna nayi nazari naga addararta ce a haka, kuma dole sai ta faru. Nayla ta zama matarsa tun a wancan lokacin, tun bashi da gidan da zai zauna da ita ta amince zata zauna dashi na kuma yarje mata ina yi mata addu'a. Yanzu batun da nake maka Nayla ta haihu dashi, gidan da bai mallaka ba yanzu ya mallaki gidan da ko kai da kanka sai ka zauna a ciki ba arka ba." Mum da mamaki da al'ajabi ta ce, "Like seriously? kana so kace yarinyar da mu ka gani tare dashi a airport arka ce?." Abiy ya girgiza kai ya ce, "itace, wannan ganin da ki ka yi musu zasu tafi Saudia su yi umra." Mum ta ce, "Kaga da zai amince ya auri Narma abin ya zo da sau i, tunda arka ce baza a sha wahala da ita wajan amincewa ta zaun a da Narma ba." Abiy ya ce, "shiyasa na kira shi da kaina na yi masa magana amma ya ce a'a. Mijinki ya sanni, bazan yi masa arya ba, bazan yi masa arya akan abinda ban yi ba. Da gaske na yi magana dashi amma ya ce shi sam bazai amince ba. Ba haihuwarsa nayi ba balle nayi masa dole, ko wanda na haifa ban yi musu dole ba balle shi." Dad da mamaki ya gama cika masa zuciya ya sake cewa, "Da gaske Nayla arka itace matar Omar Tiger?." Abiy ya aga masa kai Sen ya ce, "Da gaske kuma tun a baya ka bashi aurenta?." "Kamar yadda ka ji na fa a. Ni ban raina shi kamar yadda ka raina shi ba, na bawa ata abinda take so wanda na ke fatan zai ya kawo mata farin ciki da take burin samu a gidan aurenta. Kuma tun kafin ya zama haka take cikin walwala da farin ciki, babu abinda ta nema ta rasa a tare dashi. Yana yi mata son da baya yiwa kansa, ya kan iya sadaukar da komai na rayuwarsa a kanta, saboda kawai yana sonta sosai. Ko a lokacin da aka yi auren ko aya ban ga laifinsa ba, laifin Nayla na gani. Amma kai a lokacin da yaje wajanka laifinsa ka gani ba laifin arka ba." Dad ya an ta e baki yana girgiza kai ya ce, "Shiyasa bazai amince da Narma ba, saboda arka yake aure. Zai ga in ya auri Namra baza ka ji da i ba." Abiy ya yi murmushi ya ce, "Ko ka an ba haka bane, Narma itama ai ata ce, zan iya yi mata fighting na nemar mata da farin ciki kamar yadda zan yiwa Nayla. Da a bashi aurenta baya sonta gwara a ha ura, tunda har ya furta gwara a ha ura a yi mata addu'a. In kuwa mu ka dage akan sai anyi auren ko an yi auren bazata zamu wani farin ciki da take neman samu ba." Abiy ya gyara zama ya fusankaci sanata sosai ya ce, "Ko da nan gaba ba a raina mutum akan matsayin da yake kai, ba lallai sai ta hanyar neman aure ba, ta ko wacce hanya kar ka wula anta wanda ka ke ganin bai kai wani matakin da ka ke so ba. Kamar yadda baka san me zai faru gobe ba a rayuwarka ba, haka baka san abinda zai faru a rayuwar wani ba. Allah yana sakawa sama ta dawo asa, farin ciki ya koma ba in ciki, ba in ciki ya dawo farin ciki, ba i ya koma fari, haka zalika fari ya koma ba i. Duk an adam ba ya kaucewa rabonsa, da zarar rabonka ya kira ka babu makawa sai ya same ka. Dukkan mu ai ba rana aya muka farka muka ganmu a matakin da muke kai ba, a hankali rayuwar ta fara tafiya har muka zo yanzu. Ba a fara gini daga sama, daga asa ake farawa, a hankali sai ayi nisan zango. Komai yana da sila, komai yana da mafarki, komai yana da farko, komai yana da arshe." Dad ya yi ajiyar zuciya kawai bai ce komai ba. Abi ya ce, "ku bata shawarar yin addu'a, ta koma ga Allah tana fa a masa kukanta zata ga canji a rayuwarta sosai." Dad ya girgiza kai bai ce komai ba, amma kalaman Abiy sun shiga zuciyarsa. Abiy ya ce, "Sen da kai da matarka ku dinga yi mata addu'a, ku cigaba da nema mata sau i wajan Allah a hankali komai zai zama labari." Mum ta yi ajiyar zuciya ta ce, "haka ne, thank you." Abiy ganin haka ya mi e ya ce, "Ni zan wuce Kaduna yanzu." Har bakin mota Sen ya rako shi Abiy ya shiga aka ja motar ya tafi ya bar shi cikin tunanin neman mafita.