← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 205

Sashe 201

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kalli gadon ta kalle sa ta ce, "ban fa gane ba." "zaki gane yanzu ai, mu je ki wanke hannunki." Tare suka wanke hannu da wanke baki suka dawo. Nayla ta an harare sa ta ce, "Daman saboda na biya ka ka siyo min?." Ya aga ido sama alamun tunani ya ce, "Eh kusan haka gaskiya, dan ina so na kar i bashin kazata da kyau." "Ko babu kaza da kyau za a biya ka bashin da aka kar a a hannunka, meyasa sai da ka wahala ka fita ana sanyi? Da baka wahala ba ma zaka ga tanadin da aka yi maka. "Ina son na cike gurbin da na bari ne a rayuwarmu Jidda. "Babu wani gurbi da ka bari baka cike ba YaMar, komai ka cike sa. Ka sake bu e shafin sabuwar rayuwa a gare mu." "Da gaske Jidda!?" Ya fa a a hankali yana kallon ta. Ido ta rufe tare da bu ewa alamun eh ta ce, "komai da komai, da komai Rouhi." "Zan iya ro ar alfarma Jidda?." "Komai ka ke so ka fa a kawai "Ki zauna tare dani, ko yaushe ki kasance a tare dani, kar ki barni nayi kukan rashin ki, ki ri e ni hannu biyu, ki mayar dani dan gatan ki." "Ka auka an gama Rouhi, daman ko yaushe kai an gatan Nayla ne. Wannan alfarmar daman akwai ta, ka canja wata sai ayi maka. Ya zuba mata ido cikin soyayyarta da yake ji kullum kamar sabuwa na shiga zuciyarsa. Ganin ya zuba mata ido sai ta ce, "zan tabbatar maka da gatan da ka ke dashi Rouhi, zan baka abinda ka yi ha uri rashinsa na tsahon kwanaki" ta fa a cikin salon da ya zautar da Omar aljanunsa su fara wasa ofa. A nan suka shiga faranta junansu rai da nunawa juna soyayya mai tsayawa a zuciya. _Jiya na yi kuka sosai, na gama editing ina burin yau na yi update gaba aya na huta, ina shiga naga ya dawo farko over 10k words, haka na gama kukana editing ya dawo farko. Na so na gama uptade yau amma ba zai yu ba, sai zuwa gobe in sha Allah._ Nana Haleema P129 Nayla bata farka ba sai bayan sallar azahar, tana tashi agogon wayarta da ya juya zuwa na asar ta duba, da sauri ta diro daga kan gadon ta shiga ban aki da sauri ta watsa ruwa ta yi alwala ta fito ta tayar da sallah. Tana idarwa ta saka doguwar riga mai siririn hannu wacce take da zip arami a gaba. Yunwa take ji, hakan ya saka ta fitowa falon tana aure gashin kanta dan bata saka hula ba. A zaune ta ganshi ya bawa Marmerh wayarsa tana game, Musliha na gefen Marmerh tana taya ta kallo shi kuma ya saka Mufty a pusher yana an jijjiga pusher in ka an. Ha a ido suka yi da ita sai ta ce, "Har anyi sallar azahar ina bacci, baka tashe ni ba" ta fa a tana zama a kusa dashi. Ya bita da kallo ya ce, "Nasan kin gaji sosai, bacci ki ke son yi." Ta kalli Mufty da yake cikin pusher ta ce, "ko dan shi ai sai ka tashe ni Rouhi, bashi da abinci sai a wajena." "Da kina bacci ai na bashi ai." "Me in?." "Abincin na sa mana." Ta sake kallon sa ta ce, "Wai ina bacci aka yi haka ban sani ba?." Ya an tae baki yana aga gira tare da murmushi lokaci aya. aukar Mufty tayi da yake kallon ta ta shafa fuskarsa tana murmushi ta ce, "Tunda Daddy ya saci abinda ba nasa ba ya baka ai shikenan" ta fa a a hankali saboda su Marmerh. Murmushi ya yi ya kwantar da kansa a afadarta ya ce, "Na ha a miki tea ko coffee?." Ta ago ido sama kamar mai tunani ta ce, "Uhumm coffee." "An gama" ya fa a yana tashi ya nufi mini kitchen in da yake akin, ya ha o mata coffee ya kawo mata ta kar a tare da sipping a hankali. Ta kalle shi bayan ta ha iye ta ce, "Da ina da kai ka iya ha a coffee, ka koya da kyau." Bai ce mata komai ba ta cigaba da shan coffee, shi kma ya bu e mata abincin da yake ajjiye ya ce, "Ga abinci nan, sai ki ci. Ta ce, "Thank you my love." Bai ce komai ba sai kallonta da yake yi cikin tsananin aunarta da soyayya. Yana tuna maganar Didi da take cewa sai ya so Nayla fiye da tunaninsa, a lokacin da take fa a haushi yake ji kamar ya sha eta, amma tun tana duniya soyayyar ta bayyana wacce bai yi zato ba. Nayla gajiya tayi da kallon da yake yi mata, ta shagwa e fuska ta ce, "Rouhi ka daina kallona." "Musliha, Mummy ta cewa Daddy Rouhi" suka ji Marmerh ta fa a cikin hausar ta da take fita tar kamar ba yarinya ba. A tare suka yi dariya shi da ita, Nayla ta kalli Marmerh ta ga ita take kallo. Kafin ta yi magana Marmerh ta rigata ta ce, "Mummy kin yi kyau." Nayla ta yi dariya yana jinjinga girmar surutun Marmerh ta ce, "Zo my baby." A tare suka taso suka taho a guje, ta rungumesu tare da yi musu peck a goshi suma suka yi mata ta ce, "Kun ci abinci?." A tare suka amsa ta ce, "To ku je ku cigaba da game." "Mummy ni Mufty zan auka" Marmerh ta fa a tana kallon ta. Nayla ta ce, "A'a Marmerh, bacci yake ji yanzu, in anjima sai ki auke sa." Ta amsa da to ta koma ta zauna suka cigaba da game. Kallon ta yake yi yana murmushi mai cike da alfahari, ya kalle ta ya tuna ita matarsa ce wacce ta haifa masa yara yana ji kamar babu wanda ya kai sa farin ciki a duniya. Nayla ta sake kallon sa ganin har lokacin ita yake kallo, ta bashi light kiss a lips insa ta ce, "ka daina kallona." Bai yi magana ba kuma bai daina kallonta ta ce, "yau ma ka zama kurma ne?." "Uhum uhum! So nake ki huta dakyau." Tayi dariya ta cigaba da cin abincinta. Bata jima ba ta kammala, lokacin sallar la'asar ya yi suka sallah gaba aya har su Marmerh. Tana zaune tana cin burger su kuma suna cin shawarma. Omar ya dawo kusa da ita ya zauna, ya saka hannu a aljihu ya auko ring cover kana ya ce, "na ga hannunki." Ba musu ta basa hannunta, ya kalli hannun ya ga zoben gold in da ya bata yana nan a inda ya saka mata. Ya cire gold in ya canja masa waje, ya bu e cover ya auko ya ciro diamond ring by Titan compony ya saka mata a yatsanta. Yadda ya yi mata kyau yana kalla, ya yi murmushi tare da yiwa hannun nata kiss ya kalli idanunta kamar yadda take kallonsa. Nayla ta kalli zoben, ta aga ido ta kalle sa ta ce, "Rouhii, diamond ring!." Ya rufe ido ya bu e a kan fuskarta bai ce komai ba. Cikin wani irin yanayi na farin ciki ta ce, "Rouhi....." "Ina ji dake Jidda, kina da mahimmaci mai girma a rayuwata, li saka wannan a zuciyarki. Murmushi take yi tana kallon zoben, ta sake kallon sa cikin farin ciki ta ce, "Rouhi nima ina ji dakai, ina sonka Rouhi!. Diamond ring ne, Diomond ring compony Titan Rouhii. Siya min ka yi?." Ya murza zoben a hannunta a hankali tare da sake kissing hannunta kana ya ce, "ina da wacce zan siyawa ne in ba ke ba? Na ki ne Jidda." "Oh my god! Oh my god! Rouhi zaka yi kisan kai fa, farin cikin da ka ke bani zai min yawa" ta fa a tana ame sa cikin tsananin soyayya da farin ciki. Bayanta ya shafa a hankali, ya agota daga jikinsa yana shafa fuskarta da yatsu biyu ya ce, "in dai farin ciki yana yin yawa ina so ya yi miki yawa Jidda, in kuma baya yawa ina so daga kan ki ya fara yin yawa. Ina son na saka ki farin cikin da baki ta a shigarsa a duniya ba." "You won Rouhi, ka yi nasara akan wannan tuntuni. Ka bani farin cikin da ban same sa a ko ina ba sai a wajanka, ni ban san me zan ce ba Rouhi, ban sani ba. Na rasa wacce kalma zan yi amfani da ita wajan nuna maka farin cikina, na rasa me zance maka! Ta fa a a sanyaye tana kallon idanunsa da suke kashe mata jiki. "Ba sai kin ce komai ba Jidda, zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan na zauna dake kawai. In aka ce na za a a tsakanin ke da duk abinda na mallaka na auki aya na zauna dashi a duniya....wallahi ke zan auka Jidda. Su in na rasa su zan iya samun wasu, ke kuwa har abada na rasa kenan sai dai madadin ki." Ganin ta kwa e fuska zata yi masa kuka ya ce, "kar ki yi min kuka Jidda, ki mayar da hawaye nan bana son ganin su akan kan kyakykyawar fuskar ki" ya fa a yana goge mata ido ya ce, "Meye diamond ring na Titan? A arzu in da Alalh ya yiwa mijinki diamond ring ba komai ba ne, ke kin sani ai, tare muke yin komai dake, kin san nawa aka samu kin san nawa aka kashe, ko naira biyar ce ta shigo account ina kin san da shigowarta. Jiddana..In ana siyan duniya zan iya siya miki kawai dan ki yi farin ciki." Sake komawa jikinsa ta kwanta tana jan numfashi, ta ri e sa sosai tana cewa, "I love you so such, I love you forever and ever and ever. Thank you so much, thank you my world." Gefensa ya kalla ya ga Marmerh da Musliha suna kallon su, ya yi murmushi ya agota daga jikinsa ya ce, "Marmerh ku zo." Ba musu suka taho a guje, ya ri e hannun Marmerh da Musliha yana kallon fuskarsu da take kama da ta juna ya ce, "Ku zama shaida, Daddy yana son Mummy sosai, yana matu ar
Chapter 201 · 0% Book details