← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 205

Sashe 186

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ace nayi abinda take so da zan ga fuskar ta da farin tunda abinda take buri kenan. Amma yanzu ko na yi bazan ga hakan akan fuskarta ba, meyasa ban bari ya wuce tun tana da rai ba?. Nayla ta ce, "Ko yanzu zata yi farin ciki, kai baza ka gani ba amma na tabbatar zata yi. Yin abinda take so shine cikar aunar da ka ke yi mata, kuma zata tanadi kyakykyawan murmushin da zata yi maka a aljanna, kuna ha a ido zata yi murmushi kyakyawan ha oranta su bayyana." A irjinta ya kifa kansa ya sauke ajiyar zuciya hawaye na zuba a idanunsa. Kansa take shafawa a hankali da ya cika da gashi ta ce, "Ka cigaba da zubar da hawaye a duk lokacin da suka zo, kar ka dakatar dasu, zubarsu shine zai sassauta maka nauyin da ka ke ji." Bai ce komai ba yana kwance a jikinta itama bata ce komai ba. Ya mi e zaune ya goge idonsa ya ce, "na rasa iyayena Jidda, amma ban san haka zafi da acin mutuwa yake ba sai yanzu. Ban san haka ake ji ba sai a wannan lokacin. Ni na san bazan sake yin farin ciki ba har abada, zan zauna zaman jiran lokacin mutuwa yazo, dan rayuwa babu Didi baza ta yi min da i ba. "Na rasa mahaifiyata nima YaMar, amma ban san acin mutuwa ba sai yanzu" ta fa a tana kallonsa. Ta ce, ka daina cewa baza ka sake farin ciki ba, Allah ne yake bada farin ciki da akasinsa, rashin Didi bazai hana ka farin ciki ba, tunda ba itace take bayarwa ba Allah ne. Fa ar wannan kalmar bai dace ba, in kana fa ar hakan kamar baka kar addara ba kenan. Allah ne ya halicci Didi ya baka aronta, yanzu kuma ta koma gare shi, daman tashi ce ba taka ba. Ya girgiza kai yana suke numfashi ya ce, "Didi ta yi min komai a duniya, ta hana kanta ta bani, ta i ci ta bani, ta i sha ta bani, ta yi wahala dani, itace nemana har police station, itace kawai mai damuwa da na ci ko ban ci ba, ita ka ai ce mai shiga damuwa da damuwata, itace ka ai mai yin jinya da rashin lafiyata Jidda. Ta sadaukar da komai nata saboda da ni, kullum tunaninta wacce hanya zata bi dan ingnata min rayuwata, ko yaushe cikin tausayina take, bata so ta ga na yi fushi balle na kasance cikin acin raiii!. Ashe iyakacin rayuwar da Allah ya tanadar mata kenan, ashe raunin da take cewa tana so ta gansa a fuskata raunin mutuwarta ce, ashe lokacin da take magana akan barin komai ya wuce na ahlina mutuwar ta ce sila! Ya ja numfashi ya sauke ya ce, Allah ka ji an wannan baiwa ta ka, Allah ka kar i shahadarta, halin ta na gari ya bita." "Amin ya hayyu ya qayyu" Nayla ta fa a a sanyaye. Ya ce, "Jidda na yanke hukunci ba tare da izininki ba, na je wajan mijin Didi na ro e sa ya bani ri on Marmerh ya kuma bani. Ban nemi shawararki ba kafin na aikata, bana so Marmerh ta bar hannuna ne shiyasa. Allah yasa ban takura miki ba." Nayla ta an yi murmushi ta ce, "Didi tawa ce fa YaMar, ko bana auren ka wallahil azim ni mai ri e mata Marmerh ce, balle kuma jininta nake aure. Kar ar Marmerh da ka yi shine daidai, tunda mahaifinta ya amince ina maraba da zuwan ta. Allah ya bani ikon kula da ita, Allah ya bani ikon yi mata tarbiyyar da Didi zata yi alfahari da ita a ranar lahira." ame hannunta yana girgiza kai tare da cize baki ya ce, "Amin Jidda, na gode, na gode Jidda. Na gode da soyayyar da kike yiwa Didi da zuciyarki da gangar jikinki, Allah ya saka miki da alkhairi." Murmushi ta yi ta ce, "Amin ya rabbi. Ka daina gode min don Allah, Marmerh ata ce, Didi kuma Yayata ce. Ina aunar Didi har zuciyata, ina ganin girmanta, ina jinta kamar jinina. Bani da mai bani shawara sai ita, ko ata min rai ka yi ita nake kira ina kuka na fa awa, ta bani ha uri ta kuma bani shawarar yadda zan yi, bata ta a kallona a matsayin matar aninta ba, ko yaushe kallon anwarta take yi min. YaMar nayi babban rashi a rayuwata, ba kai ka ai ka rasa Didi ba har dani." Ya yi murmushi ya ce, daman ta ce min sai ta riga ni mutuwa, daman ta ce min tana so ta bar duniya kafin na rigata, saboda tana so ta barwa Marmerh ni a duniya. Huhhh..ashe haka Allah ya tsara, zata bar duniya ta bar Marmerh a hannuna. Nayla ta bishi da kallon tausayi, gaba aya ya canja mata kamar ba shi ba, yayi sanyi da rauni kamar an canja masa halayya, ko a kamanni ya canja gaba aya. Sanyi da raunin da Didi take fatan gani a tare dashi sai da ta bar duniya ya bayyana. Nayla ta ce, "Daman ba ta ce maka ka daina fa a akan cikin jikina ba, har ta ce maka ka yi addu'ar Allah ya ingnata cikin ba?. Har ta ce baka da tabbacin zai zauna ko?. Huhhh YaMar cikin fa ya zube, amma wallahi..." dakatar da ita ya yi ya ce, "Kar ki rantse, koda zubar dashi ki ka yi da kanki na yafe miki balle kema baki san ya fita ba. Tashin hankalin da kika shiga har cikin jikinki ya fita ya tabbatar min ba aramin matsayi Didi take dashi a wajanki ba." Ta ce, "bayan kun fita daga akin asibiti ku ka bar mu ka san me ta ce?." Ya girgiza kai a sanyaye, ta ce, "Ta ce in na haifi mace a saka sunan Hajja, in namiji a saka sunan Abiy. Sai nayi dariya ban auka wasiyya take bar min ba" ta fa a murya na rawa sosai ta kuma cewa, "na ce mata in an biyu ne fa, ta ce in duka mata ne a saka sunana dana Hajja, in kuma ne maza ne a saka sunan Abiy da sunanka" ta fa a tana kallon idanunsa. Nayla ta ce, "ina ta dariya a lokacin ban auka wasiyya ba ce, ta kalle ni ta ce kana sona sosai, nima na ce ai nima ina sonka. Ta yi dariya bayan ta yi salati ta kalle ni ta ce itama tana sonka ba ni ka ai ke sonka....." Nayla ta fa a tana kwantar da kanta a irjinsa tana kuka. Ido ya lumshe yana shafa bayanta. Nayla ta ce, "ashe ruwan da na bata ruwan arshe ne, ta ce min kamar bata sha komai ba ashe na arshe ta sha a duniya." Bayan ta yake shafawa a hankali ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Mun yi babban rashi, Allah ya gafarta mata, Allah ya lullu eta da rahamarsa. Tabbas Allah baya barin wani dan wani ya ji da i, da ace hakan na furuwa da Allah ya bar min Didi a duniya ko dan maraicina. Duk da wahalar da ta sha dani sai Allah ya kar i rayuwarta ya bar ni a duniya, sai da ta zama silar shiryuwar halayema sannan ta tafi ta bar ni. ar halak kenan!. Nayla ta amsa da amin, tana jingine a jikinsa har lokacin kafin ta ago ta kalle shi ta ga ita yake kallo. Kallon afarsa da hannunsa ta yi, sai ta mi e ta arasa wajan drawer ta auko nail cutter ta dawo ta zauna kusa dashi, gyara masa farce take yi tana yi tana hawaye. Sai da ta gama ta fita zuwa falo wajan Umma. P118 Ranar Omar da Marmerh ya kwana a kusa dashi, hannunsa yana jikin ta cikin kewar mahaifiyarta. aunar Marmerh yake ji fiye da komai a duniya, ji yake a baya ba sonta yake yi ba, sai yanzu yake yi mata asalin so. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin alhinin rashin Didi, Omar bai dawo daidai ba, yana arin kar addara ne amma wani lokacin yana gazawa. Haka zai zauna a aki yayi kuka son ransa sannan ya daure ya cigaba da harkokinsa. Ya rame, ko baccin kirki baya samu balle abinci, kullum cikin tunani da kallon hoton Didi yake. Sai da aka sake yi masa hoton irjinsa saboda nauyin da yake yi masa aka sake bashi magani. Kamar yadda burin Didi na arshe ya kasance Omar ya cika mata shi, gidan danginsu na uwa da uba babu inda bai je ba. Baba Adamu da Kawu Sulaiman godiya ya dinga yi musu akan gida da kayan akin bikin Didi. Farin ciki suka dinga yi ganin Omar a gidajensu kamar ba shi ba. Ya sake yana girmama kowa, babu aurarriyar fuska balle tsawa ko masifa. Tun daga lokacin ya zama an dangi, wannan ya kira shi wannan ya kira shi. Girmamasu yake yi kamar yadda Didi take yi, kuma ya basu matsayin iyayena zuciyarsa. an uwansa wanda basu san shi ba yanzu duk sun san shi, cousins maza da mata duk sun kar i number Omar ana gaisawa. Omar ya zama mai sanyi, duk wannan hargagin nasa da fa a babu, magana ma sai ta zama dole yake yi balle har ka ga acin ransa. Kamar yadda Didi take yawan tambayar abinda zai saka shi yayi rauni amsar ta bata bayyana ba sai bayan babu ranta, ashe rashinta shine raunin Omar. Ko yaushe Marmerh tana kusa dashi, hatta bacci a kusa dashi take yi. Yadda yake nuna aunar Marmerh arara baya nunawa Musliha, baya iya oye aunarta da kewar mahaifiyarta da yake ji a zuciyarsa. Tsohon gidansu na kusa da gidan Hajja ya saka aka rushe gaba aya, aka siyi gidajen da suke kusa da gidan aka tayar da ginin babbar islamiyya wacce za a dinga karatu da komai kyauta. angaren ha a ruwa, siyan abubuwa da za a iya yiwa mamaci gata dasu Omar ya yiwa Didi babu adadi, fatansa Allah ya kai ladan kabarinta. Duk wannan hidimar kafin Didi tayi kwana arba'in ya yi su, har lokacin bai ji a ransa ya yi mata abinda zai wadaceta a kabarinta ba. Ranar da ta kwana hamsin da biyu a kabari,
Chapter 186 · 0% Book details