Sashe 155
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iri- iri ya hanata kwana a wajan Didi. ya tasa ta a gaba har aki, ita kuma kunyar Didi take ji amma ya shafawa idanunsa toka ya ce sam bai san kunya ba. Haka ta dinga zuba masa shagwa a tana sake haukata shi, basu fito ba sai cikin dare suka yi alwala gaba ayan su suka tafi masallaci. Washe gari ma haka ne ya faru, da safe sun je ziyarar masijib uba, Uhud da sauran wajan ziyara. Da daddare Nayla ta ja Didi yawo suka tafi kasuwa. Ta dinga kai ta waje kala-kala basu dawo ba sai cikin dare sosai. KRB3P094 Nana haleema Narma tunda ta ga Omar ta tabbatar shine ta sake birkicewa, tafiyar da zasu yi ba kenan sai missing flight suka yi saboda zazza in da ya rufeta ruf dole suka dangana ga asibiti. Ruwan da aka saka mata ya sakata bacci, Mum da Dad suna tsaye a kanta suna kallonta sai da ta samu bacci sannan suka fito zuwa wajen akin. Mum ta kalli Dad ta ce, "Haka zamu cigaba da barin Narma cikin wannan yanayi?." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Lamarinta ya dame ni sosai, da gaske take son shi ba wasa take yi ba." Mum ta ce, "kuma da gaske shine C.E.O in company nan wai?." Dad ya aga kai ya ce, "Shine." "To daman arya yake yi a lokacin nan ba an daba bane?." "Ba arya yake ba, shine." "To ta ya zai samu wannan cigaban cikin sau i haka? Ba shi da ilimin komai fa, taya ya kai wannan matakin a rayuwar shi?." Dad ya ce, "Ban sani, amma abin ya bani mamaki. Wai Tiger da na sani wanda ko karatun secondary school bai gama ba shine ya kai wannan matakin, shine da wannan matsayin da ni da nake da matakin phd ban kai matsayin ba. He speak an English also, ta ya ya samu wannan cigaban within two years?." Mum ta ce, "to daman arya yake maka ya kai matakin da ya kai tun a baya, shiyasa yake dabancin mai tsari. Ni tsoro ma nake yi anya ba Dss ba ne?." Dad ya kalli Mum ya ce, "ki yarda shine Tiger, a baya bashi da wani ilimi ko wani mataki na rayuwa. Ki dawo hankalinki mana." "Dole na fita a hankalina, kana magana akan wanda China tayi signing contract da shi fa, kuma yanzu ana zancen shine Tiger wanda ya yiwa Narma asiri, ai dole na ru e." Dad ya kalle ta ya ce, "Wallahi shine, shine wancan shine wannan." Mum ta ce, "yanzu meye abin yi?." "Daman can bashi da tsoro kuma baya tsoron magana, ya kalle ni ya ce shine zai bani appointment ba ni ne zan bashi ba." "To ai ya kamata a san abinda za a yi kafin Narma ta rasa ranta." Dad ya kalle ta a nutse ya ce, "Kin amince ya aure ta kenan?." Mum ta ce, "indai zai aure ta in na amince mana." "Rayuwarsa ta baya fa? Kar ki manta komai yana nan a rubuce." "Waye zai tuna wani previous abu? ai present ake kallo yanzu a manta da wanda ya wuce. Ka same shi ku yi magana, na san bazai i mace kamar Narma ba." Dad ya yi murmushi ya ce, "baki kula da matarsa ba ne shiyasa, bana tunanin akwai abinda Narma zata nuna mata." Mum da mamaki ta ce, "har aure ma ya yi kenan?." Dad ya aga mata kai bai yi magana ba Mum ta dafe kai ta ce, "koma dai meye Narma itace first love in shi, na tabbatar zai sonta, zai so ya rayu da ita matsayin second wife in shi." "Oh kin amince ta je a second wife?." "I have no choice my dear." Ajiyar zuciya Dad ya yi yana tunanin wannan abu mai aure kai, Anya Omar zai amince bayan abinda ya faru?. Mutanen Madina ibada kawai suke yi hankali kwance, su je masallaci su yi ibada sannan su je yawo bisa jagorancin Nayla ko gajiya bata yi indai a fagen yawo ne. Didi addu'arta bata wuce Allah ya ji an iyayensu, ya sake aukaka Omar, ya sa Omar ya manta da abinda ya faru ya rungumi danginsa. Didi ta fahimci kamar tana takurawa Omar baya sakewa da matarsa in tana nan, sai ta tsiri zaman masallaci, in suka idar da sallar asuba zata cewa Nayla cikin masallaci zata shiga bazata koma ba, ko ta ce AbdulHamid ne zai zo ta kuma hana Nayla tafiya da Marmerh. Nayla haka zata koma ita ka ai, daman ta fi samu sa a hotel a zaune dan shi bai ma cika zuwa yawon da take kai Didi ba. Da sallama ta shiga ta arasa cikin akin ta same shi a zaune yana magana da Bashir a waya ta cire hijjabi ta shiga ban aki. Bata jima ba ta fito ta samu har lokacin waya yake yi, ta bu e kayanta ta auki aramar riga ta cire ta jikinta ta saka. Tana juyowa suka ha a ido ya gama wayar ta ce, "kwana biyu ban san me Didi take yi a masallaci ba, sai ta je na dawo ita ba yanzu zata dawo ba ciki zata shiga, kuma ta hanani tahowa da Marmerh." Murmushi ya yi ya taso zuwa inda take tana kallon madubi ya tsaya a bayanta ya ora kansa a kafa arta yana shafa cikinta a hankali ya ce, "ta fahimci bana sakewa da ke in tana wajan, kema bakya sakewa in tana nan shiyasa take bamu waje." Duk da tana kallonsa ta madubi amma sai da ta juyo ta ce, "Da gaske?." aga mata gira ya ce, "Da gaske." "Kai YaMar! wai kana nufin ta fahimci uncin da ka ke yi?." Ya yi murmushi ya ce, "eh mana. Itama ai mijinta na zuwa wajanta in muka fita." Ta madubin ta kalle shi ta ce, "Kai YaMar." arya na yi?." "A'a ban ce ba, amma ka dinga jin tsoron Allah." Dariya suka yi shi da ita, ya zagayo da hannayensa cikin ta yana ka llon fuskarta itama tana kallo ya ce, "inda ace hotel in da mijinta yake shi ka ai ne a akin da yake da sai ya auke Didi su je can su arata, to ba shi ka ai bane suna da yawa. Kuma in ki ka bincika Allah bata masallacin yanzu." Nayla ta ce, "To tana ina?." "Wajan mijinta mana, ba kece mai jin kunyarta ki i sakewa da mijinki ba...? Ni dan ta ni ba kunyarta nake ji kece dai ki ke kwafsawa." Fuskarsa ta ri e ta ce, "ni kam ina jin kunyarta sosai." Ya ta e baki ya ce, "Kin manta Didi ce fa? Itace wacce ta farfa o dake daga dogowar suman da ki ka a daren farkon ki da mijinki." Kallon sa ta yi ta madubi ya kashe mata ido sai ta rufe ido tana dariya. "Kunyar ta zo kenan?" ya fa a yana kallon ta da murmushi. Nayla ta ce, "Kaine ka bani kunya, wai doguwar suma." "Eh mana, ba doguwar suman ki ka yi ba?." "hmmm a dai yi shiru kawai" ta fa a tana murmushi. Ya ce, "ki ka saka hankalina ya tashi na dinga tunanin na kashe ar mutane." Nayla da shagwa a ta ce, "Rouhi.... na ce a dai yi shiru." Yayi dariya ya ce, "an yi." "Allah ya shiryaka." "Ya shirya mu dai Jidda, in na shiryu baki shiru ba ai shiryuwa." Ta ce, "Ka san me? Wai Twiny ce ta ce zata so ta ga abinda zan haifa wai wanne irin kyau zai yi." "Nima dai ina wannan tunanin shiyasa na agu naga kin haihu, duk da dai na fiki kyau amma zan taimaka ta an yi kyaun ki ka an, amma dai na fiki." Nayla ta san tsokanarta yake yi sai ta ce, "to daman ni na isa na ce na fika...? kalle ka fa." Ya an murmusa ya ce, "yau kin yarda kenan?." "Na fahimci musun ka ke so shiyasa na yi maganar." Ya yi ar dariya kafin ya ce komai ta ce, "ni bacci zan yi." "Nima haka." Tare suka kwanta suka yi bacci kafin sallar azahar. Haka suka cigaba da rayuwa a Madina bayan kwana goma suka tafi makka suka yi umrah suka cigaba da ibada kamar ko yaushe. Satin su uku da tafiya suka dawo zuwa Nigeria cikin kewar saudia. Mijin Didi ya riga su dawowa da kwana biyu, hakan ya saka shima ya zo aukar matarsa a airport suka tafi shi kuma suka tafi da Bashir zuwa gida. Bayan sun huta da kwana biyu kamar ba tare suka je da Marmerh ba saboda tsarabar da ya yi mata kuma a ranar ne ya kaiwa Didi motar da ya siya mata. Nayla ce ta shiga motar Didin ta ua, shi kuma ya shiga motarsa suka tafi can. Har lokacin Didi rabon tsaraba take yi, an mijinta sun sha kaya kamar babarsu ce ta je hakan ya farantawa AbdulHamid rai sosai. Sun yi mamakin ganin Nayla da Omar, duk da sun saba zuwan dare amma bata auka zasu fito ba tunda basu jima da dawowa ba. Nayla ta kalli Didi tun kafin su zauna ta ce, "Didi zo mu je ki ga wani abu." Didi ta ce, "meye?." Nayla ta ce, "Zo mu je dai." Tare suka fito har wajan motar Didi bata gane komai ba, Nayla ta ce, "Wannan motar." Didi ta ce, "Omar ne ya kuma siya ko ke ya siyawa?." Nayla ta yi dariya ta ce, "A'a, ke ya siyawa" ta fa a tana bata key in motar. Didi ta kalle ta ta ce, "Nayla kar ku sake ru a min tunani na kuma suma." Nayla ta ce, "Wallahi da gaske nake Didi, motarki ce, ke ya siyawa." AbdulHamid ne ya araso wajan yana fa in, "Kai kai kai! Ma sha Allah, amma mun gode. Wannan tsadaddiyar mota haka? Lallai Aisha kin zama ar gata." Didi ta kalli Omar da yake ta wasa da Marmerh yana are mata chocolate in da ya yi dakon ta saboda ita, kamar bai san me yake faruwa ba. Didi ta ce, "Omar!." Ya kalle ta ya ce, "Didi." Zata fara kuka ya ce, "Allah in ki ka yi kuka bazan shiga gidan ba tafiyata zan yi,