Sashe 156
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ke komai aka yi miki sai kin yi kuka? Na san ai kin ji da i kuma kin gode, daman na yi dan ki ji da in ne to meye na kukan?. Bana son kukan nan tun ba yau ba kin sani, amma sai ki dinga yi kuma in nayi magana ki ce na farin ciki ne, Bana son na farin ciki shima!" Ya fa a a fusace cikin masifa dan in ya yaleta kukan zata yi. Jin abinda ya ce sai ta yi shiru tana share hawaye ta ce, "To mu koma gidan." Tare suka koma bayan ya auko kayan Marmerh ya ajjiye mata ya ce, "ga tsabar Marmerh." Didi ta yi tagumi ta rasa me zata ce masa sai AbdulHamid ne yake ta godiya yana addu'a kamar shi aka bawa kyautar, Didi kam ta zama kurma sai bin sa take yi da idanu. Ta bu e baki zata yi magana ya ce, "kar ki ce min kin gode Didi, ki yi addu'a a zuciyarki kawai bana son godiyar. In kuma ki ka yi wallahi zamu yi fa a, zan daina kula ki gaba aya sai ranar da na ga dama." Didi ta yi dariya ganin ya koma mata Omar inta na baya, ta share hawayenta ta ce, "ko lokacin da ka ke jan wuya ai baka iya fushi da ni balle yanzu." Ya bu e idonu ya ce, "Har yanzu Jan wuyan ne ai, in kina musu ki gwada ki gani." Dariya ta yi sosai tana kallonsa. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Omar ka cika min burina na duniya, duk abinda nake buri a duniya ka yi min Omar, abu aya ya rage min a yanzu....." Ya kalle ta a nutse bayan ya sassauta murya ya ce, "Didi fa i abinda ki ke so, ki fa a don Allah, ko meye zan cika miki shi in sha Allah." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ala arka nake so ka gyara da an uwan mu Omar, wallahi shine ka ai abinda yake damuna a zuciyata. Fargaba nake yi kar na bar duniya ba tare da ka daidaita da ahlinmu ba, na san in na mutu babu wanda zai saka ka ka yi kamar yadda ka ke yin abinda na ce" ta ri e hannunsa ta ce, "Don girman Allah ka bar wannan tunanin ya wuce Omar, ka yafe musu ka kar esu matsayin iyayenka. Baka da wasu a duniya sai su in, su ne ahlin ka, sune danginka gaba da baya. Yayyen mahaifiyarmu da annenta inda kana mu'amala dasu zaka dinga ji kamar da mahaifiyar ka ke rayuwa. Maganarsu, kamanninsu duk iri aya ne tunda jininta ne. Ina jin sau in kewar mahaifiyarmu a duk lokacin da nake tare dasu, suna bani farin cikin da muka rasa a wancan lokacin." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba yana kallonta ta kuma cewa, "Allah ya azurta ka cikin aramin lokaci, ya baka aukakar da mutane dubu basu samu ba. Kana da mota ta kanka, kana gina gidan kanka, kana da ma'aikata sama da hamsin a ashinka, kana da mace ta gari harda arzu an da yake cikinta, to Omar me ka ke nema kuma a rayuwar nan?. Omar in ma da gaske so ake aga ka wula anta yanzu a wanne mataki rayuwarka take? In so ake aga rayuwarka ta lalace a wanne mataki rayuwarka take Omar?. Balle mutanen nan duk sun yi nadama tun ba yau ba, suna so su jaka a jikisu su nuna maka soyayyar da ka rasa amma ka i bada dama. Kar ka zama mai butulci ga ni'imar da Allah ya yi maka Omar, ka zama mai rama sharri da alkhairi. Don Allah ka bar maganar nan ta wuce, ka je gidan ko wannen su ka gaishe shi, duk abinda ya taso ka dinga saka su a cikin lamarinka" Didi tayi shiru tana kallonsa gabanta yana fa uwa. KRBP095 Nana haleema. Shiru ya yi bai ce komai ba, ya zuba mata ido kafin ya janye idanunsa daga kallonta ya cire hannunsa daga ri on da ta yi masa. Ya ha e fuska ya ce, "Zan yi tunani." Didi ta yi murmushi ta ce, "to Omar ka yi tunanin da kyau, da ni da kai bamu da tabbacin zamu kai gobe da rai, kafin mu bar duniya ka gyara zumunci nan don Allah, kar ka zama mai yanke zumunci." "Na ce ai zan yi tunani, ki bar maganar mana" ya fa a ba tare da ya kalle ta ba. Murmushi ta yi an ko babu komai an samu cigaba a lamarinsa, tunda gashi bai tashi ya fita ba kuma bai fara yi mata masifa ba. Ta ce, "an gama gini ko Omar?." Ya aga kai ya ce, "Eh, kaya ake zubawa." "Allah yasa a shiga a sa'a." "Amin." Ta kalli Nayla ta ce, "zuwa yaushe zaku tare?." Nayla ta ce, "zai yi tafiya zuwa Italy next week sai ya dawo." "Allah ya kaimu, ni na auka ma sai kin haihu, ashe a sabon gida zaki haihu. Kai komai inda ku i ba a aukar lokaci, gaba aya ginin gidan nan wata nawa aka auka har an gama." Nayla ta ce, "Wallahi nima naga gudun abun sosai Didi." Omar ya kalli Didi ya ce, "yaushe zaki je ki gani?.." "Ai na je Omar." "Ki koma." Ta ce, "to zan koma in sha Allah." Omar ya kalli Nayla ya ce, "mu tafi." Tare suka fito gaba aya motar tana nan inda aka ajjiye suka shiga ta sa motar suka tafi aka bar ya Didin a wajan. Radio ce take ta aiki a motar ana wa'azi gaba aya abinda ake fa a kamar da Omar ake, ta ga ya nutsu sosai yana ji duk da tu i ya ke yi kuma ba gida zasu tafi ba sabon gida zasu je daga nan zasu wuce gida. Nayla ta ce, "Rouhi inda ace zaka gyara ala ar nan kamar yadda Didi ta ce da yanzu ka wuce a matsayin da ka ke kai a yanzu, zumunci babban angare ne a duniya." Shiru bai amsa mata ba ya cigaba da tafiya. Omar ya tafi Italy ita kuma ta tafi Kaduna, sati biyu yayi ya dawo itama a can ta gama kwanakin sai da zai dawo ta dawo gidan. Abubuwa suna ta gaba cigaba na sake wadata da arzu i suna ta ara yawa ga Omar. A cikin wannan kwanakin suka tafi Maldives kamar yadda ya yi alqawari, tafiya ta yi musu da i amma ba can ba, saboda cikin Nayla ya girma sun je ne dan ya cika mata alqawari amma ya yi al awarin zasu dawo in ta haihu. Dawowarsu aka fara shirye shiryen komawa sabon gida, an gama komai an kuma zuba komai babu abinda aka auka a gidan da suke ciki, duk da kayan babu abinda suka yi amma ya ce shi baya da bu ata, komai sabo yake so ya zuba. Nayla da sabuwar mai aikin da aka bata zasu tafi sabon gidan suna ta ha a kayanta da za a kai can. jin motsinsa sai ta fito zuwa akinsa. Tana shiga ta ce, "Rouhi yanzu duk wannan kayan a nan za a bar su? Yanzu ina zan kai?." Ya kalle ta ya ce, "na ki ne ai ko? Ki siyar ko ki bayar duk za inki ne, ananun abubuwa su na amince ki auka, kamar frames da kayan kitchen." Nayla ta ce, "meyasa to?." Ya kalle ta ya ce, "ni tun farko ra'ayina kenan, in zan yi aure babu abinda matata za a kawo daga gidansu komai ni zan yi. Kuma yanzu Allah ya bani iko, sai ki bayar da na ki." Murmushi ta yi ta ce, "Rouhii komai na ka daban yake da na mutane, komai naka tsarinsa daban." Kallon ta ya yi ya auke kai bai ce komai ba ta ce, "yau jan ajin ake ji dashi kenan ko? Shikenan na gode." Murmushi ya yi ya ri o hannunta ya yi mata kiss a goshi, ya yiwa tulelen cikinta kiss ya ce, "ni na isa na ja miki aji? Kawai maganar ce bana so." Nayla ta ce, "Amma ku in hayar gidan nan ai basu are ba." Ya an ja tsaki ya ce, "Na bar masa" ya fa a yana zama akan kujera tana kallonsa, tana ganin ya kamata ace Didi ta fa a masa gidan waye. Ranar friday suka tare a sabon gida, gida ne ba ni da gida ba, gida ne babban gida sosai. Ko iya car park in gidan babba ne balle kuma cikin gidan. Sama da asa ne, falo biyu a asa biyu a sama. aki aya ne kawai a asa sauran da unan duk suna sama. Falon farko na saman shine na Nayla da akuna guda uku, sai falo na biyu shine na shi da aki guda biyu. aki aya na kusa da akin Nayla akin Marmerh ne, wanda aka zuba mata komai na yara, gado da stickers, da toys komai na yara aka zuba a cikin akin kamar shi ya haifeta. Daga compound in gidan akwai akin masu aiki da ban aki harda aramin kitchen dan duk Nayla ce ta ce ayi haka. Ana cikin ginin gidan ya siyi wani fili a kusa da gidan aka sake shigo dashi, gidan sai ya ara yin girma sosai ya saka aka tashi sabon apartment wai angaren Didi ne. Su Didi duk suna gidan, in aka ce ga apartment inta sai ta dinga dariya tana sake jinjina qaunar da Omar yake nata ita da Marmerh. Bai yiwa abinda Nayla zata haifa aki ba amma ya yiwa Marmerh. Su Salma da Jidda da kowa na ahlin Nayla sun zo gidan ranar da ta tare ana yabo da addu'ar Allah ya sanya albarka. Bayan kowa ya watse Omar ya zo shida su Bashir aka kawo motarta wacce ya canja mata ya siya mata babbar waccan aka ajjiye da ta sa motar. Su ma har gidan sun shigo suna ta farin ciki dan Boss in ya ci gaba su ne suka cigaba. Didi da Nayla kawai ya samu a falon, ya zauna ba tare da ya kalle su ba ya ce, "Didi baki tafi ba? Ko a nan zaki kwana?." Ta yi dariya ta ce, "ba kwana zan yi ba, amma dai