Sashe 190
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aga gira tana kallonsa ya langwa ar da kai ya ce, "Yau na zama an gatan Jidda." Ta shagwa e fuska tana kallonsa ta ce, "Daman kai an gatan ta ne." Zuba mata ido ya yi yana kallo cikin aramin hasken akin, ya ri e hannunta yana murzawa a hankali kafin labari ya sake canja salo. Suna fitowa daga wanka aka yi kiran farko na asuba, Nayla bacci take ji sosai, idanunta har lumshewa yake yi, ta kalle shi ganin ya shimfi a sallaya ta ce, "Bazan iya sallah ba, bacci nake ji sosai Rouhi." Ya bata light kiss a goshi ya ce, "ki huta kafin ayi kiran asuba, zan ro a miki duk abinda ki ke so. Me zan ro a miki?." "Rayuwa dani ka ai, babu wata macen." Ya yi murmushi ya ce, "an gama, ki huta kafin ayi sallah." Kwanciya tayi ya gyara mata gashin kanta ya sake yi mata kiss a kumatu yana ji kamar ya mayar da ita cikinsa saboda so. Shi kansa a gajiye yake kuma baccin yake ji, amma yana da bu ata da yawa a wajan Allah dole ya daure ya tayar da sallah. Ana kiran sallar asuba ya tashe ta ya ce, "Jidda! Jiddana!." Ta bu e ido a hankali ta kalle shi ta ce, "Rouhii bacci!." "Na sani, tashi ki yi alwala mu yi sallah sai mu kwanta, tashi kin ji?." in tashi ta yi tana shagwa a, ganin zata ata masa lokaci ya auketa ya shigar da ita ban akin ya ajjiye ta a gefen bathtub ya ce, "Ki yi alwala Jidda, za a tayar da sallah." Kai ta aga ya fito yana jiranta, ba jimawa ta fito ta saka doguwar riga ta saka hijjabi aka tayar da sallah suka bi masallaci suka tayar su ma. Ana idarwa ta kalle shi da idanunta a lumshe ta ce, "Good Morning Rouhi." Ya matso kusa da ita ya ce, "Good morning zam zam." Bacci ne a kanta bazata iya bashi amsar sunan da ya kira ta dashi ba, ta zare hijjabinta kalli su Marmerh ta ce, "Ka dawo dasu nan." Ya kwanta a kan gadon ya ce, "bar su a can" ya fa a yana janta jikinsa bacci mai da i ya kwashesu. Kukan Marmerh da Musliha ne ya tashe su gaba aya, Nayla ta mi e zaune kanta ya yi nauyi sosai saboda bacci, ta kalle shi ta ga ya arasa ya kwaso su dukansu ya bata Musliha ta fara bata laban. Laban in shima ya bawa Marmerh dan ya san yunwa take ji ta sha ta fara wasa. Musliha ma tana oshi ta fara kalle-kalle tana kallon babanta tana dariya alamun babu batun bacci. Nayla ta kalle shi kamar zata yi kuka ta ce, "Bacci Rouhiiii." Ya matso kusa da ita ya ce, "Kwanta ki huta, zan fita dasu har sai kin tashi." "Amma kaima baccin ka ke ji." "Zan yi anjima, amma ki huta yanzu." Ta kwanta ya rufeta ya shiga ban aki, bai jima ba ya fito ya auki baby pusher insu ya saka su suka fita daga akin. Nayla sai azahar ta farka har lokacin basu dawo ba, ta yi wanka ta shirya a lokacin ta ji ana kiran sallah. A aki ta yi sallar dan ta san in ta fita babu lallai ta samu elevetor tunda lokacin sallah ne a cike yake zuwa. Jim ka an da idar da sallah suka dawo, ta kalle shi kamar yadda yake kallonta, barinsu ya yi a cikin pusher in ya araso inda take, ta ora hananyenta a kafa arsa ta ce, "Sannu da zuwa." Goshinsu ya ha e waje aya idanunsa a lumshe, a hankali ya fara kissing inta cikin salo na soyayya, bai jima baya dakata ya kalli idanunta ta ya ce, "kin gama baccin?." Ta aga masa gira kafin ta ce, "amma fa da saura, sallah ce ta tashe ni." "Ki sake komawa, zan sake fita da yaranki har sai kin tashi." "Kaima fa na san baccin ka ke ji ko?." "In kika yi kamar na yi ne, ki yi mana bacci." Ta yatsine fuska ta ce, "Yunwa nake ji." Ya raba kansa da ita ya auki leda a bayan pusher ya ce, "Na taho miki da abinci zuma, gashi ki ci." "Kai fa?." "Mun ci na mu, ni dasu mun oshi. Murmushi ta yi ta kar a ta bu e ta ci abincin, bayan ta gama ta ajjiye ragowar ta dawo kusa dashi da yake tare dasu Marmerh sai turmurmusa masa jiki suke yi da tsalle-tsalle. Nayla ta araso ta bawa Marmerh wayarta dan tayi game, ta auke Musliha daga jikinsa ta ce, "Sai tsalle-tsalle ku ke yi masa a jiki, ba ku san ya gaji bane? Ba ku san...." Sai ta daina kallon Musliha ta kalle shi kamar yadda yake kallonta ta ce, "Ba ku san ya arar da arfinsa akan Mummynku ba..? Ku bar shi ya huta, ya gaji sosai." A yadda ta arashe maganar ya saka shi bata light kiss a bakinta ya ce, "Zumata." "Da asuba ka ce zam zam, yanzu ka ce zuma. Wanne yafi dacewa dani?." "Kuma sunayenki ne, zaki amsa sunan zuma, zaki amsa sunan zam zam. Zam zam ya fi komai da i da magani, kema kuma magani ce a gare ni mai matu at tasiri. Zuma kuma za inta mai da i ne da kuma magani, musamman pure zuma wacce ba a yi mata mix da komai ba, asalin yadda Allah ya yi za inta kamar irin ta asar nan. Haka za inki yake daga Allah Jidda, mai saka Omar zaucewa da fita daga cikin hankalinsa..." ya marairaice fuska yana sake yin asa da murya ya ce, "Zumata, Don Allah ko bayan na mutu kar ki yi wani auren kin ji? Bazan ta a farin ciki a cikin kabarina ba, zan kasance cikin halin unci da kishi." Bakinsa ta yiwa kiss ta ce, "Tare zamu mutu in sha Allah." Ya yi ajiyar zuciya yana murmushi ya ce, "Da na rasa Didi na auka na gama samun farin ciki a duniya, na yanke rai da cigaba da rayuwa, na ji dama nima na mutu na huta. Duniyar tayi min zafi, komai ba yayi min da i, komai ya tsaya cak, ina jin kamar an canja ni. Ina ji kamar gatana ta tafi, ina ji kamar farin cikina ta bar duniya, ina ji kamar rayuwata ta lalace tunda babu ita...." Ya ri e fuskarta da hannu biyu, yana shafa kumatunta da yatsa aya ya ce, "Amma a jiya kin saka min aunar cigaba da rayuwa, kin saka min aunar cigaba da kasancewa da ke, kin saka min aunar cigaba da rayuwa har nan da shekara ari. Ina so na rayu da ke Jidda, ina so na cigaba da kasancewa dake kodan na cigaba zuwa inda naje a jiya, ina so na rayu dake ki cigaba da nuna min soyayya da auna kamar dai jiya!...." Nayla tayi murmushi jin abinda ya ce, ta bishi da kallo kafin ya ce, "Allah ya nuna min ikonsa, ya nuna min ko babu Didi zan cigaba da samun farin ciki a rayuwata, rashinta bazai hana ni cimma farin cikin da yake jirana. Shiyasa Allah ya shigo min dake rayuwata, ashe kece zaki maye gurbin dangina gaba aya. Huh Allah gwanin hikima da iya tsara komai ga bawansa, baya barin wani dan wani yaji da i, domin kuwa koda ya bari in shi yake bayar da jin da i ya kuma bayar da akasinsa. Kasantuwar wanda ka ke so a tare da kai ba shine dawwamar farin ciki ba, a ko yaushe cikin jiran ikonsa ka ke." Nayla ta ce, "Wanda ya rasa uwa da uba a lokaci aya ma yana cigaba da farin ciki a rayuwar, indai ya mi a lamarinsa ga Allah zai yaye masa dukkan damuwa ya kuma bashi farin cikin da bai samu a lokacin da suke da rai ba. Kamar yadda kace, zaman wani a duniya baya zama silar dawwamar farin cikin wani." Ya girgiza kai cike da gamsuwa ya ce, "Haka ne Jidda. Allah ya cigaba da bamu ikon kar addara, Allah ya bamu ikon mi a masa lamarin mu gaba aya. Amma gaskiya ina kewar Didi sosai, ban ta a jin kewar wata halitta kamar yadda nake kewarta ba, in na tuna bata duniya bana sani lokacin da hawaye yake zubowa daga idanuna. A kullum dana farka daga bacci itace take fara zuwa zuciyata, dana rufe idona fuskar Didi zan fara gani. Amma wanda ya fini sonta ya kar e ta, daman aro ya bani ita, kuma yanzu ta koma gare shi. Ina ji a jikina tana cikin rahamar Allah." Nayla tayi murmushi ta ce, "in sha Allah." Omar ya zuba mata ido yana kallo bai ce komai ba, da suka ha a ido sai ya aga mata gira yana lumshe idanunsa. Murmushi bata ce komai ba shima bai ce sai kallonta da yake yi. "Our yesterday night is memorable!" Ta fa a a hankali tana shafa gashin fuskarsa. Lumshe ido ya yi yana kallonta ya ce, "ni na rasa ma ne zance miki akan daren jiya." Fuskarta ta ha e da tashi ta ce, "Ka bar sa a ranka kawai." Kallon bakinta yake yi kafin ya fara kissing inta. Sun manta da yara a ajjiye, sai da Marmerh ta fara kiran sunanta sannan ta zame kanta ta kalle su ta kalle sa ta ce, "Honeymoon mu ke yi ne ko childmoon?." Dariya ya yi ya ja kumatunta ya ce, "Lokacin su ne, tafiya ta gaba dole mu dire su a gida, bazai yu irin haka ta dinga faruwa ba. Murmushi ta yi tana hargitsa gashin girarsa, ta hargitsa kuma ta mayar ta gyara. Sai kuma ta mi e ta shiga ban aki ta auko sabon brush na hotel in ta bu e ta dawo kan cinyarsa ta zauna ta fara gyara masa gira. Tajeta take yi ta na bi a hankali tana kwantar da ita, bayan ta gama da gira, ta dawo tana taje gashin fuskarsa tana kwantar dashi a hankali. Shi dai kallon ta kawai yake yi yana ji ina ma ace su ka ai ne a duniyar nan, ai da ya nuna mata aunar da bai nuna mata yanzu ba. Sai da ta gama