Sashe 103
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yu ba. Daga arshe kawai na ganta a gidan mu ta zo ta ce tana sona" ya fa a yana kallon idanunta kamar yadda take kallon nasa. Nayla ta ce, "Sai kaima ka ce kana sonta?." Ya girgiza kai ya ce, "da farko na yi tunanin tana shirya wani abun ne a kaina shiyasa ta ce haka, amma daga baya na tabbatar da gaske take sai na rasa gane abinda nake ji a raina akanta. Tausayi take bani, sonta nake yi, kusancin da ta samu dani ne ya yi tasiri oho ban sani ba. Ni bana mu amala da maza balle mata, indai ba Didi ba babu macen da magana mai tsaho ta ta a ha ani da ita balle kuma wani abun. Amma Narma ce mace ta farko a duniya da ta fara......" sai ya ago ido ya kalle ta yaga ko ifta idonta bata yi a kan nasa, jira take ta ji me zai ce sai kawai. Ya yi murmushi ya ja hancin ta bai ce komai ba. Nayla cikin aguwa ta ce, "ina jinka, itace ta farko da ta fara meye?." Bai ce komai ba sai kallon ta da yake yi, har lokacin yana jikinta a kwance, ya an mayar da lips insa na asa ya tostsa ka an ya kalle ta ya ce, "Ita macen da ta fara hugging ina, haka ku ke cewa da turanci ko?." Nayla bata auke ido daga kallonsa ba saboda wani abu da ta ji mai zafin gaske ya daki zuciyarta, ta kasa koda ifta ido tana kallonsa kamar yadda yake karanto kishinsa a kwance a idanunta. "Ina jinka" ta sake fa a ko motsa idonta bata yi. Ya ce, "Ta yi hakan ina tunanin sau biyu ne ko uku dai na manta, san......" katse shi ta yi ta ce, "har sau uku tana rungume ka kuma baka dakatar da ita ba?." Ya kalle ta ya ce, "ki jira na gama baki labarin mana." "Ni bana so" ta fa a tana arin aga kansa daga jikinta, ya sake ri ota ya ce, "ai baki isa ba, na fa a miki daman haushi zaki ji kika ce kina so, sai ki bari na kai arshe." Nayla ta ha e rai ta ce, "ni bana so, ban san me zan ji a gaba ba." Ya yi ar dariya ya ce, "ai kam zaki ji" ya an saka yatsan da ya sosa girarsa guda aya ya ce, "tana da wata irin dabi'a ta shigar banza Jidda, Narma haka take shigarta ko yaushe a kuma ko ina. Itace mace ta farko a duniya da na ta a tsayawa na kalli halittarta, kuma a kan Narma na fara jin ina sha'awar mace Jidda!. Amma ba wani yanayi mai girma ba fa, sai yanzu na tabbatar da abinda naji a kanta bai wuce cikin cokali ba. Wani irin dogon tsaki Nayla ta yi, ta yun ura zata mi e ya zaunar da ita ya mi e zaune ya ce, "ba ki isa ba wallahi, ai tunda na fara sai na gama. Baki san ba a katse min magana ba?. Nayla ido ya ciko da hawaye ta ce, "bana son ji, ni ka yale ni bana son jin labarin na ka" kawai sai ta fashe da kuka mai sauti tana rufe fuskarta da hannayenta. Omar ya yi murmushi ya ce, "tun farko na fa a miki ki ka i ji, dan haka sai na gama baki labari babu inda zaki je." "Ni bana so! Bana son labarin. Ni na ce ka bani labarin ko? To yanzu bana so!" Ta fa a cikin kuka sosai. ota jikinsa ya yi ta wace ta ce, "ni ka daina ta a ni." Kallon ta yake yi ganin yadda take kuka bil ha i kamar wacce yacewa wani abun ya shiga tsakaninsa da Narma. Ya an ta e baki yana dariya ya ce, "Haba Ashiq, kin san bana son kukan nan ko?." Nayla cikin kuka da shagwa a ta ce, "to ba kai ka saka ni kukan ba? Na ce bana son labarin ka i ka daina. Fa a min ka ke yi fa wata ta ta a hugging inka har sau uku, kana ce min akanta ka fara sha'awar mace, ni ka yale ni kawai" ta fa a tana kuka har lokacin. Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Ba arya na yi miki ba gaskiya na fa a miki. Wannan tausayin nata da nake ji saboda son da take yi min, da wannan kusancin da muka samu, da wannan sha'awar da na fa a miki shine ya saka nake ji a raina ina sonta ne. Ban ta a ala antuwa da mace ba sai ita, ban ta a son mace ba shiyasa nake ji a zuciyata sonta nake yi amma ba wai ina sonta in ba ne. Kai tsaye in aka ce a wanne matsayina ajjiyeta zan ce kawai tana burge ni ne a lokacin, kuma yanayin shigarta ya saka ina jin wani abu a jikina, yana sakawa na ji nima namiji ne, kuma ina da lafiya....amma fa a dah ban da yanzu. Shiyasa na kasa gane me nake ji a kanki, indai har ita sonta nayi ke me nake miki?. Ita a gangar jikina ka ai ta ta a yin tasiri, ke kuma kin tattara komai kin shiga ciki, zuciyata, jikina, jinina, raina, da komai ina jinki a cikinsa. Shiyasa nake gab da zarewa a kan aunar, wallahi Jidda soyayyarki ta iris take jira ta haukata ni. Kuka take yi sosai, ya matse ta a jikinsa, duk da kukan da take yi sai da ya kai arshen labarin hankalinsa ya kwanta, ita kuwa haushi ya cika mata zuciya, tayi dana sanin tambayarsa da ta yi. A tausashe ya ce, "na fara sonki a lokacin da ban ta a ganin ko wacce halitta ta jikinki ba, na fara sonki a cikin hijjab da nake ganinki kullum kuma jikinki a rufe. Kishinki nake ji koda da hijjab in ki ka fita haushi nake ji a zuciyata. Ita kuwa ban ta a jin kishinta ba, ban ta a jin ina jin haushin shigarta ba, ban ta a jin haushi in naga surar jikin ta bayyane ba, ban ta a jin haushi in ta ri e wani namiji ko in tana magana dashi ba. Da ace naso Narma duk abinda zai faru wallahi bazan rabu da ita ba, inda ace sonta nayi a wancan lokacin duk abinda mahaifinta zai yi sai dai yayi amma bazan ta a rabuwa da ita ba. Da yake ba sonta nake ba cikin lokaci ka an na manta da ita da rayuwarta. Jidda ke nake yiwa asalin so, inda ace kece a matsayinta abinda ya faru a gidansu ya faru a gidan ku .hmm! Sai dai a kashe ni a yarda gawata, dan wallahil azim bazan rabu dake ba. Ki yarda dani, ban ta a son Narma ba, kuma bazan so ta ba har abada!. Duk da ya fa i kalamansa dan ta ji da i ne amma sai ta ji haushi ya mamaye mata zuciya. Ta auke kai tana harare-harare. Ya an murmusa ka an ta ji ya ce, "Kin ji matsayinta a wajena wanda ya riga da ya wuce, ni ko kamanninta ma ni manta, amma itace silar canjawar Omar. Ba dan na je gidansu an fa a min maganar da aka fa a min ba da yanzu ina nan bana sana'ar komai, wata ila da aurenki ma ba a bani shi ba. Rabona ne yazo ta silarta, kuma kin san baka tsallake addararka, sannan baka tsallake raboka, duk inda yake sai ya same ka koda a cikin mahaifiyarka ka ke. Wannan shine silar ha uwata da ita, Allah ya yi nufin canja min rayuwa ta silarta shiyasa hakan ya faru. Wannan shine amfaninta kawai a gare ni!." Tana irjinsa tana share hawaye, kishinsa take ji a zuciyarta kamar ta kurma ihu, sai kallon irjin nasa take yi tana tuna yanzu Narma ta kwanta a abinda yake mallakinta, sai ta ji acin rai ya sake mamayeta ta kawar da idanu daga kai tana kuka. Cikin sigar rarrashi ya ce, "to meye na kukan uhummm? Ke ki ka ce na fa a miki, dan na fa a miki ki ke jin haushi?." a min ka ke yi tana burge ka, wata mace ce take burge ka fa, in ban yi kuka ba me zan yi?" Ta fa a murya ta a rarrabe. Shafa kanta yake yi a hankali ya ce, "ai na fa a miki a dah kenan, amma ban da yanzu." "A da in ai, a dah in itace ta farko kafin ni." "Keda na yi kishin ki shekara goma baya ta ya zata zama ta farko? Kawai rigima ki ke ji da ita. Kafin na santa ai ke na sani ko?." Ta kalli idanunsa tana turo baki gaba ta ce, "amma a kanta fara jin abinda ka fa a min kafin ni." Ya ri e fuska ta da suka hannayensa guda biyun ya ce, "kin cika rigima kawai, amma wannan ai ya wuce bai kamata ya dame ki ba. Bana son kukan nan Jidda, bana so, ki daina." Ta share hawayen tana kallon asa bata ce komai ba, ya an yi murmushi ka an ya ce, "to ki yi dariya mana, duk da in kina fushi ma kyau ki ke yi, amma dariya ta fi yi miki kyau." Ta kawar da kai ba tare da ta yi dariyar ba ta ce, "ni kaya zan je na saka." "A haka nake so yau ki zauna, bana so ki saka komai a jikinki." Ta langwa ar da kai cikin shagwa a ta ce, "Allah ni duk na takura." Juya idanunsa ya yi ya ce, "Haka mijinki yake so" ya fa a yana kwantar da kansa cinyarta wacce take ta aukar ido. Shiru tayi bata ce komai ba tana tuna surar Narma tana jin kishi kamar ana chaka mata wu a a zuciya. Murmushi ya ke yi bai ce komai ba dan itace ta saka shi, da bata ce ba da bai bata labarin ba. Ya sake kallon ta ya auke kai yana ta e baki, inda ta san antar yanayin da yaji a akan Narma da bata ata lokacinta tana kuka, sai a yanzu ya tabbatar da sha awar