Sashe 123
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ame ta. Omar ya bita da kallon takaici, ganin yadda take rawar jiki in ta ganshi kamar ta ga abun tsoro yana bashi haushi sosai, ita bata san haushinta yake ji ba take sake tsiro da abinda take tunzura shi. Ya tako ya finciko hannunta mai lafiya, ya rabata daga jikin Didi yana girgiza ta ya ce, "Ke ni Dodo ne? Meye a jikina da yake baki tsoro!" Ya fa a yana jijjigata. Luuuu Nayla ta tafi ta kife a irjinsa, ya ago ta a gigice yana bubbuga fuskarta ya ce, "Jidda!." Didi cikin fa a da fusata akam halinsa ta ce, "ka sumar da ita hankalin ka ya kwanta. Wai me yake damun ka ne? Ciwo aka jiwa yarinyar nan fa, wannan fa an da ka ke yi mata na meye?." Bai kula Didi ba hankalinsa yana kan Nayla, ya kwantar da ita a kan kujera ya auko ruwa aka yayyafa mata. Ya kalli Didi a sanyaye ya ce, "Didi ta suma fa, mu je asibiti." "Ba dole ta suma ba, wannan aga mata murya da ka ke yi kamar ba matar ka ba. Ka san ba lafiya ce da ita ba, ka duba ciwon hannunta mana. Sai ihu ka ke mata kamar ba kai ba." Tsaki Didi tayi ta arbi ruwan hannunsa ta sake shafawa Nayla a fuska. Nayla ta ja numfashi a hankali, a hankali ta bu e ido tana kallon Didi. Didi ta ri e hannunta ta ce, "Ki nutsu Nayla, ina tare dake." A hankali take jan numfashi tana kwance a jikin Didi. Ya bita da kallo yana sauke numfashi cikin yanayin da yake nu usar zuciyarsa. Tausayinta yake ji sosai, amma haushin ta fita bai sani ba har tsautsayi ya same ta ya danne tausayin, gani yake da bata fita ba da hakan bai faru ba. Shiru suka yi babu mai magana, Didi tana shafa kan Nayla a hankali, Omar ya jawo stand fan ya kunna mata iska tana ka ata. Sun kwashe mintina talatin a haka har bacci ya kwashe Nayla. Sai da baccin nata ya yi nisa sannan Didi ta zame jikinta ta saka mata pillow, ta ri e hannunsa suka dawo babban falon ta bishi da kallo ta ce, "Omar fa a ka yi shekaran jiya? Jinin wa take magana ta gani a jikinka?." Omar ya an yi tsaki ya ce, "ni ban yi fa a da kowa ba." "To jinin wa ta gani a jikinka? Meyasa ka auki wu a ka fita? Me wu a take yi a gidan nan Omar?. Sannan waye ya jiwa Nayla wannan ciwon? Ya akayi wa annan abubuwan suka faru?" Ta fa a a sanyaye tana kallon sa. aga mata hannu ya ce, "Kinga Didi, kar ki sake tunzura zuciyata na aikata abinda zan yi dana sani, ki yale ni naji da abinda yake raina." "Bazan yaleka ba wallahi. Wanne irin fa a kayi da har matarka ta firgita da kai haka Omar? Meyasa ka ke son dawo da abinda ya wuce? Meyasa ka ke son lalata hanyar da aka jima ana gyaranta sai yanzu gyaran ya kammala?. Omar meyasa zaka biyewa zuciya?." "Mtsww! Na fa a miki ba fa a nayi ba, ni ban yi fa a da kowa ba, ki yarda mana!" Ya fa a cikin masifa yana kallon ta. Didi ta ce, "me ya kawo jini jikinka in ba fa a kayi ba? Me ka yi da wu a Omar?." "To Didi fa an nayi, nayi fa an sai me?. Har gida aka zo ana yi min wula anci, ni ake agawa murya har ana cewa in ban fito ba naji tsoro, ni ake cewa in ban fito ba na ja da baya. Bana ta a ja baya, bana ta a jin tsoron ko wacce halitta a duniyar nan!. Tunda da salon da suka dawo kenan mu je zuwa, ina nan yadda nake ban canja ba!. Tunda suka yi kuskuren ta a lafiyar matata babu wanda zan bari, zasu san ja da baya ba tsoro bane" Sai ya yi asa da murya ya ce, "Ko kura ta rame ta wuce rainin karnuka wallahi! Akan a ta a min ku zan iya salwantar da rayuwar ko waye!." Didi ta fara hawaye ganin Omar in shekarun baya yana arin dawowa, dan har maganarsa ta canja ta koma ta Omar Tiger da ta auka ya jima da mutuwa, sai gashi ya dawo yana tsaye a gabanta. Kafin ta yi magana ya ce, "Jidda suka tura a kashe, Jidda suka yi arin kashewa shine silar ciwon hannunta. Tunda aka ta a min lafiyar matata har ta zubar da jini babu wanda zan yale wallahi!." Didi cikin kuka ta ce, "Omar ka rufa mana asiri, don Allah ka yi ha uri kar ka koma rayuwar da ka bari don girman Allah!" Ta fa a cikin kuka mai sauti. Ya bita da kallo kafin ya ja tsaki ya ce, "kina nufin na bar wanda suka ta a min Jidda kenan? Sun yiwa banza ko Didi..?" Ya yi wafa yana girgiza kai yana binta da kallo kafin ya ce, "kin cika min kunne, bana son kuka" ya fa a yana bata waje. Didi ta zube a wajan tayi kuka son ranta, ba kowa ne yake bata tausayi ba sai Nayla, bata san hawa da sauka ba an fara arin kashe ta a karo na biyu. Sai da ta gaji da kukan sannan ta koma wajan Nayla taga har lokacin bacci take yi. Ta kira mijinta a waya suka wuce gida dan ta san bazai saurareta a yanzu ba, zuciyarta cike da tsoro da fargaba dawowar abi'ar Omar. Shima da ya koma wajan Nayla ya koma, ya zauna a gefenta ya ora kanta a cinyarsa yana shafa kanta. Hannunta mai ciwon ya kalla yan jin wani irin unci a zuciyarsa, ji yake kamar Nayla bata dace da aurensa, tunda gashi ta silarsa ana neman rayuwarta a karo na biyu. Ya jima a haka a zaune kafin ya auke ta ya kai ta aki ya kwantar da ita shima ya kwanta yana kallon ta. Washe gari ma haka Nayla ta farka da tsoronsa, shi kuwa baya ce mata komai dan acin ran da yake ji bai ragu ba. Tunda suka gaisa ya duba hannunta ya tabbatar taci abinci tasha magani sai ya share ya cigaba da harkokinsa har ya bar gidan. Allah ya taimake ta Didi ta dawo gidan suka yini tare sai zanan ya yi mata da i sosai. Bai dawo ba sai dare, ya shigo da sallama dashi da mijin Didi suka fito falon. Didi ta amsa tana binsa da kallo ya zauna yana kallon Nayla da tayi la was a jikin Didi. Didi ta bishi da kallo sai kawai ta fashe da kuka, aramin tsaki ya yi ya ce, "to meye na kukan?." Didi ta ce, "Omar wu a ka auka fa." a min a inda kwana da makami ya zama haram, ki fa a min inda aukar wu a dan kare kai ya zama babban laifi Didi." Didi ta goge ido ya ce, "Don girman Allah Omar kar ka koma waccan rayuwar, Allah ya yi maka komai a rayuwa, ya azurta ka da mace kamar Nayla, Allah bai duba laifukan da kayi a baya ba ya ha a maka da sana'ar da ka ke ganin bu i a rayuwarka, ya ha a maka da kyautar a kamar Marmerh, meyasa zaka butulcewa wannan ni'imar da ya yi maka Omar? Meyasa zaka koma rayuwar da babu komai a cikinta dai azanta?." Ya ja numfashi ya ce, "ni ban koma waccan rayuwar ba. Abinda ki ke tunani ba haka ba ne." Didi ta yi shiru tana kuka, jin kukanta yake har zuciyarsa hakan ya saka ya ce, "Wu ar da na auka na fita ban yi amfani da ita ba, an sanda sun kama Wal iya dashi da yaransa, kafin su bar ofar gidan nan ne suka yanki wani yaro da ya biyo su Bashir suka fito. Jinin da aka ce miki an gani jinin yaron ne dana ri e shi kafin su kai shi asibiti, bayan wannan ni ban yi komai ba." Bata daina kuka ba ta ce, "Omar don Allah!" Ya katse ta ya ce, "kar yi min magiya, na rantse da Allah in hukuma bata hukunta su ba sai na auki mataki a hannuna, wallahi Omar in da bakya so ya dawo sai na dawo sa arfinsa Didi. Bazan auki raini da wula anci ba, ke kin san halina, babu halittar da zan agawa afa" Ya nuna Nayla ya ce, " arin kashe ta suka yi, da basu samu dama ba kalli yadda suka ji mata ciwo har sai da aka yi mata inki. Sai da ta kwana ta yini a asibiti saboda su, ki duba yadda take a firgice babu nutsuwa saboda abinda ya faru. Wallahi tunda suka yi gangancin ta a min mata bazan bar maganar nan ba." Didi ta sauke ajiyar zuciya tana kallon hannun Nayla ta kalle shi ta ce, "waye shi wanda ya zo in?." Omar ya ora afa kan aya ya ce, "wani matsoraci ne, tsohuwar adawa ce, tsohuwar gaba ce, tsohuwar ta un sa a ce. Ya kwana biyu yana prison, yana fitowa kuma ni ya tunkaro kamar yadda ya faru cikin azumi. Shi ya yi nasara tunda ya saka an jiwa Jidda ciwo, sannan ya cutar da mutum aya a angarena." Ya girgiza kai ya ce, "akwai irinsu da yawa, ni na san akwai irinsu masu jiran sa a a kaina" ya fa a yana girgiza kai yana tuna rayuwar baya. AbdulHamid ya ce, "ba sai a kai shi ga hukuma ba? Ko prison in ne ba sai a sake mayar dashi ba?." Omar ya kalli AbdulHamid ya ce, "Yana da iyayen gida da yawa, kamar yadda a baya nake gagarar zaman prison shima haka. Baza su bari ya sake komawa ba a yanzu. Shiyasa na fa awa Didi, in hukuma bata auki mataki ba ni zan auka" ya fa a yana nuna kansa. AbdulHamid ya ce, "Ka yi ha uri kar ka koma waccan rayuwar Omar, mu jira mu gani in za a auki matakin." Bai ce komai ba ya kalli Nayla da take lafee a jikin Didi ya auke kai. Ya sauke numfashi ya ce, "Kar