Sashe 202
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sonta, bashi da abinda yake so kamar ta. Daddy yana ji ina ma Mummy ta zama popcorn ya cinye." Marmerh sarkin wayo ta yi dariya ta ce, "Daddy dama mutum yana zama popcorn?." Ya ja kumatunta ya ce, "I wish Mummy ta zama haka, I want to be with her Sai ya daina kallon su ya kalli Nayla da take kallon sa ya ce, for rest of my life. Musliha ta ce, "Daddy, ina son Mummy." Ya bata hannu ya ce, "give me five." Suka tafa tana dariya, shima ya ce, "Daddy ma yana son Mummy." Marmerh ta ce, "Nima ina son Mummy." Suka tafa itama yana shafa kansu cikin aunarsu. Ya juya ya kalli Nayla da take ta murmushi tana kallon su ya ce, "Muna son Mummy, muna sonta sosai." Gaba aya ta ha a su a jikinta har shi ta rungume tana ajiyar zuciya. A kunnenta ya ce mata, "I want to be with you, ki yi wani abun, kin ji Mummy." Kallon sa ta yi ya aga mata yalwatacciyar girarsa sama, ta yi murmushi tana jin aunarsa na sake shiga zuciyarta da gangar jikinta. Tashi ya yi ya shiga aki bai ce komai ba, ta kalli su Marmerh da suka koma suka cigaba da game a wayarsa, sai ta kunna musu tv ta kai cartoon, suka ajjiye waya suka fara kallon tv. Nayla ta auki Mufty ta shiga dashi akin. Ajjiye sa ta yi a kan gado, ta nufi Omar da hanzari afe a jikinsa. Omar ya agata sama yana juyawa da ita a cikin akin cikin tsananin soyayya. Sai da ya gaji sannan ya sauke ta, ya ri e fuskarta tare da ha a goshinsa da tana idanunsa a rufe. Nayla ta ce, "Na gode Rouhi." Kai ya girgiza alamun baya son godiya ta sake komawa jikinsa tana ji kamar za a raba su. Haka zaman Canada ya kasance cikin shau i da soyayya kamar amare, sun ara sha uwa da aunar junansu a cikin kwanakin, Nayla ta tabbatar da har yanzu babu wata a zuciyar Omar sai ita ka ai. Satin su aya suka shiga America, daga nan suka shiga Qatar, daga nan suka shiga Egypt, daga nan suka shiga Riyadh. Satin su biyar basa asar sannan suka dawo Nigeria. *Bayan wasu shekaru.......* Nana Haleema P130 Abubuwa da dama sun faru a shekarun, ciki harda samun cigaba da Omar ya samu a fannin kasuwanci, ya shahara matu a, har ta kai ta kawo yanzu bai cika harka da an Nigeria ba, da yawan abokan kasuwancinsa an foreign countrys ne. Kasancewar da turanci a bakinsa babu abinda yake yi masa wahala aiwatarwa. Har lokacin kuma bai yi karatu ba, duk da Nayla tayi naci akan ya shiga ko da open university ce amma ya ce shi baya da bu atar yi. Omar ya kuma so busy, dan kusan ko yaushe ba ya asar, ga su Marmerh su shiga makaranta bai cika tafiya da Nayla ba sai ya zamar masa dole. Ba ma shi ka ai ba, har Bashir wani lokacin shi yake aike wata asar ya dawo. Ya aurar da su Bashir duk su ukun, shine ya auki nauyin komai a lokacin bikin, ya basu gida da kuma mota, ya yi komai da komai na biki, hatta abincin da an biki zasu ci Omar ne ya yi. Nayla itace ta auki nauyin lefe gaba aya tayi musu, aka yi musu bikin an gata babu abinda suka kashe a ku insu sai abinda ba a rasa ba. Bayan an kai amare aka aika musu da abinci, aka cika musu store taf da kayan abinci harda ruwa da lemo na bawa ba i. Ai kuwa Omar ya sha albarka a bakin ko wanne dangi, addu'a aka dinga kwarara masa, ana yiwa iyaye da Didi addu'a, ana yi masa fatan gamawa da duniya lafiya. Omar ya zama babban Alhaji,matashi mai ji da ku i da alfarma a nigeria dama asashen etare, kai da ka gansa ka ga yadda ya sake komawa ka san ku i sun zauna, saboda fatar jikinsa, maganarsa, jan ajinsa da komai na da ya canja. Ya sake zama mara sabo da mutane, in baka san sa ba ku ka ha u zaka iya fassara sa a mutum mai wula anci, amma in ka san waye shi kai zaka bada labarin kirkinsa. Duk da wannan dau ar da ya samu baya fashin ziyarar kabarin Didi duk ranar juma'a kamar yadda ya saba, ba shi ka ai ba, duk sati tare suke zuwa dasu Marmerh su yi mata addu'a su fito. Yawan shiga ma abarta da yake yi ya saka yake ganin kabarirrikan da suke da bu atar gyara, ba tare da ya san waye a kwance a jiki ba zai bada ku i a gyara. Har ya zama ya sanar da masu gadin ma abartar indai an samu kabarin da ake bu atar gyara shi a sanar dashi kai tsaye. angaren sadaka da taimako kuwa sai abinda ya yi gaba lamarinsa. Islamiyyar da aka gina ta zama babbar islamiyya da ake ji da ita a birnin Kano, har lokacin kuma komai free ake yi, babu ko sisin kowa. Duk abinda ya tashi a dangi Omar yana yi kuma yana zuwa, dangi kowa alfahari ake yi dashi, dan shekara bazata zago ta koma bai kai mutane umara ba. Hakan har ya zamar masa jiki, har ya riga ya sava rabon kujerar makka kamar ba ku i yake kashewa ba. Hakan sai ya zama abin alfahari a danginsa, ko a wani wajen in ka ce kai an uwan sane har kallon ka ake yi, saboda ko baka san sa a fuska ba sunansa ya zaga duniya. Duk abinda ya taso a dangi musamman wanda basu da arfi wajan Omar ake zuwa, kuma yana yi baya gajiyawa, sai dai yau da gobe ta an adam. Umma Saroot, Mama Zainab da Anty Aisha sun zama kamar sune iyayensa, duk wani alkhairi da ya samu baya mantawa dasu sai sun san ya samu. Zuwan su Saudia ta dalilinsa kam ba a cewa komai, haka kawai zai ce musu wani satin zasu tafi, har ta kai ta kawo ansu da jikokin su ma sun je ta dalilin Omar. Su a wajansu mutuwar Didi alkhairi ta zama a gare su, har a wajan Omar in ta zama alkhairi, tunda gashi ta silar barinta duniya yake yin aikin alkhairin da lokacin baya baya yi. Arzu i ya zauna, albarka ta samu, cigaba ya samu, abinda ba a yi tunani zai faru ba ba ya faru domin. Omar ya zama fitattce a duniya, haka kamfaninsa ya zama mafi ololuwar daraja a Nigeria da wajen ta. Babu abinda yake cewa Allah sai godiya, yana kuma fatan Allah ya ji an iyayensa da Didi Yayarsa. Mijin Didi har shi albarkar Omar bai bari ba, ba ma iya shi ka ai ba, har yayyen Marmerh da suka ha a uba aya dasu alkhairisa bai tsallake su ba. A cikin shekarun Allah ya yiwa Hajja cikawa, an yi kuka rashi kuma an yi mata addu'a, dan Nayla ta sha kuka sosai, har ta so ta fi Salma shiga damuwa duk da Salma itace suka rayu tare. Anyi bikin Jalila anwar Nayla, su Nayla an sha hidima a Kaduna, babu damar ta yi hoto sai dai ta ga yana yawo a social media ana rubuta Mrs Exclusive Footwear by Tiger. Nayla ta sake haihuwa ta haifi namiji, ta yi tunanin sunan Omar in za a saka kamar yadda Didi ta ce, amma sai ya ce a saka sunan mahaifinsa. Yaro ya ci suna Usman ana kiransa da Muhsin. ***** Nayla tana zaune a falo, Marmerh da Musliha sun dawo daga makaranta tana koya musu assignment. Marmerh tana rubutu tana kuka saboda laifin da ta yiwa Nayla ta zane ta. Tsaki Nayla ta yi cikin fa a ta ce, "Allah Marmerh in baki daina kukan nan ba zan sake dukan ki, zan yi miki dukan da zaki yini kina kuka wallahi." A lokacin Omar ya shigo da sallama, Nayla ta amsa tana kallon sa. Omar jin Marmerh tana kuka sai ya ce, "Marmerh lafiya ki ke kuka?." Jin tambayar da ya yi mata sai tashi a guje ta ri e sa ta ce, "Daddy Mummy ce ta dake ni." Ya kalli Nayla kamar zai yi magana sai ya fasa, ya araso ya zauna yana share mata hawaye ya ce, "in kun gama ku je ku kwanta ku huta tunda babu islamiyya yau." Marmerh ta ra a ta wuce a tsorace kar Nayla ta sake dukanta, ta shiga aki Musliha ma ta tashi tabi bayan yayarta. Ya kalli fuskarsa babu walwala Nayla ya ce, "Ina Mufty?." "Bacci yake" ta bashi amsa a ta aice. auki Muhsin da yake ta yi masa dariya yana mi a masa hannu, ya an yi shiru na wani lokaci kafin ya kalle ta ya ce, "Jidda bana son duka na fa a miki ba tun yau ba, in zaki yi musu fa a ki yi amma ban da duka. Akan ne zaki daki Marmerh don Allah? Me yarinyar nan ta sani da zaki yi mata dukan da zata yi wannan kukan?. Gaskiya bana so, kar na sake ganin haka. Bana so naga suna kuka ko ka an, bana so na gansu a damuwa balle su zubar da hawaye." Nayla ta bisa da kallon mamaki ta ce, "laifi tayi min, shiyasa na dake ta." "Har laifin me zata yi da zaki dake ta? Har wanne laifi Marmerh zata yi miki da zaki saka hannunki a jikinta?. Ki daki Marmerh ki ce kin daki me? Ko tausayinta baki ji ba, dukan yarinya kamar Marmerh kamar rashin tausayi ne. Kar ki sake dukan ta na maimaita miki. Ki yi mata fa an da ya kamata amma ba wai duka ba." Nayla bata ce komai ba jin ya fara magana cikin fa a ba kamar farko ba, tana tankawa birkice mata zai yi su yi kaca-kaca baza su kwana lafiya ba. Shiru ya sake ratsa tsakaninsu, cike da jin haushi ya kuma cewa, "kin yi na farko na share ban yi magana ba, kin yi na biyu ban nuna miki ba, kuma dan kinga ina yin shiru ko kunyar idanuna baki ji sai ki ka kuma yin na uku. Komai Marmerh,