← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 205

Sashe 170

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aiko min da kaya sosai." "Eh ta fa a min, ta ce min ita zata gyara mai jego." Nayla ta an yi murmushi ta ce, "Turaren wutar mai da i sosai, haka humra ma." Didi ta ce, "Sosai ma kuwa, ga ri aki da ri e jiki. Ni naga kamar kina sallah, har kin samu tsarki kenan?." Da sauri Nayla ta waiga baya ta ga Omar baya nan ta kalli Didi ta ce, "Eh Didi, bayan yin suna babu jimawa ya auke." Didi ta fahimci bata so Omar ya sani sai ta ce, "Ma sha Allah, Allah ya ara lafiya." Ta amsa da amin kafin Didi ta ce, "Ni zan wuce gida Nayla, don Allah kar ki bar komai ya dame ki." Ta yi murmushi ta ce, "Babu komai Didi." "Ya tafi da Marmerh, ki kar o min ita." Nayla ta amsa ta kar i Musliha ta bawa mai kula da ita sannan ta hau sama ta shiga akin Omar. A kwance taga Marmerh a kan gado, ta auko ta bata ce komai ba ta sakko ta kawo mata ita har mota, Didi ta shiga motar ta ja ta tafi. Didi ana tafiya Nayla ta aure fuska, ta juya ya koma gidan ta hau sama kai tsaye inda ta ganshi ta wuce. Har zata shiga akin nasa sai kuma ta fasa dan haushinsa taji sosai, ta auka zai fa a mata akan maganar Narma Abiy ya kira shi, kuma da ta tambaya sai ya ce zai fa a kuma bai fa a ba ya cigaba da harkarsa, hakan sai ya ata mata rai, sai ta ga babu amfanin ta yi masa maganar kawai ta share shi.v KRB3P105 Narma haka suka koma gida cikin yanayi mara da i, Mum tana ganin shigarsu ta mi e ta ri o Narma ta kwantar da ita a jikinta suka samu waje suka zauna Mum ta ce, "Safna ina ku ka je ne haka? Ina ta kiran ku babu wanda ya auki wayata." Safna ta ce, "Gidan Omar mu ka je." Mum ta ce, "What? Gidansa kuma?." "Eh Mum, can muka je muka same shi." "To ya aka yi?." Safna ta ta e baki ta ce, "Kusan ya wula anta mu zan ce, wata tsawa da ya yiwa Narma sai da gabana ya fa i wallahi. Amma a haka Narma kuka take yi tana so ya saurareta amma ya i, idonta ya kalla ya ce baya sonta ba zai aure ta ba, ta daina wahalar da kanta a akansa, shi in ya yi gaba baya dawowa baya." Ajiyar zuciya Mum ta yi, a lokacin Dad ya shigo falon ya ji abinda Safna ta ce ya zauna Mum ta ce, "To ya Narma? Me ta ce?" Ta fa a tana ta a wuyan Narma tana jin body temperature ta. Safna ta ce, "Ni tunda muka taho nan bata ce komai ba, amma kuma dai bata kuka, wani lokacin ta kan yi murmushi kawai." Dad ya kalli Narma ya ce, "Narma kin gani da idonki, kuma kin ji duk abinda mu ka yi dashi ko? Har baban matarsa na samu ya yi masa magana amma bai yi aiki ba." Ta kalli Dad ta ce, "Da ka amince min tun farko da haka bai faru ba Dad...." Ta ja numfashi ta ce, "amma shikenan na yarda addarata ce kamar yadda Yayarsa ta ce, zan yi ha uri, in kuma ha urin ya zama ajalina shikenan." Mum da tashin hankali ta ce, "Akan Omar sai ki mutu?." "Yes Mum, ina son shi son da ban ta a yiwa wata halitta a duniya ba, ina aunarsa matu auna." Safna ta ce, "Baza ki mutu ba Bestie, baza ki mutu ba, zaki cigaba da rayuwa kamar kowa, zaki samu wanda zai kula da ke. Ki daina fa ar wannan kalmar babu da in ji." Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad zan shiga Saudia, ina so naje nayi addu'a sosai. Bazan iya cigaba da zama a Nigeria ina ganin Faruk ba, zan tafi can ko zan samu nutsuwa." Dad ya ce, "Shikenan." Bata jira me zai ce ba ta wuce aki Safna ta bi bayanta. Dad ya kalli Mum ya ce, "Wai wannan yaron da na raina shine yake wahalar min da zuciyar yarinya haka, abin haushi abin takaici da acin rai. Saboda shi mu kazo Kano gashi zuwan bai yi amafanin komai ba, sai acin rai da ya ara mana, Na yi dana sanin saninsa a cikin rayuwata gaba aya. Ban ta a kasa yiwa an abinda suke so ba sai a kansa, a kansa na aukar mata al awari kuma na kasa cikawa. Komai suke so ina samar musu dashi, amma na gaza bata Omar." Mum tayi shiru kafin ta yi ajiyar zuciya ta ce, "amma tabbas nayi darasin rayuwa Dear. Duk yadda mutum ya ke kar ka wula anta shi dan baka san ya zai zama nan gaba ba, Ban yi tunanin an daban yaron nan zai iya zuwa wani matakin rayuwar ba, balle har ya kai ga mun nemi alfarma a wajansa ya kasa yi mana ba. Kuma wai alfarmar ma ta auren armu, ban auka zai aikata hakan ba. Tabbas Allah ya nuna mana ba komai ka ke nema ka samu ba, duk ta amarka akan duk abinda suke so kana samar musu dashi Allah ya nuna mana shi yake baka iko. Wannan da bai nufa ba gashi bai faru ba." Dad ya yi shiru bai ce komai ba, amma ya san tabbas abinda ta fa a haka ne, tsaki ya yi ya tashi ya shiga ciki yana tunani da tausayin arsa. Nayla haka ta kwana biyu tana ata rai, yana lura da ita ya kuma san dalilin fushin, a ganinsa meye na fushi tunda a gabanta ya yanke hukunci, ta kuma san bazai canja magana ba meye zata wahalar da kanta tana fushi kamar wacce aka yiwa laifi. Haka suke rayuwa kafin ya fito ta ajjiye masa breakfast ta bar falon, kafin ya dawo daga office ta ajjiye masa abinci, baya sake ganin ta sai ya yi da gaske. A ranar lahadi da yamma ya shiga falonta wanda bai cika shiga ba saboda ba in da ake yawan yi, sannan ga wacce take zaune da ita shi baya sakewa a waje in akwai ba uwar fuska. Kukan Musliha yaji daga cikin akin Nayla, kai tsaye akin ya wuce ya bu e sai ya ganta tana sallah. arasawa ya yi ya auki Musliha ya fita daga akin ba tare da ya yi magana ba. Da fa uwar gaba Nayla ta idar da sallar, Allah ya sani bata so ya ganta tana sallah ba, shiyasa take rufe akin in zata yi sallah, yau ma tautsayi ne ya saka ta bar ofar a bu A sanyaye ta mi e tsaye ta zare hijjabin daman riga da wando ne a jikinta an kanti, rigar tana da tsaho har guiwa amma bata da kauri, wando kuma black jeans ne, ta saka hula ba a sai shigar ta kar e ta kamar ba wacce take jego ba. Fita tayi zuwa falonsa, ta same shi da Musliha a zaune har lokacin tana ta kuka. Zama tayi a gefensa ya bita da kallo dan shigarta ta auki hankalisa sosai, ta auki Musliha a jikinsa, ta bu e ma allan gaban rigarta ta fara shayar da Musliha. Shi dai ido kawai ya zuba mata yana kallonta cikin burgewa, rainon ma kyau yake ma musamman a lokacin da take shayar da ita, sai ya ji kamar ya auketa ya saka a aki yana ta kallonsu. Nayla bata kalle shi ba dan ita tsoro take ji bata so ya yi mata maganar ta fara sallah, shi kuma kyaun da tayi ne yake aukar hankalinsa, ga wani haske da ta sake yi sai hamshi take zubawa mai da i shiyasa ya kafa mata ido kawai yana kallonta. Shi ya katse shirun ya ce, "Gobe zamu kai ta passport, ina tunanin zamu yi tafiya a kwanakin nan." Nayla ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "to." Daga nan tayi shiru bata sake cewa komai ba. Gumin da Musliha take yi a goshinta ta saka hannu tana goge mata har lokacin shayar da ita take yi bata cire ba. Bacci ta yi a jikinta, ta cire ta ta mayar da ma allan ta rufe, ta gyarata a jikinta tana gyara mata hular kanta. Shiru ya sake ratsa tsakaninsu, kamar ta yi masa maganar Narma amma sai ta fasa, ta gama gyara Musliha har lokacin bata kalle shi ba. Shi kuma kallon ta yake yi yana murmushi a zuciyarsa, wai kishi take yi kuma take fushi dashi, ita a wajanta haka take kishin ana share miji kuma ana fushi dashi. Bayyana murmushin nasa ya yi har ta ji sautinsa, sai a lokacin ta ago suka ha a taga sai murmushin yake yi, sai ta yi tunanin ko sallar da ya ga ta fara ne ya saka yake murmushi, dan ta san halin kayanta, tsaf ganinta tana sallah zai saka shi murmusawa dan an da e ba a ha u ba. Gabanta ya fa i sosai dan ita bata shirya koma masa ba. Bata iya cewa komai ba shima kuma bai ce ba, dan shi bai ga laifin da ya yi mata da take share sa ba. arin mi ewa ta ke yi zata bar wajan, ya daure ya ce, "Ina zaki je?." Nayla ta kalle shi ta ce, " aki zan je." "Kar ki tashi, ki zauna" ya fa a cikin bada umarni yana kallon ta. Fasa tashin tayi tare da yin ajiyar zuciya, sai ta sake bashi dariya ya sake yin murmushi ya ce, "Hajiya Jidda manya mata! Ranki ya da e gimbiyar mata, sarauniya mai mulki a duniyar Omar" ya furta yana murmushi. Bata kalle shi ba wasa take yi da hannunta, ya sake yin murmushi ya ce, "Dole sai kin saka na yi magana ne? Ni ban ga dalilin wannan fushin ba, laifin me nayi miki?." Ta kalle shi a ufule ta ce, "Sai yau zaka tambayi me ka yi min? Kwana nawa da yi min laifin sai share ni ka ke yi irin baka damu da ni ba balle fushina?." Dariyar da ya ke oyewa ta bayyana ya ce, "Jidda ni ban yi miki
Chapter 170 · 0% Book details