Sashe 95
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayla cikin kwanakin ta samu lafiya saboda tana samun kulawa daga wajan Omar, baya bari ta ta yi komai har girki shine yake mata, baya fita ko ina yana gida tare da ita, ko ya fita in bazai jima ba zai dawo. Ya tare a kusa da ita ko yaushe tana kwance a jikinsa, sai hakan ya haifar da sabuwar auna da kuma sha uwa mai yawa a tsakaninsu. Ta yarda da batun Didi, yana da sau in kai in ku ka saba, yana hira sosai kuma yana dariya. In bai ga dama bane zai tsuke bakinsa, ko ta yi magana sai dai ya yi murmushi kawai ko ya bata amsa da ido. Ta yarda da gaske ya iya girki, in ya dafa abincin ya bata baza ka ce namiji ne ya dafa ba. Nayla ta zama ar gata a wajansa, abincin ma a baki yake bata ita kuma tana zuba masa shagwa a yana biye mata. Har ta gama jinyarta Salma bata zo ba haka Jidda ma bata zo ba sai dai su yi waya, hakan ya yi mata da i dan sai take jin kunyar su san abinda ya faru har hakan ya kai ta ga doguwar jinya. Bayan sallar magriba ya shigo ya same ta a zaune tana karatun alkur'ani, hakan da take yi yana matu ar burge shi da sake saka zuciyarsa fa awa a cikin kogon aunarta. A fili take karatun dan ta fitar da ko wanne shai anu da suke cikin gidan, muryarta a hankali cike da sanyi tana karatan suratul Yusuf A.S tana lumshe da alama surar tana yi mata da (Gidan da ake karatun alkur'ani baya zama da shai anu, koda akwai su a gidan indai za a dinga karantawa za su fita daga cikin sa. Gidan da ake karanta baya zama da talauci, tashin hankali, damuwa ko unci. Karatun alkur'ani yana kawo walwala da farin ciki a cikin gida, yana kawo zaman lafiya da korar shai anu na oye da na fili. Ana so a dinga karanta alkur'ani a bayyane domin ya shiga lungu da sa o na gidan, ya za ulo mugayen mutane da mugayen aljanu ya fitar dasu daga cikinsa. In ba a samu dama ba ana iya kunnawa a tv ko mp a bu e volume yadda zai ratsa ko ina, musamman suratul ba ara. Allah ya sa alkur'ani cece mu, Allah ya sa ya zama hujja gare ba hujja akan mu ba amin.) araso ya zauna yana kallonta, ta katse karatun ta ajjiye a gefe, ta kalle shi sai ta yi murmushi kamar yadda fuskarsa take a sake. Omar ya an girgiza kai ya ce, "ya kamata nima ki dinga tuna min inda na manta, akwai inda suke yi min nauyin karantawa saboda na jima ban karanta ba." Nayla ta yi dariya ka an tana mamakin rashin girman kai irin nasa, ba ko wanne namiji bane zai iya cewa namiji an uwansa ya koya masa karatun alkur'ani ba balle matarsa, da yawan maza basu iya karatu ba, kuma suna so a koya musu amma bazai iya cewa matarsa ta koya masa ba saboda girman kai, gani suke yi kamar fa uwa ce hakan da kuma raini. Tace, "to duk ranar da ka shirya." "Da gaske nake, naga kina dariya. Ba dan Allah ya taimake ni Didi ta tsaya akan karatun wajan marigayi Malam Salahudden ai da babu abinda na sani, bana tunanin zan iya koda karatun sallah. To Didi hana ni sakewa ta yi, gashi bana iya yi mata musu, shima kuma marigayin bana iya ja da magarsa, na jima ina karatu a wajansa har na sauka nayi, daga baya ne na gudu." Nayla ta sake yin dariya sosai ta ce, "ba sai ka koma ba." Ya ora yatsunsa biyu na farko a goshinsa ya an sosa da guda aya, ya kalle ta ya ce, "Ina attending online a yanzu haka. Ni ai babu mai iya zama dani ido da ido har ya koyar dani, sai dai ke in, in baza ki tuna min ba shikenan kin huta. Kuma fa iyawa ne ban yi ba, na iya fiye da ke, wahalar karantawa wani wajan yake yi min." Nayla ta sake yin dariya ta ce, "ni na isa? Ka yi ha uri zan tuna maka. Daman alkur'ani haka yake, in ka barshi da kwana aya zai barka da sati, in ka barshi da sati zai barka da wata, in ka barshi da wata zai barka da shekara, in ka bar shi da shekara zai barka har abada." Kai ya girgiza ya ce, "balle ni bai bar ni har abada ba kuma bai bar ni da shekara ba, da ne bana karantawa saboda abi'ar da na saka a gaba, shiyasa haddar da na fara duk ta zube, amma daga baya an godewa Allah. Tunda har nayi register da ku ina na shiga ajin ai na san abubuwa sun canja" ya fa a yana an murmushi. Nayla ta wara ido ta ce, "daman ka fara haddar alku'arni?." Harararta ya yi ya ce, "ban sani ba." Dariya tayi sosai ta kwanta a jikinsa ta ce, "sorry my love." Ya yi murmushi ya ce, "A'a,YaMar." Ta yi murmushi ta ce, "Sorry YaMar." Kissing in lips inta ya yi bai ce komai ba. Waya aka yiwa masa ya auko yana kallon wayar ya dafe kai ya ce, "tun azu ake kirana da wannan number, in na auka bana gane yaren da ake yi." auka ya sake yi ya saka a speaker, ana fara magana zai kashe Nayla ta kar a suka fara magana da matar. Bayan sun kammala ta kalle shi ta ce, "Shugabar wani babban store ce daga garin Abetuka, tana so ka bata dama tana so ku ha u zata fara kar ar kayanku tana kaiwa garinsu. Pidgin English take yi shiyasa baka ji, nima dan na zauna da su a school ya saka na an iya ka an." Ya ta e baki ya ce, "to ni English in ma na iya ne balle wani pidgin? Yanzu yaushe zata zo?." "Kai zaka bata time." "Zan gani" ya fa a tana cigaba da danna wayarsa ko a jikinsa. Nayla ta ce, "Amma YaMar ya kamata ace ka fa a english inka, ba a san inda wannan aiki zai kai ka ba. Zaka iya ha uwa da turawan da suke son kayan nan, kuma ka ga dole sai da english za a yi magana dasu." Ya kalle ta ya ce, "ke ba kin iya ba?." Nayla ta ce, "na iya." "To kin iya mana, bani da ra'ayi kuma bazan yi ba." Nayla ta yi shiru dan ta san bazai yi in ba ta koma jikinsa ta kwanta ya ce, "Tashi mu je gidan Didi." Ta amsa da to ta tashi hijjabi kawai ta saka suka tafi. Yana ajjiye motar AbdulHamid yana fitowa daga gidan zai tafi masallaci. A nan suka gaisa shida Omar suka wuce masallaci ita kuma ta shiga gidan. Tana zaune suna hira da Didi duk da kunyarta take ji, amma sai ta ga Didi bata tambaye ta komai ba sai itama ta basar suka cigaba da hira. Suna cikin hirar suka dawo da sallama, suna shigowa Umma ta tashi ta shiga aki su kuma suka zauna. Didi ta kalle shi kafin ta yi magana ya ce, "Didi ina yini." Ta yi murmushi ta ce, "lafiya lau Omar, ya ka ke?." "Lafiya. Ina Marmerh?." Didi ta ce, "gata a hannun Nayla, zaka iya aukar ta in ne?." "Tsoron aukarta nake ji Didi." Ta yi dariya ka an bata ce komai ba, Omar ya kalli AbdulHamid ya ce, "ni daman wajanka na zo." AbdulHamid da murmushi ya ce, "to Allah ya sa lafiya." "Godiya zan yi maka akan abubuwan da suke ta faruwa, na gode." "Me ya faru?." "Komai ma" ya fa a ba tare da ya kalle shi ba. AbdulHamid ya yi murmushi ya ce, "to ni dai ban san me ya faru ba Omar, nima kuma na gode da ka bani auren Yayarka." Kallon asan ido ya yi masa kamar zai yi magana sai kuma ya share bai ce komai ba yana ta e baki. Omar ya kalli Nayla da take ta wasa da Marmerh ya ce, "Sai na ce ki bani Marmerh sannan zaki bani?." Nayla ta kalle shi da mamaki ta ce, "in na kawo ta baka ce ba cewa zaka yi ai baka ce ba shiyasa." Harararta ya yi, ta girgiza kai ta mi e ta mi a masa ita, ya zaunar da ita a kusa dashi bai ce komai ba. Ita kuma wallahi kunyar Didi take ji ga mijinta a zaune shi kuma ko a jikinsa. Didi ta yi dariya tana kallonsu ta ce, "Yalla ai mu yi masa gori don Allah, mu tuna masa abinda ya wuce. Na ga alama kansa yana rawa, ya manta mun san dawar garin, ba dan mu ba da yanzu bai yi rawar kan nan ba." AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "A'a babu ruwana." Shi ma Omar in murmushi ya yi dan ya san dashi take, tana magana akan aurensa da Nayla da yadda ya dinga tijara a kai. Ya ce, "Yauwa, ya batun gidan hayar nan da muke ciki ne? Yaushe ku insa zai are?." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ai da yake na fa a maka gidan abokin Yalla ai ne, da ya ji an uwana ne a gidan sai ya ce kawai ya bar gidan har sai nan shekara biyu sai a sake biyan ku in. Dan haka yanzu sai wata shekarar in Allah ya nuna mana." Harararta yake yi cikin kallon kin raina min hankali, ya ha e fuska kamar ba shine yake murmushi ba ya ce, "kin san ban yarda da wannan karatun na ki ba ko? Kamar ya an barshi har shekara biyu a naira dubu ari biyar? Wannan gidan ne za a bayar a haka?. Didi wai mai aramar wala ki ka mayar da ni ne?." Didi ganin zai fara halin nasa sai ta ce, "kwantar da hankalinka ai ba arya nake yi ba, ga yalla ai ka tambaye shi ka ji. Ba haka aka yi ba?" Ta fa a tana kallon AbdulHamid tana yi masa alama da ya amsa. AbdulHamid babu yadda zai yi dole ya yi arya ya