Sashe 84
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rage masa, amma ko alamun motsi Nayla bata yi. "Wayyo Allah, me yake faruwa haka? Jidda! Nayla! Hauwa! Ashiq ki bu e ido don Allah, ki taimake ni ki bu e idanunki!" Ya fa a kamar zai yi kuka yana jijjigata amma Nayla bata ma san yanayi ba. Ajiyar zuciya ya yi ya fitar da iska mai zafin gaske cikin rashin sanin abinda zai yi mata. Hannunsa ya kai hanci ta wai ko zai ji tana numfashi amma ji bai ji komai ba hakan ya saka shi ya tsorata sosai. yar ya lalla a ya iya mi ewa ya shiga ban akin ya ebo ruwan sanyi ya dawo yana shafa mata a fuska a hankali, jikinsa rawa yake yi sosai saboda zazza in da ya ke damunsa, amma ita yake so ya ga tayi ko da dogon numfashi ne hankalinsa zai fi kwanciya. Ya kuma shafa mata ruwan amma har lokacin bata motsa ba tana hannunsa kamar matacciya. Sai da ya shafa mata ruwa sau biyar a fuska yana jijjigata sannan ya ji ta saki numfashi a hankali ta tafi luuuu ta kifa a irjinsa. "Alhamdu lillah!" Ya furta a bayyane ya ajjiye abin ruwan ya ri e kanta ya sake jijjigata ya ce, "Ki bu e ido, ki tashi don Allah, ki ta shi kin ji....?." Nayla har lokacin bata dawo duniyar ba tana duniyar suma. A bayyane ya ce, "Wayyo Allah na, me na aikata ne haka? Yanzu me zan yi? Ban san me zan mata ba, ban sani ba" ya fa a a raunane yana shafa fuskarta kamar ya zubar da hawaye haka yake ji. Bai san abinda zai yiwa Nayla ta dawo daidai ba, bashi da ilimi a wannan angare, ba o ne shi kuma sabon shiga, ba on ma wanda bashi da ilimi kwata-kwata a kai, bai ta a sanin wani abu da ya shafi yanayin da yake ciki a yanzu ba, bai san ya zai mata ba. Tashi ya yi da yar bayan ya kwantar da ita ya arasa ya kunna hasken akin, da sauri ya kashe yana wara idanu waje ganin abinda bai yi tunanin gani. Gabansa fa auwa ya ke yi, cikin fa uwar gaba yana tambayar kansa to wannan jinin kuma daga ina ya zo? Ba dai daga jikin Nayla ya ke ba?. Da sauri ya sake kunnawa yana kallon wajan cikin tsoro da firgici, jikinsa karkarwa yake yi saboda tashin hankali da sanyin da yake ratsa shi, ya auki remote in fankar ya kashe, ya taka ya koma inda take ya sake auko ta gaba aya ya dawo da ita jikinsa. Zafin jikinta ya ha u da zafin jikinsa, sai ya sake zama wani special zafi mai huci, kallonta yake yi bai san abinda zai mai yi mata ba, bai san abinda zai yi mata ta dawowa daidai ba. Ji yake kamar ya fashe da kuka saboda takaici, bai ta a jin haushin rashin abokai da bashi dashi ba sai yanzu, tabbas da yana da abokai da babu ta yadda za a yi bai yi ilimi a wannan angare ba. Cikin hirar samari ko masu aure bazai rasa sanin abinda zai yi mata a yanzu ba, ko bai sani ba zai iya kiransu a waya ya tambaya amma yanzu bashi da kowa. Ta a screen in wayarsa ya yi ya ga har lokacin asuba ya kusa, ya runtse ido ya yi ajiyar zuciya yana sake jijjiga Nayla amma har lokacin bata numfashi. "ya zanyi!? Ya zanyi ni Omar? me zan yi mata!?" Ya fa arfi cikin yanayi na rauni da ya bayyana a tare dashi. Ruwan da ya ajjiye ya auka ya cigaba da shafa mata a fuska yana kiran sunanta a hankali, dauriya kawai yake yi amma shima bashi da lafiya sosai. A hankali yaji ta sake yin numfashi tana fitar dashi mai zafin gaske a irjinsa, ya ciagaba da shafa ruwan a fuskarta cikin salon tausayasawa da sanyin jiki matu a. A raunane ya ce, "Kin tashi? Kina jina? Ki yi magana ina so na fahimta in kin tashi, kina jina?" Abinda yake fa a kenan yana sake jijjigata. Nayla har lokacin bata hankalinta, tana jinsa sama-sama amma baza ta ce ga abinda yake cewa ba, tana cikin duniyar azaba da ciwon jiki ga zazza i mai shegen zafi. Kanta kuwa ciwo yake yi kamar zai fashe, ko ido baza ta iya bu ewa ba saboda ciwon da take yi a kanta ya yi yawa. "Jidda ki bu e ido kin ji, ban san me zan yi miki ba, Ki ta shi don Allah." Bata iya motsawa ba har lokacin, ba jinsa take yi sosai ba abinda ta sani kawai tana cikin tsananin ciwo wanda bata ta a tsintar kanta a cikinsa ba. Omar ya ce, "Wayyo Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!!. Me zan yi ne?" Ya fa a cike da damuwa yana sake kallon ta a jikinsa idanun a rufe, fuskarta kumbura sosai idanunta sun tasa alamun kuka sosai. _Wanka zata yi ko abinci zan bata? Me zan yi mata ne?._ abinda ya tambaya kenan a zuciyarsa yana kallonta cikin so da auna da kuma tsantsar tausayi. Idanunsa lumshewa suke yi saboda jirin da yake aukarsa, amma ya i rufe idon saboda Nayla, ya tabbatar indai ya rufe idonsa to bai san lokacin da zai bu e ba, in ya rufe ido ita kuma ya kenan?. Kallon ta ya tsaya yana yi tana sauke numfashi a hankali ga hawayen da suke sakkowa daga gefen idanunta, bakinta ya mutu murus ta kasa koda bu e bakin balle ta yi magana, danunta kuwa a kulle su ke, ko motsa idanun bata son yi balle ta bu w su. Kiran sallar asuba na farko aka fara yi a masallaci, ya runtse ido ya kwantar da ita ya mi e yana tunanin abinda zai yi mata. Ban aki ya shiga ya fito ba tare da ya yi komai ba, jiri ne ya kwashe shi, ya tafi zai fa i ya yi sauri ri e bango da yar yana jan numfashi a wahalce amma ita yake kallo. Yadda yake jin sanyi ya san itama haka, ya auka zai samu sau i da ya zubawa kansa ruwa sanyi amma sai ya ji azaba ya arasawa kansa, shiyasa yake tunanin aukarta ya zuba mata ruwan sanyin. Fita yake so ya yi yaje kitchen ko zai iya dafa mata ruwan zafi amma bazai iya ba. Shi sam ya manta da akwai water heater a ban akinsa, shi daman bai damu da ruwan zafi ba, ko a gidansu haka yake yi bai cika amfani dashi ba, tun Didi tana magana har ta daina, ta kan ce an ce mai wanka da ruwan sanyi zai ji sanyin ashi, shi kuma ya bata amsa da ya yi sanyin nama ba ashi ba. Takaici yake ji a zuciyarsa, yana ji yana gani ya kasa taimakawa matarsa wacce yake matu auna, inda ace yana da dama kuka zai yi amma kukan ma ya i zuwa cikin idanunsa. yar ya iya fita zuwa kitchen, biyu-biyu yake gani amma a haka ya auki kettle ya zuba ruwa ya kunna ya zauna a kitchen in akan tiles yana jira ya yi. Da yar ya iya mi ewa tsaye ya auki kettle in ya fita yana tanga i kamar an maye, ruwan zafin ya an zuba a hannunsa ya yarfe hannu cikin azabar da ta ratsa shi, amma bai sakata ba ya shiga ciki ya juye ya kunna ruwan sanyi bai jima yana zuba ba ya kashe ya fito. Kallon ta yake yi yana tunanin ta yadda zai iya aukarta ya kai ta ban akin, a hankali ya araso yana numfashi sama-sama ya gwada aukarta amma ya kasa ya mayar da ita ya ajjiye. Ya sake gwadawa ya sake kasawa ya sake kwantar da ita, cize bakinsa yake yi ya dafe bango yana ri e jijiyoyin kansa da suke harbawa kamar zasu tsinke. A karo na uku ya gwada ya auketa amma shi da ita suka yi baya suka koma kan gadon suka zube. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Abinda yake maimaitawa kenan, ko a mafarki bai auka wannan yanayin zai riske shi ba, amma sai gashi ya riske shi a lokacin da bai shiryawa hakan ba. yar ya iya mi ewa ya sake aukarta ya taka da yar, ya kuma takawa sai ya tsaya cak yana sauke numfashi yana jin jiri na aukarsa. A haka aka arasa bandakin tana jikinsa kamar mara rai, du awa ya yi ya zube a asan tiles in ban akin, tana jikinsa har lokacin ya auki ruwan yana zuba mata tun daga kanta har afafunta a tunaninsa hakan ne zai saka ta dawo daidai. Dogon numfashi Nayla ta ja, ganin haka ya saka shi ya cigaba da zuba mata ruwan tun daga gashin kanta har farcen afarta yake ji awa da ruwa yana bubbuga fuskarta. Numfashinta sama-sama yake fita, tana jin zubar ruwan a jikintq ta kuma dawo hayyacinta kawai bazata iya magana bane, ita ka ai ta san halin da take ciki. Sai da ruwan nan ya are tass yana kwara mata sannan ya kalle ta ya ga har lokacin dai Nayla bata dawo daidai ba. Ganin ta yi dogon numfashi har yana jin fitar nunfashinta sai ya ji da i a ransa, ya sake ota a karo na biyu suka fito ya ajjiye akan sofa, kan gadon ya arasa ya janye bedsheet in da ya la'ance ya auki duvet ya jefa a kai ya an ware inda zata iya kwanciya ya sake dawo da ita kan gadon. Rigar baccinta ta jiya ya mayar mata ya koma ya zube akan kujera yana juya kai saboda ciwo. Shi a tunaninsa iya abinda zai yi mata kenan, ya kuma gama yi mata shiyasa yake hutawa. Nayla kuwa zafin ciwon kai da zazza i ya saka numfashinta yake sama da asa ta kasa fahimtar a wacce duniya ta ke. Rawar sanyi take yi sosai alamun zazaa i, ya kalle ta sai ya mike da yar ya fita ya shiga akinta ya auko blanket ya dawo ya rufa mata ya zauna a gefenta ya ri e hannunta yana murzawa a hankali. Zafin jikinta ya dame shi sosai, duk da shima haka nasa jikin yake amma ta ita yake yi ba ta kansa