Sashe 55
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bu e baki ya ce mata ba ya sonta, ido da ido ya kalle ta ya fa i haka, ya kuma ce har abada bazai so aurenta ba, gwara ta ha ura duk da son da take yi masa. A haka ta fito ta bu e kayan ta saka doguwar riga ya zauna a gefen gadon. Wayarta kalla ta ga tana haske, ganin sunan Salma sai ta share bata auka ba ta jingina da fuskar gadon idanunta a lumshe. Ranar da ta fara ganin murmushinsa ta tuna a gidan Didi, da ranar da suke je Kaduna ya yi mata murmushi da ranakun da suka biyo baya. Zuciyarta harbawa take, in ta ce bata son Omar arya take yi amma ya zata yi? Hakan shine mafita a gare ta da rayuwarta. Ranar tare suka kwana a akin da Mama kasancewar mai gidan baya nan. Duk motsin da Nayla zata yi sai Mama ta bu e ido ta ce lafiya, hakan shine yake yiwa Nayla da i take jin Mama kamar Ummanta da ta bar duniya. Da safe wanka tayi ta shirya, sai dai kallo aya zaka yi mata ka hango damuwa da ramar da tayi lokaci aya. Ummimi ce ta shigo ta kalle ta ta ce, "Yaya Nayla ki fito falo in ji Mama." Nayla ta girgiza kai ta fito zuwa falon a sanyaye ta sakko daga saman. Dukkan su suna zaune wani yana danna waya wani kuma yana shan tea. Kafin Nayla ta arasa sakkowa aka yi sallama aka shigo falon. Wacce take bin Abbas ce da ake kira da Yaya Zahra da yaranta guda biyu suka. A guje suka taho wajan Mama suka fa a jikinta suna murnar ganin ta. A lokacin Nayla ta sakko daga saman ta ce, "Yaya Zahra sannu da zuwa." Anty Zahra ta kalleta tayi murmushi ta ce, "Naylan Mama." "Na'am Yaya, sannu da zuwa." "Yauwa Nayla, lafiya ki ke naga fuskarki ta an kumbura?." Mama ta ce, "bata jin da i ne." Nayla ta kalli Abbas da Khalid ta ce, "Yaya Abbas Ina kwana, ya Khalid ina kwana." A tare suka amsa Abbas ya ce, "ya jiki? Ina fatan baki kwana da zazza in ba." Nayla ta ce, "Eh ban kwana dashi ba, tunda Yaya Khalid ya yi min allura ya sauka." Khalid ya ce, "Amma fuskarki ta kumbura, kuka kika kwana kina yi ko?." Nayla bata ce komai ba Khalid ya ce, "Nayla kar ki stressing kan ki da yawa fa, ko meye yake damunki ki kwantar da hankalinki ki sanar da Mama in ba haka ba zaki jawowa kan ki ciwo da arancin shekarunki, ki kwatar da hankalinki ki fa i duk abinda yake damu ki bazai gagari iyayen mu ba in shaAllah." Nayla ta aga kai alamun to. Yaya Zahra ta ce, "A nan ta kwana kenan, Mama lafiya dai ko?." Mama ta ce, "eh to lafiyar dai zan ce. Abbas in baza ka je aiki ba anjima zaka kaini gidan Daddy." Abbas ya amsa da to amma ya damu da ya san damuwar da ta saka Nayla a wannan yanayi. Mama ta ce, "Nayla tashi ki je ki ci abinci." Bata musa ba ta tashi sai gata ta dawo da tea a hannunta zama tayi tana sha suna hira a falon sama-sama. Nayla ce ta mi e tsaye a sanyaye ta ce, "Mama bara na auko wayata a sama." Mama ta amsa mata ta hau saman da kofin a hannunta. Yaya Zahra ta ce, "Wai ne ya same ta ne? Ba dai sakinta ya yi ba?." Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce, "bai saketa ba, amma ta ce sakin take so, ita kar a auki lokaci kawai ya saketa ta gama auren, shiyasa zan je na samu Daddy anjima." Yaya Zahra ta ce, "Tofa, ita da kanta ta ce ta gaji da auren?." Mama ta amsa mata Yaya ta ce, "ba a san dalilin ta na fa in hakan ba, tunda har ta furta da kanta gwara a raba auren." Mama ta ce, "shiyasa zan sanar da Daddy, ta inda aka hau ta nan ake sauka." Yaya ta amsa suka cigaba da hira har Abbas da yake zaune. Kamar Yadda Mama ta ce bayan sallar azahar Abbas ya kai ta gidan Daddy, ta same shi a falo ta yi masa bayanin yadda suka yi da Nayla. Abin ya bashi mamaki sosai, ya ce aje a kawo masa Naylan. Abbas aka saka ya koma ya aukota. Lokacin da ya koma a zaune ya same ta tana waya ita da Salma, ya kalle ta ya ce, "Nayla ta so mu je, Daddy yana son magana dake." Kashe kiran ta yi ta ce, "To bara na auko mayafi" ta fa a a sanyaye tana wucewa ta hau sama ba jimawa ta dawo suka tafi. A falo ta samu Daddy da Mummyn su Salma da kuma Mama. Ta shiga suka gaisa gaba aya ana tambayarta ya jiki ta amsa musu da ta ji sau i. Daddy ya ce, "Hauwa na ji abinda Maman ki ta ce, auren kawai ki so a raba?." Nayla ta aga kai a hankali kamar mai ciwon wuya. Daddy ya ce, "wani abun ne ya faru?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Babu komai Daddy." Daddy ya ce, "Haka kawai ki ke so a raba auren babu abinda ya faru?." "eh daddy." Daddy ya ce, "to shikenan. Yanzu a wajan Maman ki zaki zauna har sai an raba auren?." Nayla ta aga kai alamun eh Daddy ya ce, "babu laifi, shiga wajan an uwanki ku gaisa." Nayla ta mi e ta shiga cikin gidan. Mummy ta kalli Daddy ta ce, "Jikinta a sanyaye yake duk yadda aka yi dole ce ta saka ta furta wannan kalmar Daddy, kamar ba a son ranta ba." Mama ta ce, "Kamar a gabanki akayi Mummy. Jiya tana fa a min jiya tana hawaye alamun abun yana yi mata ciwo sosai, ni da farko na auka ma sakinta ya yi." Daddy ya yi ajiyar zuciya ya ce, "mu jira mu gani in mijin na ta zai biyo sahu, in dai ya biyo sahunta matsalar ba mai girma ba ce, in kuma bai biyo sahu ba matslaar mai girma ce wacce yake nuni da wata ila bai kar i aurenta ba ne har yanzu." Mama ta ce, "haka ta ce min daman wai baya sonta." Daddy ya yi murmushi ya ce, "shiyasa na fa a miki, in har yazo nemata matsalar ba mai girma ba ce, zai biyota dan ni dai bazan neme shi ba, amma indai bai zo ba za a raba auren kamar yadda Naylan ta nema. Daman dukkan mu ba son zamanta dashi mu ke yi ba, babu yadda zamu yi ne ya saka muka amince tunda tana so kuma mahaifinta ya zartar da hukunci. Zan kira mahaifinta na sanar dashi yanzu dan ya san abinda yake faruwa. Ni dai bazan nemi Omar dan naji abinda ya faru ba, tunda har ya san ta baro gida zan saka masa ido na bashi lokaci naga zai nemeta, kamar yadda na fa a in yazo daidai ne, in bai zo ba ma daidai ne." Mama ta ce, "hakan ya yi, gwara ma da hakan ya faru ko babu komai ta huta a gida, har ga Allah wannan auren nata ba wani kwanta min ya yi ba." Daddy ya murmusa ya ce, "kar dai ki shiga tsakanisu ki zo ki ji kunya, babu ruwanki da nuna mata bakya son aurenta, babu ruwanki da nuna mata bakya son mijinta, ki tsaya a tsakiya kawai, in tayi ruwa rijiya in bata yi ba masai. A yanayin da take magana acin rai ne ya saka ta ce a raba auren, mu bata lokaci ta warware daga baya sai komai ya biyo baya." Mama ta ce, "Allah dai ya kyauta kawai." Aka amsa da amin. Sai bayan sallar magriba sannan Nayla da Mama suka koma gida. Abiy yana zaune yana amsa waya, Mama na gefensa sai Jawad kamar ko yaushe yana cewa, "To Alhaji Junaid duk abinda ku ka yanke ai daidai ne, dani da ku duk aya ne a wajan Nayla, dukkan mu iyayenta ne, abinda ku ka ga daidai ne ku aiwatar kawai babu ata lokaci ko jiran umarnina." Murmushi ya sake yi ya ce, "Na baka wu a da nama a wannan lokacin ma, duk abinda ka yanke ka ke ji a zuciyarka daidai ne ka yi kawai." Abiy ya sake cewa, "babu komai ai duk aya ne. Allah ya za a abinda ya fi alkhairi." Daga haka suka yi sallama Abiy ya yanke wayar. Mama ya kalla da take kallonsa ya ce, " arki Nayla ce ta bar gidan mijinta ta koma gidan anwar mahaifiyarta." Mama ta ce, "Akan me?." "Wai ta bar auren, ita ta gaji." Mama ta ce, "Subahanallahi! Allah ya sa ba wani abun ya yi mata ba. Kai wannan yaro an yi shai ani wallahi." Abiy ya murmusa kawai bai ce komai ba. Jawad ya ce, "Abiy akan me take so a raba auren to?." Abiy ya ce, "ta ce kawai ita bata son zaman auren a raba shi." "To ina mijin na ta?." "Ni ban sani ba Jawad, na basu wu a da nama duk abinda suka yanke daidai ne. In sun raba auren daidai ne, in ba su raba auren ba ma duk aya a wajena." Mama ta ce, "Wannan aure babu abinda zai raba shi, in sha Allah Nayla sai ta cigaba da rayuwa a cikin sa!" Mama ta fa a tana kallon Abiy. Abiy da Jawad duk kallonta suka yi cikin mamakin kalamanta, ganin suna kallon ta da alamun mamaki akan fuskarsu sai ta ce, "Yarinya arama da ita ace ta zama bazawara? Ina amfanin wannan auren tun farko amma ta dage sai da aka yi?. Bana so a raba auren nan saboda an lalata mata uruciyarta, tana yarinya da ita a ce ta zama bazawara abin sam bai yi ba. Duk wacce take amsa matsayin uwa a wajanta bazata so auren nan ya mutu ba." Jawad ya ce, "ni kam Mama ban ga aibun hakan ba, in hakan shine mafi alkhairi Allah ya tabbatar, abinda ya kamata ki ce kenan." Ta harari Jawad ta ce, "Baka da hankali ai, baka san meye zawarci ba. Dan rashin