← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 205

Sashe 48

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take tana kallon sa. are mata kallo yake yi, sabuwar sha'awarta na sake kunnuwa a zuciyarsa. Tana sanye da shigarta ta ko yaushe, ya ce, "Bazan sake ki ba Narma, ko me zai faru wallahi ina tare dake matsayin miji." Narma ta ce, "Wallahi sai ka sake ni, ai ko kana so ko baka so zama da ni ya are a rayuwarka." "Haka ki ke tunani kawai, amma har yanzu lokaci sakin ki bai yi ba dan ban ga wanda ya isa ya saka na sake ki ba Narma. Wato na sakeki ki komawa wancan an shaye-shayen an daba ko? To baki isa ba wallahi. an daba ya fi min kai sau dubu, Ina sonsa son da bana yi maka shi, kuma bazan yi maka shi ba har abada." "Wannan ke ta dama kuma Narma, abinda na sani you're my wife, dole kuma ki yi abinda nake so" ya fa a yana are mata kallo. Mum ce ta katse shi ta ce, "Ashraf fita ka bar gidan nan, ka cire komawar Narma gidan ka domin baza ta ta a komawa ba har abada." Ya kalli Mum ya ce, "Mum ko court bazata raba aurena da ita ba wallahi, Ina son zama da ita." Dad ya ce, "ka san kana sonta ka dinga wahalar da ita?." Narma ta ce, "Dad ba ya sona, ya fa a min ba sau aya ba baya aunata." A fusace ya juya ya kalle ta ya ce, "eh bana son ki, bana aunar ki kuma bazan sake ki ba!." Dad ya kalle shi cikin tsananin fusata ya ce, "you know what? It's my fault, laifina ne da na dau i aure na baka ba tare da na yi bincike mai kyau a kan ka ba. Laifina ne da na duba relationship ina da mahaifinka na dau i my own daughter na baka ba tare da ka bayar da ko sisi ba. Amma yanzu dole sai ka sake ta ko kana so ko baka so Ashraf, zaman ta da kai ya kare." Mum ta ce, "Ko kunya baya ji, in front of our eyes yake fa ar baya son Narma, kuma kana expecting zamu sake baka ita ne ta zauna da kai? Ka goge wannan tunanin daga ranka Narma baza ta sake zaman auren da kai ba." "I'm sorry Mum and Dad, bazan iya sakin ta ba kome za a yi sai dai ayi. Kuma zan auki matata a duk lokacin da naga dama" ya fa a yana fita daga falon. Narma ta kalli Dad cikin kuka ta ce, "Dad kalli abinda ka jawo mana, lokacin da na ce bana sonsa baku saurare ni ba ku ka yi forcing ina akan aurensa. Na ce ban so amma babu wanda ya saurare ni balle a fahimci bana so in. Dad duk abinda ya same ni ku ne silar komai, duk halin da na shiga ku ne ku ka jawo, inaa da wanda nake so, na kawo shi gidan nan ku ka wula anta shi saboda ra'ayinku, na auka duk abinda nake so zaku yi min amma kun kasa. It's over!" ta fa a tana hawa sama a guje tana kuka sosai. Mum ta kalli Dad a fusace ta ce, "Duk abinda ya faru da ata bazan yale Ashraf ba wallahi, babu ruwan da abinda yake tsakanin ka da mahaifinsa, zan yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata" ta fa a tana barin dining in itama. Dad ya yi shiru ya bisu da kallo a lokacin Najwa ma ta tashi ta hau sama, ya yi ajiyar zuciya yana ji a zuciyarsa duk abinda ya faru da Narma kamar shine sila. KRB3P025 Arewabooks@nanahaleema11. An yi shagalin sunan a Kaduna, yarinya ta ci sunan mahaifiyar mijin suna yi mata la i da Mihada. Nayla a waya take ganin komai gaba aya ta damu da rashin zuwanta, sai da Yaya J ya kira ta ya dinga rarrashi sannan ta sake ta cigaba da harkokinta Zaman su da Omar yana nan yadda yake babu abinda ya canja, tana fita aikin ta dawo wani lokacin ta wuce gidan Hajja ko gidan iyayenta da suke garin sai dare ta dawo gida. Kamar ko yaushe ranar Alhamis Nayla ta dawo daga wajan aiki tana zaune tana kallo a tv, Didi tayi mata waya take sanar da ita an yi rasuwa a gidan Kawunsu inda suka ta a zuwa. Nayla ta ce, "To na taho yanzu ne Didi?." Didi ta ce, "sai gobe za a yi jana'iza, ki bari sai goben, sai dai kuma zaki je aiki." "Babu komai zan samu na zo, ai Friday ce. Allah ya ji an rai." Ta amsa da amin ta kashe wayar. Washe gari kuwa da wuri ta shirya kamar zata tafi aiki ta wuce gidan rasuwar dan ta gane gidan. Tun daga bakin layin zaka san anyi rasuwa, dan manyan motoci ne sosai na mutane da suka zo jana'iza. Ta ajjiye motarta shiga gidan ta kira Didi ta sanar da ita inda take aka rakata suka zauna tare. arfe tara aka yi jana'iza, Didi ta ri e hannun Nayla tana kai ta wajan wanda mutuwarta shafa tana yi musu ta'aziya. Har su Kawu sai da ta yiwa, lokacin goma na safe ta yi sannan suka yi sallama da Didi ta wuce wajan aiki a lokacin. Bata jima sosai ba ta koma gida ta sanar da su Hajja rasuwar dan su yiwa Didi gaisuwa. Tana zaune da yamma sai ga Didi ta shigo, kana ganin yadda ta shigo ka san ranta a ace yake sosai, ga cikinta ya girma sosai duk ta saka babban hijjabi amma ana gani, fuskarta duk ta canja tayi ja sosai. Didi ta kalli Nayla da take yi mata sannu da zuwa ta ce, "Nayla Ina Omar?." A lokacin ya shigo falon ya kalle ta ya ce, "gani." Didi ta juya ta kalle shi ta ce, "Meyasa kai wani lokacin baka aiki da tunani ne Omar? Mutuwa fa aka ce, matar Kawu babba ce ta rasu amma ka kasa zuwa ka yi musu gaisuwa. Tun Daren jiya na fa a maka, maimakon ka je ko ladan jana'iza ka samu sai baka je ba saboda wani banzan tunanin ka. Ai mutuwa ta fi gaban wasa, tunda aka ce ta mutu ko meye a zuciyarka sai ka kawar dashi ka yi mata addu'a haka musulmi na gari yake. Kai ka ai aka yiwa laifi a duniya ne ko kai ka ai ne me zuciya!?." Kallon ta yake yi jin yadda take yi masa fa a shiyasa ya shareta, in ya tanka ofar da yake tsaye a jiki ma ta tanka. Didi ta ce, "Yanzu ka wuce mu je ka yi musu gaisuwa, in har na isa da kai ka wuce mu je yanzu ba anjima ba." e baki ya yi ya ce, "bazan je ba, da nawa mahaifin ya bar duniya itace ta fara kallona ta ce an rage iri a duniya, dan yanzu ta mutu kuma sai ace na je gaisuwar mutuwarta? Kema kin san wasa ki ke yi." "Ta riga ta mutu, ko me tayi maka ya kamata ace ka manta dashi ka yafe mata. Kuma ba dan ita zaka je gaisuwar ba, saboda Kawu zaka je da kuma anta." Omar ya ce, "Didi babu inda zan je gwara ma ki daina wahala da bakin ki." Didi ta fusata sosai ta ce, "Sai ka je Omar, in dai na isa na fa a maka sai ka je!." "Bazan je ba, akansu ki ke aga min murya haka? Su in su waye a rayuwata?." "Iyayenka, iyayenka ne ko kana so ko baka so, danginka ne wanda baka da kamar su." "Iyayen wasu dai amma ban da ni, ba iyayena ba ne kar ma ki sake danganta ni da su!" Ya fa a cikin muryarsa mai amo wacce ta sa Nayla ta toshe kunnenta. Didi ta ce, "ko kana so ko baka so iyayenka ne, gwara ma ka hutar da kanka ka so. Wannan banzar zuciyar babu inda zata kai sai dana sani." Bai tanka mata ba ya kawar da kai ta ce, "Ko baka so dole ka je ka yi musu gaisuwa, in dai na isa da kai." Ya girgiza kai ya ce, "kin gama yi min dole Didi, kin ga ina yin abinda ki ka ce shiyasa ki ke yin abinda ki ga dama. To ta are!" ya fa a a kausashe yana kawar da kai gefe. Didi ta matso kusa dashi ta ce, "wai wacce irin zuciya ce da kai?." "Wacce Allah ya yi min." arya ka ke, kai ka sakawa kan ka wannan ba in hali ba Allah ba. Kuma zan gani in ina da darajar da zance ka yi abu ka yi, in kuma bani dashi zan gai." Omar a fusace ya ce, "Kina dashi, amma a wannan lokacin bazan yi ba!." "Iyayenka ne dai ko ka i ko ka so, sune danginka, komai na rayuwarka sai ka neme su, su ne suka kar ar maka aure!. Ko gobe zaka sake yin wani abun wajen su dai zaka je, baka da inda ya fi su, kaga kenan dole ka ce da mijin iya baba." Nayla bata ta a ganin wannan fa an na su ba, ta saba ta ga suna hira da nisha i da aunar juna, ganin su a haka gaba aya sai ta damu saboda yanayin da Didin take ciki. A sanyaye ta ce, "Didi don Allah....." "Ke!!" Ya fa a cikin tsananin tsawa yana kallon ta da idanunsa da suke waje suka kuma koma jajaye. Baya Nayla tayi a firgice, iya tsawar da ya yi mata ma abin tsoro ne balle kuma idanunsa da suke a waje. Ya nuna ta da yatsa ya ce, "kar ki sake cewa komai a wajen nan, duk ba ke kika jawo ba? Ba ke kika jawo min ake yi min gorin su ne suka kar i aurena ba!?" Ya fa a yana kallon ta kamar ya tsinka mata mari. Didi ta kalle shi ganin ya koma kan Nayla ta ce, "Dani zaka yi ai ba ita ba, ni ce nayi maka laifin ba itace tayi maka ba Omar!." "Auren da ki ke batun su suka kar ar min ni nace Ina so? Ko na ce ina son auren ne? Ba ha a baki ki
Chapter 48 · 0% Book details