Sashe 71
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi murmushi ta ce, "mu ne Umma, barka da yamma." "Barka dai Nayla, ya mai gidan naki? Omar sarkin an rigima." Murmushi ta yi bata amsa ba dan yadda take mata magana ba su san tana gida ba. Umma Saroot ta ce, "Omar akwai rigima, ina jinsa yazo yana ta wasa da arsa." Nayla dai bata ce komai ba sai murmushi kawai. Umma ta ce, "in zaku ci abinci akwai." Salma ta ce, "babu komai Umma, mun oshi." Ta yi murmushi ta shiga aki. Jidda ta ce, "Didi wallahi Umma na da kirki sosai, gata suna kama da Omar." Ta yi dariya ta ce, "maza ya ji ki." Kira ne ya shigo wayar Didi ta kalli mai kiran ta kalli Nayla ta ce, "Mijinki na kira na, ban san da me yazo ba kuma." Nayla bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Didi ta auka ta saka wayar a speaker dan ta san bazai wuce zancen Nayla ba. Daga can angaren ya ce, "Didi!." Didi ta ce, "Na'am Omar." "Kina lafiya? Ya Marmerh?." "Lafiya lau, Na ga baby swing da ka aiko mata dashi, Omar yana da tsada fa, na yi tunanin siya na fasa saboda ku in da yawa." "In bakya so ba sai ki ona ba, kuma kar na sake yin abu ki ce min yayi tsada, ku ina ne ai ko?." Didi ta ce, "na ka ne, amma...." "Kin ga Didi, ba ke na yiwa ba ai ata na yiwa, In ke ce zan ma kalle ki ne?." Tayi dariya ta ce, "Ya na jika haka kamar mara lafiya? Lafiya dai ko?." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Gaba aya na zama mai rauni kamar ba ni ba, ko magana bana so ayi min haushin yarinyar can da nake ji da an yi min magana sai na fara fa a, ita kuma na kasa yi mata fa an. Ni da bani da yawan ciwo amma yanzu kullum da ciwon kai da zazza i nake yini, ba kuma komai ne yake kawo min ba sai damuwa." Didi ta kalli Nayla da take kallon Didin tayi murmushi ta ce, "Wacce yarinya kenan?." "Wa nake da ita bayan ke da Marmerh?." "Oh ai na ji kace yarinya ne shiyasa. Me matar ta ka ta kuma yi maka kuma?." "Meye ma bata yi ba." "Amma ka ce ka daina yi min maganarta, har ka sakko daga fushin?." Omar ya ce, "na fa a miki na canja, ni kaina canjin nan yana cutar da ni. Didi na kasa mantawa da ita kamar yadda nayi niya, gashi sai da na kira ki dole na yi maganarta. Amma ita aukar kalamaina take yi matsayin na arya, a duniya akwai wanda zan yiwa arya ne dan na burge shi... sam babu." Didi ta yi murmushi ta ce, "ni sai ka kira ni kai ta masifa kuma ba ni nayi maka laifin nan ba, Nayla ce ba ni ba." "Didi!." Jin yadda ya furta a sanyaye sai ta ce, "Na'am." Omar ya ce, "ya zan yi ta amince da gaske ina sonta? Me zan yi da zai tabbatar mata da ina son rayuwata da ita kuma bazan iya rabuwa da ita ba? Me zan yi?." Didi ta ce, "na ce maka duk kalaman da ya zo zuciyarka shi zaka fa "Ki daina ora ni a keken era, haka ki ka fa a min kwanaki, da na je gidansu na fa a mata abinda yazo daga zuciyata arshe kuka ta dinga yi, Bana so na ga tana kuka ko kusa." Didi ta ce, "Alhaji Omar an uwan Aisha, mijin Nayla baban Marmerh. Yanzu me ka ke so nayi maka?." Murmushi ta ji ya yi mai sauti amma bai ce komai ba. Didi ta ce, " an soyayya, Ina jinka kayi magana mana." "Kin raina ni ko? Dan kin ga yanzu na zama wani iri ko? To Tiger har yanzu sunana ne wallahi, kawai wannan matar tawa ce ta ora min pressure, ko ya akayi ma na fa a da yawa haka oho. Ni fa soyayya bata yi daidai da zubina ba, ban san ya aka yi na bari na yi zurfi haka ba. Allah in aka auna jinina ya hau." Dariya Nayla tayi dan wallahi dariya ya bata sai kuwa ta ji ya ce, "Waye yake dariya?." uwa na yi tana yiwa Marmerh wasa." "Amma kamar na san wannan muryar." "Gaskiya baka santa ba." "Ya yi. Ba fa ko wanne banza zaki dinga bawa yarinyar nan ba, wasu suna zuwa aukar yara ne dan su cutar dashi." Didi ta yi murmushi ta ce, "to Omar, ka samu ka yi magana da Nayla in ko zaka ji da "Ni bazan kira ta ba Didi, ki barta tayi tunani kamar yadda ta ce min. In bata da ra'ayi shikenan." "Sai ka rabu da ita in?." "Hmm! Inda za a yi tashin hankali dani kenan, Allah sai na tashi garin Kano harda Kaduna garinsu. Na kira ki ne ji lafiyar ki da ta Marmerh kuma na ji, Sai anjima" ya fa a yana yake wayar ta bi wayar da kallo tana murmushi. Salma ta ce, "Omar kenan, wato shi soyayyar ta sa ma ta musamman ce. Ita da yi masa laifi ke da shan fa a." Didi ta yi murmushi ta ce, "Ranar da ya je gidan Mama yana dawowa ya kira ni, yadda ya dinga yi min masifa sai ki auka wani laifin na yi masa. Ya ce na shaida bazai sake yi min maganar Nayla ba, Amma gashi ba a je ko ina ba ya kasa" ta fa a tana kallon Nayla da take murmushi. Didi ta ce, "Nayla na fa a miki gaskiya? Wallahil azim Omar yana sonki, ban ta a ganin rauni a tare dashi ba sai a kan soyayyarki, Omar in ya ce ya bar abu ya bari amma gashi ya kasa sai da ya yi min zancen ki. Ban ta a ganin halittar da Omar ya bawa ha uri ba sai ke, babu halittar da Omar ya yi kewa sai ke. Kamar yadda ya ce haka ne, shi ba mai yawan rashin lafiya ba ne, amma a kan ki sai da ya sha fama da zazza i da ciwon kai. Kar ki yi tunanin ina fa a miki haka ko dan ki koma masa ko kuma dan Omar an uwana ne, kin san ni mai fa a miki gaskiya ce a kansa. Bazai miki arya dan ya burge ba kamar yadda ya ce, duk abinda ya fa a miki wallahi ba arya yake yi ba Nayla, da gaske ke yana sonki da zuciya aya da gangar jikinsa. Mace ta farko a duniya da ya so kuma yake so kece, Omar baya oye min komai nasa, hatta yadda zuciyarsa ke bugawa a kan ki ya fa a min Nayla." Nayla dai murmushi take yi cike da farin ciki amma sai ta kalli Didi ta ce, "Narma fa?." Didi tayi dariya ta ce, "bazan baki amsar Narma ba, amma daga ranar da zaman ku ya koma na farin ciki ki tambaye shi da kan ki, ki ce masa a wanne matasayi ya ajjiye Narma a kwanakin baya, na tabbatar zai fa a miki." Nayla ta yi murmushi Jidda ta ce, "samun soyayyar irin su Omar abu ne mai wahala Nayla, komai yana fa a daga zuciyarsa babu arya balle ya fa a dan ya burge ki. Nayla ki bar hutun nan haka ki koma, kina sonsa yana sonki me za a jira kuma?." Salma ta ce, "aji take so ta ja masa, da alama shi kuma tsinka ajin zai yi." Didi tayi dariya ta ce, "ban ga laifin ki ba Nayla, ki tsaya ki yi tunani zama da Omar wallahi sai ka shirya. Halinsa yana na babu inda yaje, sai kun zauna zaki fahimci abinda baki ma san dashi ba. Dan haka ki nutsu, in zaki iya da zafin ransa bismillah, in baza ki iya ba ki kama kan ki ki ja gefe. Abu aya na sani kawai, Omar yana sonki." Salma ta ce, "Didi ya ki ke zugata ne?." "Ba zuga ba ce ba Salma, gaskiya ce. Omar ya wuce duk tunanin ku zama dashi sai da ha uri." Nayla tayi murmushi ita dai bata ce komai ba amma hirarsa da ake yi ma da i take ji. Sai magriba sannan suka wuce gidan Mama. Suna shiga falon suka tarar da Mama a zaune da alama su take jira. Suna shiga ta ce, "Jidda kina da yarinya arama ki ta biye musu kuna yawo ko?." Jidda ta ce, "yanzu zan wuce Mama, motata zan auka." Mama ta ce, "Daga bara mu je saloon mu dawo sai yanzu magriba ko?." Salma ta ce, "mun an shiga siyayya ne daga nan sai muka shiga gidan Didi." "Ai ya yi kyau. To Abba ya gan ku, ya kira ni yana ta fa a, yana cewa Nayla na da aure ina bari tana yawo. Dan haka umarni ne ba shawara ba, gobe ta shirya ta koma gidan mijinta in ba haka ba da ni da ku duk ran mu sai ya aci." Salma ta ce, "gobe kuma Mama?." Mama ta ce, "ni na aike ku tafiya yawon? Zan kira wacce zata yi mata unshi gobe da safe, sannan zan aika aje a gyara gidan da daddare sai ta koma" ta fa a tana bar musu wajan. Jidda ta ce, "gashi gobe bana nan zamu fita da Baby." Salma ta ce, "Tunda Abba ne ya ce kuwa sai ta koma goben, dama dai Daddy ne zai iya sakkowa, amma Abba babu wasa. Ki je zamu yi waya" Suka shiga ciki ita da Nayla ita kuma Jiddq ta fita. Kamar yadda Abba ya ce hakan ce ta da faru, washe gari mai lalle ta zo da safe aka yiwa Nayla afa da hannu amma na saman fata, bata cika son wanda ake yi a tafin afa da hannu ba ta fi son ba i ko ja amma na kan fata. Da wuri aka gama yi mata, daga gidan Hajja aka aika aka je gyara gidan. Da yake da Salma duk wani abu da suka siyo Salma ta saka, daman frames ne da babu a gidan suka siya suka kafa, sai wanda ta ajjiye mata a aki dan bata san inda