Sashe 5
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani wajan daban, sai an lalla a shi ma sannan zai iya zuwa gidan. Meye amfanin ma son da take yi masa oho, gashi duk wannan abubuwan da suke faruwa bata jinta daina sonsa, sai dai wani lokaci tashin hankali ya kansa ta ji komai ya fita daga ranta amma da ta nutsu soyayya sa zata motsa. Nayla ki samu ki yi bacci, ko zaki ci abinci?. Nayla ta girgiza kai alamun a a kana ta ce, oshe nake Salma, bacci nake so yazo ya i zuwa gaba aya. Salma ta ce, zai zo in sha Allah. Wutar solar ce a gidan nan ko nepa?. Nayla bata amsa ba ita kuma fita dan ta duba. Tunani kala-kala Nayla tayi shi kafin bacci ya auketa saboda kanta da ya yi mugun nauyi bata san lokacin da tayi bacci ba. Washe gari bata farka ba sai sha biyu na rana, ta bu e ido ta ganta a sabon gida ba gidansu ko gidan Hajja ba. Ajiyar zuciya tayi ta mi e zaune a lokacin Salma ta shigo ta ce, Mrs Omar kin tashi? Ga ruwan wanka can mai zafi na juye miki a boket sai ki je ki yi wanka. Kin san gidan babu water heater, babu bathtub, babu shower glass sai dai bokitin. Kuma Mama ta yi ari har bokiti an ajjiye miki a ciki. Nayla ta kalle ta itama ita take kallo, Salma ta ce, ki tashi ki yi wanka zaki fi jin da i, kayan ki na saka miki a wardrobe in an kawo sauran daga Kaduna sai ki arasa sakawa dan wannan basu da yawa gaskiya. Akwai Sabon brush da toothpaste suna ciki duk na ajjiye miki. Kai ta girgiza ta mi e tsaye ta saka slippers in da yake bakin toilet in akan doormate ta shiga. Sabo da irin toilet in gidansu masu shegen girma sai ta ga wannan arami, duk da bashi da anta, yana da girma amma a idonta arami ne sosai. Har towels da bathrobes akwai a ciki, ga washing machine babba a gefe, an yi aramin bathroom cabinet me kyau a gefe an jera mata towels, bathrobes, showerl gels, soaps, shampoos da sauran kayan ban aki. Harda aramar hand dryer a ajjjiye a gefe. Abin ya bata mamaki ganin shower gel in da take wanka dashi a ban akin, bata tsaya godon tunani ba tayi wanka tare da alwala ta fito. Lokacin Salma ta sake shigowa akin Nayla ta kalle ta ta ce, Salma na ga shower gel ina, waye ya siyo?. Salma ta ce, ni ce na shiga sahad kafin ki tashi, bana so ki nemi komai ki rasa har ki ji babu da i a zuciyarki shiyasa na siyo komai na amfani. Har pad na siyo miki na ajjiye saboda ko amfaninta zai tashi kusa. Murmushi Nayla ta yi ta ce, na gode masoyiya. Murmushi itama tayi ta ce, bathroom in naki mai kyau wallahi, ya burge ni, kin san ina son bathroom mai komai fari. Matsalar kawai babu water heater, amma akwwi tank ina jin gidan akwai borhal, in kika kunna shower ruwan sanyi ne zai antayo. Nayla bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Salma ta ce, Yanzu dai ki shirya ki yi sallah ga abinci. ta furta a ta aice tare da zama tana kallon akin. Kai da ganin furniture akin ka san masu tsada ne, sai aukar ido suke yi kasancewar su sababbi. akin yana da madaidaicin girma dan ya cinye komai kuma bai matse ba ya yi yadda ake so, ga kuma center carpet a tsakiyar akin a ora aramin table a kai wanda aka yi masa ado a kai. Daga can arshen akin akwai aramar cousion guda aya wacce take kusa da carpet in da aka ajjiye. Ga cabinet na ajjiye takalmi da jaka a gefe. Duk ta san tsarin Mama ne wanann, amma tayi matu ar mamaki da aka iya tsara komai a cikin kwana biyu kamar an jima ana shiryawa hakan. Wardrobe in ta kalla ta ganta a gefe mai aton mudubi a jikinta. Saman akin ta kalla ta ga fanka ce gata nan tana ta aiki har lokacin bata auke ba. Salma da take tsaye tana kallonta ta ce, gidanki ya yi kyau ma sha Allah, ki gama sai mu fita har gate ki gani. Mai ta shafa wanda ta san shima Salma ce ta siyo ta shirya cikin atampa inkin da saba ko yauahe, ko bubu ko Tbubu ko kuma Ashape. Ashape ce wannan ta yi mata kyau duk da bata cikin walwala ko ka an. Sabon hijjab ta gani sai ta kalli Salma ta ce, ke wai har nawa ki ka kashe a wannan siyayyar? Naga sabon hijjab. Salma tayi dariya ta ce, Ga sabuwar sallaya nan ma, ki yi sallah ki zo mu je falo ki ci abinci. Amsawa tayi ta tashi tayi sallah ta idar sannan suka fita falon. Sai yanzu take kallon falon, shima ya yi kyau cikin kujeru milk da adon golden a jikin su, labulayen ma milk colour ne. Hatta dining table in irin kujerun falon ne, ga turkish carpet a shinfi e komai dai ya yi kyau gwanin sha awa. Salma ta kawo mata tea da ta dafa ta ajjiye ta ce, sauran abincin daga gidan Hajja aka kawo, gashi nan sai ki ci ta fa a tana ajjiye mata ita kuma har lokacin kallon falon take yi. Salma ta ce, falon ya yi kyau sosai Nayla, gashi babba ma sha Allah. aramin nan na ciki wanda muka zauna jiya shima yayi kyau amma wannan yafi kyau. Naga daga wajen ofar falon harda public toilet. Yanzu kenan wannan shine akin Omar Ta fa a tana nuna wata ofa da take hanyar da zata kai ka aramin falon. Sai da gaban Nayla ya fa i jin ta ce akin Omar, kafin tayi magana Salma tami e ta ce, bara na shiga na gani, dan wata ila iya yau in nake dashi, gwara na shiga na gani kafin ya fara kwana a ciki ta fa a tana wucewa. Ita kanta Nayla sai ta ji tana so ta ga ya akin ya ke amma bata motsa ba. Ganin fitowar Salma ta yi tana cewa, Nayla ai har yafi wanda muka kwana a cikin girma, kuma shi funiture in ciki irin komai na wannan falon nan ne, kenan set aya ne da kayan falon. Toilet in ma yafi naki girma, kuma naga harda water heater a ciki, akwai shower glass sannan shima da washing machine. Su Omar an samu banza ta fa a tana ar dariya tana kallon Nayla. Nayla dai bata yi magana ba, amma tana tunanin kenan dai gidan two falo ne kuma two bedrooms. aya bedroom in a falon farko aya kuma a falo na biyu. Tea in ta shanye tas, Salma ta bata magani ta sha ta zauna tana ta jan ta da hira wai dan ta sake. Buga gate in ake yi hakan ya saka Salma fita dan ta bu e, tare suka dawo da Jidda ta shigo tana cewa, Gaskiya ne, wannan khamshi haka? Lallai gidan amarya ne wannan ta fa a da fara a tana arasowa. Nayla ta kalle ta ta ce, Twiny baza ki daina yawo ba ko? Kina ta wahalar mana da Babyn mu. Jidda ta zauna ta ce, Shima ya san na yi busy ai. Ya jiki?. na samu sau i sosai, ko ciwon kan babu. Har na ji da i wallahi, daman da ke na kwana a raina. Salma gidan nan fa ya yi kyau wallahi, na lura kuma har da solar ko? Ta fa a tana kallon Salma. Salma ta ce, solar ce, kuma har fridge za a iya ora mata. Yanzu nake maganar gidan nima, na ce wallahi ya yi kyau daidai zaman mutum aya. Amma na so three bedrooms ne ba two ba, two ya yi ka an ai. To ita da waye? Daga ita sai shinfa. Jidda ta kalli Nayla da bata ce komai ba ta ce, ga kayan kitchen in ki can na kawo miki suna mota, na gaji da ajiya, yau Allah ya yi zan kawo miki kayan ki. Ta kalli Salma ta ce, Lokacin bikina da muka je siyayya duk abinda ya yi mata sai ta auka ta ce ta siya na ajjiye mata. Haka ta saka ni ajiyar kaya kamar yar cirani, yanzu gasu can a mota na kawo mata, lokacin amfanin su ya yi. Nayla ta an yi murmushi kawai amma bata ce komai ba. Jidda kallon Nayla tayi cikin tausayi, in ban da ikon Allah gida mai falo biyu da bedrooms biyu ai Nayla ta fi arfinsa, irin sa Abiy yake bawa ma aikatan gidan sa in zasu yi wani, wani ma yafi wanda take ciki kyau da girma. Da Allah ya tashi ikonsa sai ga Nayla a gida irin wannan, ko a mafarki ta san bata yi tunanin hakan zai faru ba. Lokacin da aka kai Jidda gidanta Nayla cewa tayi ita gidan yayi mata ka an, duk da sama da asa ne babban gida iya ganinka amma Nayla tace ita nata sai ya ninka haka. Da yake baka canjawa kanka addara ga inda Allah ya kawo Nayla matsayin gidan aure. Salma ce ta mi e jin ana sake buga gidan ta fita, jim ka an suka dawo Mama da Jalila da kuma Jalil harda Jawad. Nayla ganin su ya saka ta mi e da sauri ta arasa jikin Mama ta rungumeta. Mama tana murmushi ta ce, Kar dai ki yi min kuka amarya. Nayla ta fara goge ido ta kalli Jawad da yake kallonta yana murmushi ta ce, Ya J sannu da zuwa. Yauwa Nayla amarya ya fa a da tsokana yana kallonta. Zama suka yi duk aka gaisa, Mama ta kalli Nayla da take hawaye ta ce, da na san kuka zaki yi Allah da bamu zo ba. Nayla ta goge ido bata ce komai ba. Jawad ya kalle ta ya ce, Inyee amarya, wannan gida mai kyau haka. Murmushi tayi ka an ya sake cewa, kar ki damu ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce ya zama tarihi in sha Allah. Ni a zuciyata ma ji nake na amince da wannan auren naki, dan ina so ki saka ni a tsagin masu