← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 205

Sashe 158

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ya juyo yana kallin ofar midwife ta shigo da sallama ta ce, "Sannu Maman Baby." Nayla ta goge idanunta ta ce, "Yauwa sister" "Ya jikin na ki?." "Da sau "Me ki ke ji yanzu?." "Ciwon kai." Ta ce, "zan ga bp inki." Omar ya bata waje ta auna bp Nayla sannan ta ce, "Bp ki ya hau shine silar ciwon kan, anya baccin nan ya ishe ki?." Nayla ta ce, "nayi bacci iya yadda zan iya." "Okay ya kamata ki sake yin bacci kam, yanzu ki ci abinci zuwa anjima sai ki kwanta ki huta. Zan fa awa Dr abinda yace zan sanar dake." Nayla ta aga kai ta fita ya dawo kusa da ita ya ri e hannunta. Nayla ta kalle shi a raunane ta ce, "Wai jinina ya i sauka." Ya kalle ta yana shafa fuskarta a hankali, cikin son kwantar mata da hankali ya ce, "zai sauka in sha Allah." Shiru tayi bata ce komai ba, ya ago fuskarta yana kallon idanunta, ya ri e fuskarta da hannayensa, ta an lumshe ido ta ce, "Rouhi hannunka sanyi" ta fa a tana ri e hannun nasa tana shafa shi a fuskarta. Peckimg inta ya yi a goshi yana kallon idanunta da suka yi kama da na marasa lafiya. Ya gyara mata hular kanta ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, zai sauka." Ta aga kai alamun to, ya sake pecking inta a kumatu yana kallon ta. Tashi ya yi ya jawo gadon babyn ya kalli Nayla da take kallon Babyn ya ce, "Kin ga kyautar da Allah ya yi mana ko Ashiq?." Nayla a raunane ta ce, "A lokacin da baby take gab da fitowa daga jikina, na rasa hankalina Rouhi, ina jin kamar na mutu kamar ina da rai, na kasa gane a raye nake ko kuma a mace. Ciwon haihuwa ciwo ne wanda duk mai kwatance bazai iya kwatanta shi ba Rouhi" ta ora hannunta akan fuskar babyn ta ce, "Amma lokacin da ta fito aka zaro ta aka ora min ita a irjina, sai na ji wani farin ciki, na ji soyayyarta na mamaye ko ina na jikina. Rouhi ba a banza uwa take son abinda ta haifa ba, ita ka ai ta san ta yadda ta same shi. Wallahi na daina ganin laifin son da mahaifiya take yiwa anta, ko bata yi niyar nuna soyayyar ba sai ta nuna" ta fa a hawaye na gangaro mata tunawa da mahaifiyarta. Ta dawo da hannunta fuskarsa tana shafawa a hankali ta ce, "Nayla ce ta haihu yau YaMar, ina ganin abin kamar a mafarki, gani nake kamar zan farka na ganni a gidan Abiyna. Ina ma mahifaiyata tana da rai da na ninka biyayyar da nake yi mata sau babu adadi, domin yau na ana abinda ta ji a lokacin da ta haife ni." Hannunta da yake fuskarsa ya ri e ya sumbaci hannun, ya shafa fuskarta yana share mata hawaye ya ce, "Allah ya ji ansu yasa suna aljanna." "Amin Rouhi, amin ya rabbi." "Ki gode Allah da ya yi nufin kina daga cikin wanda ya yiwa ni'imar haihuwa Ashiq, ki gode masa." Nayla ta ce, "Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!!." Murmushi ya yi ya ce, "Na rasa da wacce kalma zan yi amfani na nuna miki farin cikin da nake ciki a yanzu. Kallo aya na yiwa armu soyayyarta ta gama mamaye ko ina a zuciyata, nima ji nake kamar a mafarki wai ni Omar ne yau nake da ar da dole a gaban sunanta a saka Omar. Abin mamaki yake bani, amma in na tuna ikon Allah sai na ji sanyi a zuciyata. Tunda Allah ya bani ke nake ganin canji da yawa a cikin rayuwata, yau ni kika haifawa wannan kyakykyawar yarinya a matsayin ata. Na gode Ashiq!." Murmushi tayi ta shafa kansa, ta lumshe ido ta bu e taga ita dai yake kallo ta ce, "Ni ai ko ban ce ba ka san ina sonka, na kusa mutuwa saboda haihuwar arka" ta fa a tana mayar da fuskarta kalar tausayi. Dariya suka yi a hankali shida ita ya kalli Babyn ya ce, "ina so na auke ta ina tsoron kar ta fa i." Nayla ta mi a hannu ta aukota ta ri eta a irjinta tana kallon ta kafin ta kalle shi ta sake kallon ta ta ce, "Tabarakallah ma sha Allah! ar tamu ta auko suffar kamannin mahaifinta, gata nan kyakykyawa kamar babanta. Allah ya sa kar kamanninta su canja, so nake ta zauna da kamannin YaMar ina." Ya yi murmushin farin cikin da yake ji yama ratsa zuciyarsa. "Assalamu alaikum!" Aka fa a daga bakin ofa suka amsa aka shigo. Dr ne ya shigo ya araso ciki ya mi awa Omar hannu suka gaisa ya ce, "An samu aruwa, Allah ya raya." Ya amsa da amin ya kalli Nayla ya ce, "Madam ya jiki? Nurse ta ce har yanzu bp ki bai sauka ba, da alama a asibiti zaki yi bikin sallah." Nayla ta ce, "Kaina na ciwo har yanzu." "Saboda jinin naki da bai sauka ba ne, hutu ya kamata ki samu ban da hayaniya, ki yi bacci sosai." Nayla ta ce, "To." "Amma akwai maganin da za a baki shima zai taimaka miki in sha Allah, sannan ki ci abinci mai arin jini." "Na gode" ta furta tana kallon arta. Daga nan ya fita daga akin. Omar ya ce, "Na sanar da Abiy, amma bani da number Mama da na fa a mata" ya fa a yana kallon ta tunawa da kalamanta na kwanakin baya. Nayla bata kalle shi ba ta ce, "bani wayar na kirata." Nayla ta kar i wayarsa ta saka number Mama Sa'adatu ta sanar da ita. Ta saka number Twiny dan ta haddace ta fa a mata, Salma kuwa ta san tunda Abiy ya sani zai fa awa Jawad, Jawad kuma zai fa a mata. Nayla ta kalle shi bayan ta gama wayar ta ce, "Ka kuwa sha ruwa? Na ji ana zancen gobe sallah." Ya kalle ta ya ce, "na sha ruwa mana Ashiq, amma bayan shi na kasa cin komai." Ta kalle shi a an firgice ta ce, "baka ci abinci ba? Rouhi azumi fa ka yi." Ya zuba mata idanu yana yawo da wayar idanunsa a kanta ya ce, "Kina kwance zan iya cin wani abu? Wallahi na manta azumi nake yi sai da naga ana ta shan ruwa sannan na tuna ashe na yi azumi. Bani da nutsuwa Ashiq, sai da ki ka farka sannan hankalina ya kwanta." Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "to yanzu ka je ka ci abinci." "A Ina?." Sai ta kalle shi ta yi ajiyar zuciya tunawa da bashi da kowa tunda Didi bata nan, Nayla ta ce, "to tea ka ha a mana ai ka iya, don Allah kar ka zauna da yunwa ka ga babu lallai mu tafi gida yau tunda sun ce bp na bai sauka ba." Omar ya yi ajiyar zuciya yana kallon ta ko kifta ido baya yi amma bai ce komai ba. "Rouhii." "Ashiq." "Ka je ka ci abinci, ni na samu sau "Zan ci, amma sai kin nutsu yanzu ki ka gama kuka fa." "Ai na daina, kuma na tabbatar yanzu Mama zata zo." "To ki jira ta zo sai na je, bani Yayata na auketa" ya fa a yana mi a mata hannu alamun ta bashi babyn. Bashi ita ta yi ya ri eta yana kallon fuskar yarinyar, zuciyarsa sai ta karye ya ji rauni yana mamaye sa, sai ya ji ina ma shima mahaifiyarsa tana da rai, da yau ta ga abinda Omar inta ya haifa da zata yi farin ciki sosai. Ajiyar zuciya ta ga ya yi ya kalle ta ya ce, "Da wanne suna zaki kirata? Ko Aisha inta zaki ce?." Ta girgiza kai ta ce, "Sunan Didin zan fa a kai tsaye babu girmamawa? A'a bazan iya ba. Zan kirata da Musliha." aga gira sama ya ce, "Meye kuma Musliha? Bazan yarda a sakawa ata sunan wata dabbar ba." Murmushi ta yi ta kalle shi ta ce, "ba sunan dabba bane Rouhi. Musliha yana nufin Righteous, good doer, reformer. Sunan larabawa ne irin ku." Ta e baki ya yi ya ce, "Ni dai Didi zan ce, babu wani Musliha da zan ce." Ta yi murmushi ka an kawai bata ce komai ba dan kanta nauyi yake mata. Ganin ta yi shiru sai ya kalle ta ya ga ta an kawar da kai gefe ya ce, "Ashiq ya dai?." Nayla ta kalle shi kamar zata yi kuka ta ce, "kaina ne ya yi nauyi sosai Rouhi, har bana son motsawa." "Subahanallah! To sun ce ki ci abinci ai, kuma baki ci ba, auketa a hannuna na samo miki abinci...Ko kuma barta bara na ajjiye ta da kaina, ki yi addu'a kar na yar miki da ita." Murmushi ta yi kawai bata ce komai, ya ajjiye ta akan gadon ya kalle ta ya ce, "itama yunwa take ji Ashiq." Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba. Matsowa ya yi ya dafa kanta, cikin tausayawa ya ce, "Sannu Jidda, bara na samo miki abinda zaki ci." Zai motsa ta ri e hannunsa ta ce, "ina zaka je? Kaima baka ci komai ba." "Kin fi ni bu atar cin abincin Jidda, haihuwa ki ka yi fa." "Kaima azumi ka yi, gwara ni daman tun safe bana azumin, na kuma ci abinci, amma kai fa?." "Sai kin samu lafiya zan nutsu Jidda, ki bari na samo miki, na san baza su rasa entry a wajan nan ba, Ina zuwa." Ta sake ri e shi tana langwa ewa ta ce, "A'a Rouhi, in ka siyo ka fara ci ka ji?." Saboda ya katse musun nata ya saka ya ce, "To." Knocking ofar aka yi, Mama Sa'adatu da Ummimi suka bu ofar suka shigo. Nayla ta yi murmushi tana kallon su, Mama ta araso ta dafata ta ce, "Sannu Nayla, shine baki fa a mana ba?" Sai ta kalli Omar da yake tsaye ta ce, "Omar yanzu Nayla tana nan har haihu babu labari?." Murmushi ya yi ka an, cikin rashin sabo suka gaisa ta amsa ta ce, "na auka in za a taho asibitin ni za a fa awa sai aka yi min anwaken zagaye? Yanzu
Chapter 158 · 0% Book details