← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 205

Sashe 178

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ji sosai, ka bata cerelac ko na je na bata." "Zan bata, ki kwanta ki huta. Sannu" ya furta cikin tausayi yana kallonta. Komawa ta yi ta kwanta shi kuma ya tashi zuwa kan table akin, a nan ya ga duk abinda yake bu ata da zai ha a mata kamar yadda ya saba, da kansa ya ha a mata ya zauna yana bata sai dai duk ya ata kayan jikinsa itama jikinta haka. Tana gama sha ta sha ruwa sai kuma ta fara kuka tana kiran Mummy. Nayla ta fara bacci kenan ta ji ihunta tana kiran sunanta, ya kalle ta ya ga ta bu e ido a wahale ta ce, "bani ita." "A'a Jidda, baki da lafiya ki bar ni da ita." "Bazata daina kuka ba, in tana kukan bazan iya baccin ba, ka bani ita kawai." Ajiyar zuciya ya yi ya arasa inda take ya ajjiye mata Musliha. Hannunsa ya kai wuyanta ya ta a ya ji zafi sosai ya ce, "Jidda jikinki da zafi, tashi mu je asibiti." Nayla ta ce, "zai sauka, haka yake yi min kullum, zuwa nan da magriba zai daina." "Haka zaki zauna da ciwo? Ki tashi mu je." "Bana son tashi, kaina cirewa zai yi." "To sai na auke ki." "Ka bari kawai, zai daina haka nake yi kullum." Tashi ya yi ya je ya canja kayansa ya dawo da ruwa da towel ya zauna a kusa da ita, ganin Musliha tayi bacci a kusa da ita sai ya auketa ya kwantar akan baby bed inta da yake falon, ya dawo ya mi ar da ita ya kwantar a jikinsa ya zuge zip inta rigarta ya bu e ta baya. Cire mata rigar yayi gaba aya ya ajjiye ya fara goge mata jikinta da ruwan sanyi. Ajiyar zuciya ta yi jin sanyi na ratsa ta ya shafa mata ruwan a fuska, ta kifa kanta a irjinsa tana jan numfashi da yar. Sai da ya ji zafin jikin nata ya ragu sannan ya saka hannu yana shafa bayanta a hankali cikin tsananin tausayinta. A hankali ya furta, "me zaki ci....Uhum?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "babu." "Ki tuna, me ki ke so a kawo miki?." "Kunun gya a nake so da kilishi." Omar ya ce, "bara na je na saka ayi kawo miki." Ta ri e shi a jikinta ta ce, "Kar ka tashi, ina jin sau in jikina a haka." "Zan fa awa Salima ta yi miki kunun ne, shi kuma kilishin zan saka a kawo miki." "Bana so ka tashi, ka zauna." "To Sannu, ki yi ha uri ki yafe min. Ban yi niyar saka ki a wannan yanayi ba." Bata iya magana ba ya cigaba da shafa bayanta a hankali, tausayi take bashi amma ko ka an baya ji a zuciyarsa zai iya ba da goyan baya a zubar da cikin nan. A hankali ya ji tayi bacci a jikinsa, ya yi murmushi yana kallon ta tare da kissing inta a forehead yana shafa kumatunta a hankali. "Ki yi ha uri Jidda" ya sake fa a yana shafa kanta a hankali. aukarta ya yi ya kai ta aki ya kwantar da ita ya rufeta ya rage mata ac. A falon ya zauna saboda kar Musliha ta tashi ta yi kuka ta tashe ta. Har aka yi sallar i'sha bacci take yi zuwa lokacin Musliha ta farka tana wajansa. Sai takwas ya sake shiga akin da Musliha a hannunsa, ta mi awa Nayla hannu tana kiran Mummy. Murmushi Nayla ta yi idar da sallar ta kenan ta ce, "Musliha!." Kar arta tayi ta rungume ta a jikinta tana shafa kanta ita kuma tana ta dariya. Fita ta ga ya yi bai jima ba ya dawo da tray a hannunsa ya zauna akan gadon ya ajjiye tray a tsakiya ya ce, "ga abinda ki ka ce kina so." Nayla ta kalli kunun gya ar ta yamutsa fuska ta auke kai ta ce, "ka auke, bana son hamshinsa ko ka an." Da mamaki ta ce, "ke ki ka ce kina so." "Ya fita daga raina wallahi, gwara dai kilishin, Ka fita dashi kar ya saka ni amai." Bai musa ba ya tashi ya fitar dashi falo ya dawo, ya zauna kusa da ita ya fara bata kilishin a baki tana ci. Kilishin ya yi mata da i sosai dan yana da yaji ita kuma yajin ne ke mata da Ta ci da yawa sosai, ya bata ruwa ta sha ya auke tray in daga tsakiyarsu ya ajjiye a gefe, Musliha tana tsaye a bayansa ta afe masa wuyan tana yi masa wasa. Hannun Nayla ya ri e sai ta zame ta mi e da sauri zuwa ban aki, da sauri ya bi bayanta ya ga gaba aya kilishin da ta ci ya dawo har ta hanci. Ta gigice saboda yaji, hankalinsa ya tashi ya bata ruwa ta sha ya ri ota suka dawo aki ya zaunar da ita ya ce, "Abinda ki ka ci ya dawo, zaki kuma ci?." Ta ce, "Haka nake fama, komai na ci sai ya dawo." "To ki kuma ci." "Ko na ci zai dawo." "Kuma ba ki fa a min mun je asibiti ba?." Ta kalle shi ta ce, "fushi ka ke yi dani ai, kuma ko mun je asibiti babu abinda zasu iya yi min, laulayi ne kawai." Ya ri o hannunta duka biyun kafin ya ora hannu aya akan fuskarta ya ce,"Amma lokacin Musliha ba haka ki ka yi ba, zan iya irga sau nawa na ga kin yi amai, bakya zazza i kuma bakya ciwon kai." Ta kalle shi da jajayen idanunta ta ce, "Wannan ya canja, Mama ta ce daman haka abun yake." Ya ago fuskarta da ta sunkuyar yana kallon idanunta tana karanto tausayinta da yake kan fuskarsa sosai, ta kuma san ya yi rauni duk fushin da yake yi da ita ya kau daga zuciyarsa. A hankali ya kai bakinsa goshin ta ya yi kissing ya sake ri e hannayenta ya ce, "Allah ya baki lafiya." "Amin." "Jidda!." Ta ago ido ta kalle shi ya ce, "Ki yi ha uri." Bata ce komai ba ya kuma cewa, "Kwana biyu na share ki, raina ne ya aci akan batun zubar da ciki nan amma kina raina, kema kin san bazan iya yaleki ba. Ban san haka ki ke fama da ciwo ba Jidda, da na sani da na kasance a gefenki a ko yaushe, amma ki yi ha uri!" Ya fa a a tausahse a hankali yana murza yatsun hannunta. Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ni daman wannan wahalar nake gudu shiyasa na ce zan zubar, kuma ga kula da Musliha. Bata yarda da su Salima balle su auke ta, daga ni sai kai take yarda dasu, kuma kai ba zama ka ke yi ko yaushe ba." "Shiyasa na ce ki ha uri Ashiq, tabbas kina shan wahala ga tsananin ciwo ga kula da ita, ki yafe min don Allah, ina ji kamar ban miki adalci ba. Na yi miki cikin da yake baki wahala kuma na shareki, sannan ga ata da ki ke kula da ita." ago ido tana kallonsa ya ce, "Eh duka laifina ne, da sai na san hanyar da zan bi na yi miki irin wancan cikin mara wahala." Jin abinda ya ce sai ta yi murmushi wanda bata shirya ba, ganin ta yi murmushi sai ya samu damar cigaba da yi mata wayo, ya le a fuskarta ya ce, "Da gaske nake, duk laifina ne." Ya dawo gabanta ya sauke guiwarsa a asa ya dafa guiwarta, Musliha tana daga bayanta a tsaye tana wasa da yarin kunnen Nayla. "Sai ki fa a min tun farko baki son ciki mai wahala sai a san hanyar da za a bi, duk da cikin Musliha share ni ake yi amma gwara hakan akan ace kina zama cikin wannan ciwon. Jidda bana so na ganki cikin koda yanayin acin rai ne balle ciwo, azu da na ji zafi a jikinki iris ya rage ban yi hawaye ba. Ina yi miki soyayya ta har abada, inda na san hakan zai faru da ranar da za a samun cikin nan ba a yi gaggawa ba, wata ila gaggawar ce ta kawo wannan wahalar." Murmushi ta kuma yi bata ce komai ba. Ya ce, "Amma fa na ji haushi da ki ke zancen zaki zubar min da ciki, ba ke ka ai ba har Didi da ta biye miki ko kula ta na daina yi, ban da azu da ta kira ni tun ranar bana yi mata magana. Kashe min ana fa zaki yi, kin san wahalar da na sha kafin na samar dashi kuma ki ce zaki zubar?. Raina ya baci matu a, na fara tunanin ko dai kin daina sona ne shiyasa bakya son ana?." Nayla zata yi magana ya ora hannunsa akan le enta ya an bude ido ka an ya ce, "Shiiii! ki jira na gama. Duk uzurinki akan cikin nan ban kar a ba, ko meye bai kamata ace ki furta zaki zubar dashi ba. ana ne fa, ko da sati aya da haihuwar Musliha aka sake samunsa ban yi tunanin zaki ce zaki zubar ba, wasu nema suke yi basu samu ba, Allah ya bani kuma ni sai na wula anta?. Jidda ko ba ta hanyar aure aka samu cikin nan ba banyi tunanin zaki ce zaki zubar ba, balle cikin na halak ne." Yatsansa ya auke daga kan bakinta sai ta ce, "Nifa ban ce zan zubar saboda wani dalili ba, kana ganin yadda Musliha take shan wahala saboda rashin kula da ita da bana yi. Kuma ga cikin yana bani wahala, haka nake fama da wannan ciwo duk yamma da asuba, kaima ka daina kula ni balle na samu ko sannu ka ce min na ji da i. Ga exams zan fara next week, ta ya zan iya da wannan yanayin ni ka ai?." Zai yi magana ta ce, "kar ka ce min ni na saka kaina karatu, da izininka nake yi da baka amince ba bazan yi ba. Yanzu ka ga an ce dole na yaye Musliha saboda ina da aramin ciki, kana ganin nayi mata adalci? Wata bakwai kawai a duniya ace an yayeta?. Twiny ta jima da haihuwa, amma ko
Chapter 178 · 0% Book details