Sashe 42
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ya tambaya har ya yi mata sannu. Kwanciya tayi a hankali saboda jin da in kulawarsa sai ta ji zata iya baccin ma. Ba jimawa ta sake mi ewa zaune ta sake ri e kanta cikin ciwon da yake damunta. A hankali ya mi e ya arasa ya kunna hasken akin yana kallonta, kuka take yi bilha i tana zaune ta ri e kai. Mamaki abin ya bashi, mai neman maganin ciwon kai ina shi ina kuka kuma?. A hankali ya araso inda take ya zauna a gefenta a karo na farko a zamansa da ita. Sai da yaji wani irin yarrr dan kafa arsa ta ta a ta ta ka an, ya ji wani abu kamar jan wutar lantarki kafin ya dawo daidai. Duk da ciwo yana damunta sai da ta ji wani iri a jikinta da mamaki mai matu ar yawa. "Cire hannun ki" ya furta gab da ita hakan ya saka taji maganar a kunnenta. A hankali ta sauke hannun daga goshinta shi kuma ya kai hannunsa goshinta ya ri e jiijiyoyin kan nata. Yadda suke bugawa da gudu zai baka tabbacin ba aramin ciwo kanta yake yi mata ba, sai ta sake bashi tausayi dan ya san azabar ciwon kai tunda yana yi, ga kan nata ya yi zafi. Addu'a ya fara yi mata wacce annabi Muhammad S.A.W ya koyar damu yayin jin ciwo. A online school in da yake attending aka sanar dasu addu'ar, kasancewar bata da tsaho karantawa uku ya haddaceta a kansa. Sannan ya ji sheikh Isah Ali ibrahim Pantami ya koyar da ita a wani tafsir insa wanda ake orawa a whatsapp status ko tiktok. Bai ta a gwadawa ba, amma yana ji a jikinsa in ya gwada mata zata samu lafiya. A zuciya yake karantawa hannunsa na ri e da kanta kusan mintina uku kafin ya zare hannun ya tofa a hannunsa ya shafa mata a goshin a hankali. (Za a ri e inda yake ciwo, ko ina ne yake maka ciwo zaka ri e wajan sannan ka yi Bismillah sau uku, sai ace A'uzu billahi wa udratihi min sharri ma ajidu wa uhadir. Ina neman tsari da Allah da kuma Ikonsa daga sharrin abin da nake ji (na ciwo) kuma nake jin tsoransa. Za a karanta afa bakwai. Addu'a ya ini ce, sai ka saka yarda da ya ini sannan zaga amfaninta, in ka yi don gwaji ba tare da amincewa ba bazata yi maka aiki ba.). Nayla tunda hannunsa ya sauka a goshinta ta ame am saboda gudun da zuciyarta ke yi, ta tabbatar da zai kasa kunne da kyau zai ji yadda zuciyar take bugawa dan ba bugu take na wasa ba, bugu take mai arfin da kuma sautin da take iya jiyo shi a kunnenta. Hannun Omar masoyinta akan goshinta ai dole zuciyata buga ko bata shirya ba. Bata san ya gama ba ta ji ya zare hannunsa a kasalance kamar baya son magana ya ce, "Ki kwanta, sannan ki daina kuka. Ban da shirme me neman maganin ciwon kai meye zai kai shi kuka" ya fa a yana tashi daga wajan. Nayla ta ja numfashi hamshin turarensa ta sha a lokacin da ya motsa, ta kwanta a hankali a lokacin duhu ya mamaye akin dan ya kashe hasken ya ga yana damunta. Cikin mintina da bai wuce biyar ba bacci mai da i ya auke Nayla. KRB3P021 Arewabooks@nanahaleema11. Omar yana kallon ta har baccinta yayi nisa sosai sannan ya auke kai daga kallon ta ya tashi ya dawo kan gadon dan bazai yi kwanan takura irin jiya ba. Kwanciya ya yi a can arshe itama tana arshe akwai space mai yawa a tsakiyar su. Kallon gefenta ya yi yana mamakin wai shine kwance da wata mace a kan gado aya, Allah mai iko mai yadda ya so a lokacin da ya so, in ba dan ikon Allah ba shekaru biyar masu zuwa baya kawo aure a ransa. Juya mata baya ya yi tunani kala-kala yana zuwa ransa dan shi kam ya kasa bacci. hamshin turaren ta ya dame shi, ko ya ya motsa sai ya ji shi a hancinsa. A haka shima bacci ya auke shi da yar, bai farka ba sai arfe biyu na dare ya bu e ido. Kallon inda take ya yi yaga tana yadda take amma ta juya yanzu tana kallon bayansa sa anin lokacin da ta kwanta. Sake rufe ido shima ya yi ya cigaba da bacci bai tashi ba sai asuba. Yau ma har ya yi alwala ya saka jallabiya bata motsa ba. Tunani yake ya tashe ta ko ya yaleta? Kallonta ya ke yi sai yaga ta bu e ido kai tsaye suka ha a ido da ita, ganin haka sai ya janye idonsa ya fita daga akin. A inda ya same ta bayan ya dawo tana wajan kamar jiya, ya zauna akan kujera kamar jiya bai ce mata komai ba. Nayla ta ce, "Ina Kwana." Maimakon ya amsa sai ya ce, "ya ciwon kan?." Nayla ta yi murmushin jin da i har tsakiyar ranta sannan ta ce, "ya daina ciwon gaba aya tun a jiya." Bai ce komai ba daman bata yi tunanin zai ce ba ta ce, "na gode." Nan ma bai ce komai ba sai aramin jarbinsa da ya zaro a aljihu yana ja a hankali. Nayla ta ce, "YaMar zan je asibiti anjima, sannan na wuce wajan aiki." Ya jita amma ya share bai ce komai ba, Nayla har ta fitar da ran zai amsa mata sannan taji ya ce, "Shi zuwa aikin dole ne?." Ta kalle shi jin abinda yace amma ga mamakin ta idanunsa a kulle suke kamar ba shi ne ya yi magana ba. Ta ce, "eh." Shiru ya sake yi bai ce komai ba amma yana mamakin ita da bata da lafiya aikin me zata je kuma?. Nayla ta ce, "Ka bar ni na je?." Ya bu e yana kallon ta cike da mamaki ya ce, "kin ji na ce kar ki je?." Ta girgiza kai ta ce, "A'a." "Da in zaki tafi tambaya ki ke yi?." Nayla ta bishi ido tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba ku in da yake ajjiye akan table in yake kalla. Nayla ta ce, "kaine ka ce ba sai na tambaya ba ai, Amma ka yi ha uri." Mamaki ta sake bashi jin harda bashi ha uri, kamar zai yi mata magana sai ya fasa kar ta ga ya za e da yawa a lamarinta. Tashi tsaye ya yi ya arasa wadrobe ya bu e ya auki abinda zai auka ya dawo inda yake zaune amma bai zauna ba, a lokacin Nayla ta mi e tsaye ya mi a mata ku i ta saka hannu ta kar a ya ce, "ki siyi magani." Nayla ta kalli ku in ta kalle shi har ya juya ya koma ya zauna. Nayla ta yi murmushi farin ciki, annushuwa tana mamaye mata dukkan ilahirin jikinta da zuciyarta, ta ce, "Na gode YaMar." Bai motsa ba balle ya tanka, ita kuwa da i yayi mata yawa da tana da dama da tabbas da ta taka rawa saboda farin cikin da take ji. Agogo ta kalla ta ga har shida ta yi ta ninke sallayar da tayi sallah ta ajjiye inda ta auka tana ta murmushi ita ka ai. arasawa tayi bakin gadon ta fara kokarin gyarawa dan in ta fita babu lallai ta dawo akin. Bai ce mata pim ba har ta gyara gadon tsaf ta zo zata wuce shi ta ce, "Sai anjima YaMar" ta fa a tana fita daga akin tare da ja masa ofar. _Wai YaMar, inda ta iya fa ar R in ma da sau i, amma wata kalmar take fa a daban a madadin R in. Na rasa meyasa sunan yake min da in ji a bakin ta._ abinda yake fa a a zuciyarsa kenan yana murmushi shi ka ai wanda bai san dalilinsa ba. Kawar da tunanin ya yi ya tashi ya kashe haske ya kwanta. Yau ma ya jima yana bacci sai goma ya tashi, ya yi wanka ya sake gyara akin kamar yadda ya saba ya shirya. Yau wankan maroccon yallabiya ya yi marron kala mai shegen kyau da fa i kamar kayan sarakai haka take. Fitowa ya yi falon ya yi karo da Didi a zaune tana sha tea. arasowa ya yi ya zauna ya ce, "Ina kwana." Kallon sa ta yi ta ce, "ka tashi lafiya." Bai amsa ba kamar yadda ta san bazai amsa ba daman. "Ina ta jiran ka daman, ga abinci nan ka ci." "Bana jin yunwa." Hararasa tayi ta ce, "ka ci don Allah, ai Nayla bata nan balle ka ce baza ka ci ba." "Daman na ce miki saboda ita ne bana ci?." "Baka ce ba, amma zaki fi sakewa ka ci in bata nan tunda haka ka orawa rayuwarka." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba amma yana tunanin ko ta je asibitin, ko me aka ce yana damunta, ko ya ciwon kan nata yanzu bai sani ba. Didi ta kalle shi ganin yayi shiru kamar mai damuwa ta ce, "nima gidan zan kulle, shiyasa na ce mata ta auki key dan gidan Hajja zan je, bazan sake dawowa nan ba gida zamu wuce." Omar bai ce komai ba ya sake yin shiru yana sauke numfashi Didi ta zuba masa ido ta ce, "lafiya na ganka kamar mai damuwa?." Ya ce, "lafiya" ya furta kafin ya sake kallon ta ya ce, "Shi zuwa aikin nan nata wai dole ne?." Didi ta ce, "dole ne mana, dashi ai ka aureta kuma iyayenta sun fa a maka zata cigaba da aikinta." Ta e baki ya yi bai ce komai ba, Didi ta ce, "kana da matsala da zuwa aikin na ta ne?." "Ko aya, na ga bata da lafiya ne kawai." Didi ta ce, "ta ce min zata biya asibiti daman yau." Shiru ya yi bai tanka ba Didi tana murmushi da mamakinsa, gaba aya sai ta ga ya canja, tana kuma da tabbacin ko ba ya son Nayla to yana gab da fa awa, domin alamun hakan sun bayyana a tare dashi. Maganar abinci da ta sake yi masa tana magiya ya saka shi ya sha tea kawai ya