← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 205

Sashe 66

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ba, babu abinda zai saka shi sakinta. Ya tabbatar mana da yana matu ar son Nayla." Mama Sa'adatu ta ce, "to wai me ya ha a su har ta dawo gida haka?." Daddy ya ce, "ya sanar damu komai, ya tabbatar mana zaman da suka yi na wata shida ba zama ne na mata da miji ba, ya zauna da ita ne saboda dolen da Yayarsa tayi masa ba dan yana so ba. Amma a yanzu shi ya kawo kansa yake kuma so a sake bashi Nayla a karo na biyu." Mummy ta ce, "ikon Allah, da bai san da hakan ba sai yanzu?." Daddy ya kalle su dan ya katse musun ya ce, "kuna ji, na amince da son da yake mata sosai, na kuma amince a yanzu zai ri eta hannu biyu matsayin matarsa. Abinda ya rage zamu zauna mu ji ta bakinta gobe in Allah ya nuna mana. Sa'adatu ki barta ta kwana a nan, gobe Ali da Khabir zasu zo dan a tabbatar da abinda yake zuciyarta, in zata koma masa shikenan, in bazata koma ba babu wanda yi mata dole." Mama Sa'adatu ta ce, "Gobe ya yi wuri Yaya, sati biyu tayi fa bai neme ta ba, shi kuma daga zuwa yau sai a zauna da Nayla gobe kamar daman jira mu ke yi ta koma? A sake bata lokaci ta an samu nutsuwa don Allah." "Amma kin san tana son mijinta ko?." "Na fi kowa sanin hakan, wannan kukan da take yi zai tabbatar da soyyayar da take masa." Daddy ya ce, "to ni dai na riga na ce masa gobe, bazan canja daga goben ba." Mama ta ce, "ai shikenan, amma gaskiya yayi wuri kamar daman shi muke jira" ta fa a tana ata rai. Nayla kuwa Salma ce ta shiga wajan ta ganin kukan da take yi sai ta ri ota ta ce, "Haba Nayla, wannan kukan fa? Me ya faru ki ke wannan kukan?." Nayla ta kwanta a jikin Salma tana kukan har lokacin kafin kukan ya fara raguwa a hankali tana jan numfashi. Salma ta ce, "Haba don Allah, wannan wanne irin kuka ki ke ke yi haka? Wani abu ya faru ne?." Nayla ta kalle ta ta ce, "Ya zo Salma." "Daman ai na fa a miki zai zo ko? Kuma na fa a miki in yazo ba sakin ki zai yi ba." "Salma na kasa gane a wannan yanayi nake ciki, ban san me nake ji ba a zuciyata." Salma ta ce, "farin ciki ki ke ji, na tabbatar da yanzu yana sonki bazai iya kuma rabuwa dake ba Nayla." Nayla ta ce, "bai ce min yana sona ba Salma, amma ya ce bazai iya sakina ba." Salma ta yi murmushi ta ce, "To a gidan Daddy zai za e ya nuna miki soyayya ne Nayla? Ai soyayya da auna sai kin koma gidansa, na tabbatar daga ranar zaki fara jin da in duniya. Don Allah ki bar wannan kukan, abinda mu ke so ne ya samu farin ciki ya kamata mu yi ai." Nayla ta yi murmushin jin da i ta ce, "Don Allah bakya jin hakan kamar a mafarki?." Salma ta ce, "ke addu'ar da muka yi akan hakan ta wasa ce? Ai na tabbatar da indai Omar alkhairi ne a gare ki zaman ku zai zama na soyayya da farin ciki kamar a asar larabawa. Amma fa ba daga su Daddy sun tambayarki zaki koma ba, yauwa...sai kin ja masa aji wallahi, saiya an jigatu kamar yadda ya wahalar mana da ke." Nayla tayi dariya ta kwanta a jikin Salma ta ce, "Salma na rasa me zan yi wanda zan nuna ina matu ar farin ciki. Wai shine da kansa yazo, baya oye abinda yake zuciyarsa kenan abinda ya ce min gaskiya ne?. Wallahi ban san wanne irin farin ciki nake ji ba." Salma ta goge mata hawaye ta ce, "komai zai zama labari in sha Allah, zaki fara rayuwar jin da i daga nan Abiy ya yafe miki ya tabbatar da yanzu Omar ki ka aura ba Tiger ba. Tiger ya jima da mutuwa yanzu Omar ne yake rayuwa." Nayla ta rungume Salma cikin farin ciki. Bayan sallar magriba Mama ta shigo akin da Nayla take har lokacin hira suke yi da Salma ta ce, "Nayla Daddy ya ce ki zauna a nan saboda gobe suna so zasu tambayeki ra'ayinki akan komawa gidan mijinki. Amma nima goben zan dawo ai, in zaki bi ni mu je gaba aya kawai." Nayla ta ce, "To Mama zan bi ki in." "Yauwa mu je mu tattauna, dan bazan bari daga an zauna dake gobe ki koma ba, akwai abubuwa da yawa da ba mu yi a wancan lokacin ba zamu yi yanzu. Na san kina son mijinki, wannan lokacin ki ke jira kuma gashi yazo, Daddyn ki ya tabbatar min da gaske mijinki yana sonki kuma zai gyara abinda ya ata. Baza ki koma da wuri ba sai min yi shirye-shiryen da ba mu samu mun yi wancan lokacin ba." Nayla ta yi murmushin jin da i ta kwanta a jikin Salma tana murmushi. Sai dare suka bar gidan suka tafi gidan Mama Omar kuwa tunda ya fita daga gidan yake jin zuciyarsa a matu ar damuwa, a haka ya ajjiye motar ya shiga cikin gidan ya zauna yana furzar da iska. Bai samu zarafin tunani ba aka yi kiran sallah ya tashi ya shiga masallaci. Bayan an idar ya dawo yana tuna yadda take hawaye sosai sai ya ji jikinsa gaba aya ya mutu.Tsigar jikinsa har tashi take in ya tuna yadda hawaye suke mata zarya akan idanunta. aramin tsaki ya yi kawai ya mi e ya auki key in motar ya fita ya hau motar kai tsaye ya tafi gidan Didi. Sai da ya je a hanya ya ga wani masallaci ana sallah ya tsaya ya yi sallah sannan ya arasa ofar gidan ya kira wayar Didi ya ce gashi a ofar gida. AbdulHamid ne ya fito yana cewa, "Omar kamar ba o, har yanzu wai in kazo sai ka yi waya, baza ka shiga kai tsaye ba? Gidan Yayarka ne fa." Omar ya bi bayansa yana cewa, "Gwara dai hakan." A falon ya samu Didi a zaune ya bita da kallon tausayi, gaba aya tausayi take bashi ta koma wani iri kamar ba ita ba. Ya ce, "Sannu Didi, har yanzu wai lokacin haihuwar nan bai yi ba? Duk kin canja." Didi ta ce, "da saura Omar. Zauna mana." Omar ya zauna yana kallonta ya ce, "Sannu" ya fa a cikin sanyi da nuna tsnatsar damuwarsa akan yanayinta. Gaisuwa suka yi kafin Didi ta ce, "Ya na ganka da damuwa? Ko basu amince da dawowar na ta ba?." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "A'a Didi, sun kar e ni hannu biyu fiye da yadda nake tunani, mun yi magana dasu cikin fahimta da wasa da dariya. Amma sun ce min sai an tambayeta an ji in zata koma, kamar yadda aka bani dama a wancan lokacin itama za a bata dama." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "gaskiya ne ai Omar, ya kamata a bata dama itama kam gaskiya. Amma meye na ga ka damu?." "Didi...." Sai bai arasa ba saboda damuwa, ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ita da kanta ta ce min ita bazata sake zama dani ba, ita dole sai na saketa ta gaji. Didi babban abin haushin ma kuka fa take yi, ban san ana jin zafin hawayen wani a cikin rai ba sai da naga tana kuka. A duk lokacin da na ga kina kuka ina ji a zuciyata, amma ban ta a jin irin haka, na kasa mantawa da yadda take kuka Didi, na kasa mantawa" ya fa a yana an lumshe idanunsa. AbdulHamid ya yi dariya amma bai ce komai ba. Omar ya kalle shi ya ce, "ka ce in ina bu atar shawara na neme ka, me zan yi?. Ni ban san me ake yi ba, ban iya rarrashi ba, ban iya magana da mace ba, ban iya komai ba. Duk arfina da tunanina ya are akan matarka, me zan ce mata?." AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "To ayi ha uri da muka arar maka da arfinka, amma yanzu ya kamata ka yi tunani, a duk lokacin ka ke tare da ita duk abinda ya zo zuciyarka shi zaka fa a mata." Ya nuna Didi ya ce, "Gurguwar shawarar da matarka ta bani kenan, ta ce na fa i duk abinda yazo raina amma da na fa a mata sai ta ke kuka. Me na ce mata da ya saka ta kuka? Didi me kika saka na fa a ne?" Ya arasa fa a yana kallon Didi. Didi ta yi murmushi ta ce, "babu lallai kalamanka sune suka kasa ta kuka Omar, wata ila akwai abinda ta tuna ne. Wata ila yadda ka kalle ta ka ce baka sonta shine abinda yazo zuciyarta har ya sakata kuka." "Kuma fa ko Didi...ko lokacin ata min ran da kika yi ne ya saka na ce haka, amma ko a lokacin jin abinda nake ji a kanta sosai." Didi ta yi murmushi ta ce, "ita bata ga haka a lokacin ba, dole ta ji babu da i." "Duk laifin ki ne, da baki ata min rai ba da yanzu tana gida muna zaman mu lafiya." ata maka rai ya yi amfani, ba dan haka ba da har yanzu baka tabbatar da kana sonta ba, kana nan kana zuba mata wula ancin da ka saba." Ya kalle ta ya ce, "ni bana wula anta ta, kuma ko baki ata min rai ba zuwa yanzu na fahimci mahimmacin da take dashi a rayuwata." Didi ta ta e baki ta ce, "kai dai ka sani. Ita abinda ta sani ka kalli fuskarta ka ce bana sonki, bata san wannan bayanan naka ba." "To wai ita tana sona ne? Meyasa take jin haushi dan na ce ban sonta?." Didi ta kalle shi ganin ita yake kallo ta ce, "ba lallai ai sai tana sonka ba Omar, ta kar i aurenka kuma tana kallon ka a matsayin mijinta dole ta ji babu da i in ka furta haka akanta." Ya yi aramin tsaki ya ce, "ni yanzu ku bani
Chapter 66 · 0% Book details