Sashe 135
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana haleemaa Ranar alhamis da daddare fa a suka yi da ita kaca-kaca, ya yi fushi ya yaleta dan yana ganin kawai raina masa hankali take yi da wannan sabon salon da ta auko, yana kuma ganin nuna mata da yake yi yana bu atarta shiyasa take yi masa haka, wata ila jan aji ne ko wani abun a wajanta. Dan bazai manta ba, a cikin mazan da suka zauna a China ya ji aya daga cikinsu na maganar, yana cewa mata in suka ga ana nuna ana bu atarsu ana jin da in tarayya dasu wasu suna rainawa mijin hankali, su dinga jan aji har wasu su ce sai an biya su. A lokacin bai auki abin da mahimmaci ba, kuma bai saka musu baki ba dan ba sabawa ya yi dasu ba, amma a yanzu ya ji a ransa tabbas dan yana sonta yana bu atarta ya saka take yi masa haka. Ya san baza ta yi haka dan ku i ba sai dai jan ajin, kuma zai nuna mata shi an halak ne, bazai sake sauraronta a wannan angare ba. Nayla haka ta kwana duk ta damu, tayi kuka har ta gaji amma ta kasa gane abinda yake damunta. Tana ji a ranta tana so ta samu na gaba da ita ta fa a masa ko taje asibiti, yanayin yana cutar da ita kuma yana cutar da mijinta. Da safe juma'a bai nuna mata yana fushi da ita ba, dan a wajansa komai angarensa daban, dan tana nuna masa wani hali a wancan angaren bazai shafi wani angaren na zamansu ba. Tare suka ci abinci har ya shirya ya tafi masallaci, bai jima baya dawo ya kalle ta ya ce, "Zo ki za ar min kayan da zan saka." Tare suka je ta auko masa sabuwar suit in da ya siyo, ya kalle ta ya ce, "ta yi? ni da kayan hausawa zan saka." Ta aga amsa gira duk da nauyinsa take ji sosai, ta ce, "tana yi maka kyau, ka saka ta". Bai musa ba ya mi a hannu zai kar in bashi tayi tana warwarewa alamun ita zata shirya shi. Bai hanata ba, ta shirya shi ta fesa masa turare, ya auki comb zai gyara gashin kansa ta kar a zata fara gyara masa ya zare shi daga hannunta ya ce, "ki barshi, zan yi da kaina." Sak Nayla tayi, jikinta ya sake yin sanyi dan ta san fushin jiya ne ya jawo haka, ta koma ta tsaya ya gama abinda yake yi ya kalle ta ya ce, "na yi kyau?." Murmushi ta yi ta ce, "ka yi kyau sosai." Murmushi ya yi kawai ta bi shi da kallo, in ba dan yana fushi da ita ba babu abinda zai hana bai rungumeta ba. Cikin rauni ta ce, "Ka yi ha uri Rouhii, wallahi....." dakatar da ita ya yi ta hanyar aga mata hannu, ya an daure fuska ya ce, "na ce miki kin yi min laifi ne?." Ta ce, "A'a." "To meye na bada ha urin?." Shiru ta yi bata ce komai ba. Share batun ya yi yana gyara ma allan rigarsa ya ce, "da wanne yare zan yi magana? Ni ba turanci nake ji ba, ba kuma yaren China nake ji ba." Sai ya bata dariya ta ce, "ka yi magana da yaren ka, suma ai da yaren su suke magana. In ban da nigeria ma ai ko wacce asar da ta cigaba da yaren su suke amfani." Murmushi ya yi ya ce, "ki kasance active, kin san kece transilator ina." Murmushi ta yi ta ce, "An gama." "Zan tafi" ya fa a yana kallon ta. Tare suka fito harabar gidan, da yake motar tana ofar gida sai ya kalle ta ya ce, "ki koma, ki ta yi min addu'a." "In sha Allah Rouhii, sai ka dawo." Fita ya yi ba tare da ya ri e koda hannunta ba. Nayla ta fara hawaye dan ta san fushi yake yi da ita shiyasa tun daren jiya bai sake kai hannunsa jikinta ba. Jiri ne yake aukarta ta koma falo ta zauna tana jin kanta na juyawa sosai. Ta yi shiru tana tunanin mafita, kunya take ji ta tambayi Mama Sa'adatu ko Mamanta ta Kaduna, dan maganar akwai nauyi sosai, ta ya ya zata iya ce musu da zarar mijinta ya fara ta ata da niyar aikata wani abun sai ta ji kamar zata mutu? Ta ya zata iya fa a musu wannan maganar?. Ajiyar zuciya tayi dan bazata iya ba gwara ma ta je ta ga likita kawai. Bayan ta tafi da jimawa ya kirata a waya, tana auka ya ce, "Jidda wa ki ka sani lawyer a nan Kano?." Nayla ta ce, "Yaya Muhammad, an Daddy ne." "Tura min number sa yanzu, da gagggawa." Da to ta amsa ta kashe wayar ta tura masa number ta yi shiru tana jiran tsammani. Daga nan bai sake yi mata waya ba har bayan magriba kuma bai dawo ba. Duk ta damu tana kiransa amma bai auka ba, so take ya dawo kawai ta ji ya aka are. Tana wannan tunanin ya shigo gidan da sallama, abin mamaki shida Yaya Mahmmad in ne wanda take k ira da Yaya Babba, kaf jikokin Hajja shine babba shiyasa suke ce masa Yaya Babba. Da mamaki ta ce, "Yaya Babba! Yau kai ne a a nan?." Yayi murmushi ya ce, "dole ki ganni a nan, na zo na taya ki murna." Kallon sa tayi ta kalli Omar da yake tsaye ta ce, "me ya faru?." "Zaki ji daga bakin mijinki, Ni dai ina tayaki murna Allah ya sanya alkhairi." Ya kalli Omar ya ce, "Omar zan wuce." Tare suka sake fita da Omar suka barta a wajan, duk ta ru e tana jira ya dawo. Ba jimawa ya dawo, ta matso inda yake amma sai ya yi baya yana kallonta, bata damu ba ta ce, "Rouhi me ya faru? Ka fa a min don Allah." Takardar da take aljihunsa ya mi a mata, hannu yana rawa ta bu e tana karantawa. Baki ta rufe da hannunta tana sake wara ido a takardar kafin ya ga ta zube ta yi sujjada a wajan ta ago zata shiga jikinsa ya an kauce ya ce, "baki ce Alhamdu lillah ba!." Jikinta ya yi sanyi ganin ko ta a shi ya i bata damar yi. Abin ya yi mata yawa ga damuwa ga farin ciki, haka ta daure ta ce, "Na fa a da na yi sujjadar godiya ga Allah. YaMar contract na aiki da company ka suka nema har na shekara aya fa, ai dole na ce Alhamdu lillah." Murmushi ya yi yana girgiza kai ya ce, "Kamar wasa ba, wai Omar ne zai yi aiki da babban company na asar China. Sun ga products in mu ya yi musu suna so a dinga fita dashi zuwa asar su. Ni ban san abinda zai faru ba kenan, kin san komai na su mai a'ida ne shiyasa na tambaye ki lawyer. Sai da Yayanki ya je aka saka hannu aka jima ana ta cike-cike sannan komai ya kammala." Nayla hawayen farin ciki ya sakko mata ta ce, "Allah mun gode maka, Allah ka cigaba da saka mana albarka a duk abinda muka saka a gaba." "Amin Ashiq!." Wayarta ce ta fara ara ta duba ta ga sunan Salma ta auka Salma ta ce, "Ke Nayla kinga yadda hotunan mijinki da an China suke trending? Wai ashe contract ya samu da su shine ko labari?." Nayla ta ce, "Salma yanzu abin ya faru, dawowarsa gida kenan." Salma ta ce, "Maza ki duba wayarki zaki ga abin mamaki." Katse kiran Salma ta yi tana shiga instagram da abinda ta fara karo kenan. Ta karanta caption in a bayyane tana cewa, "Mutum na farko an africa, an nigeria, bahaushe ya saka hannu a yarjejeniya tsakaninsa da asar China. Sun ulla yarjejiya akan zasu dinga kar ar products insa suna kaiwa asar China." Kallonsa ta yi ta ce, "Rouhii kaine mutum na farko a kaf africa da aka ta a bawa wannan damar, kaine na farko fa Rouhii, kaine na farko." Gangar jikinsa bu atarta jinta a jikinsa take yi, rungumeta yake so ya yi tsam-tsam tayi kukan a irjinsa amma baya son aikata hakan dan arshe shine zai kwana a ciki. Ya dake bai nuna mata ba ya ce, "Sun fa a Jidda, da ni suka fara signing wannan contract in a kaf Africa. Fatana Allah yasa mu fita kunyarsu." arar shigowar message ya ji, ya kalli wayar ya ga ku in da aka turo masa a acc ya haskawa Nayla wayar ya ce, "alert insu ya shigo." Kalla ta yi ganin yawan ku in ta wara idanu ta ce, "Numbers in sun rikice min, nawa ne?." Dariya ya yi ya ce, "ke da kike ar boko ma kenan, balle ni." "Didi ta sani?." "Yanzu zan fa a mata." "Mu je gidan tare kawai." Zai yi magana sai ga kiran Didin yana shigowa, ya yi murmushi yana auka ta ce, "Omar zo ka bu a mana ga mu mun zo." Murmushi ya yi ya ajjiye wayar ya kalle ta ya ce, "ki saka hijjab." Ba musu ta tashi ta auko shi kuma ya fita. Didi tana shigowa ta rungume Nayla, itama kuka take yi sai ta saka Nayla kuka. Omar gaisawa suke yi da AbdulHamid yana yi masa murna kafin ya kar i Marmerh da take hannunsa. Sun saba da yarinyar sosai, ta fara dariya shi kuma yana yi mata wasa cikin aunarta. Nayla daman kuka biyu take yi, ga na damuwa ga na farin ciki, Didi ta agota daga jikinta Nayla ta ce, "Nayla ina ta ya ki murna, Allah ya taya ri o ya tabbatar da alkhairi." Nayla ta ce, "Amin Didi, nima ina taya ki murna, Allah ya sa silar nasarar kenan." Ta yi murmushi ta ce, "Amin." Ta kalli Omar ta ce, "Ina ta jiran wayarka shiru, sai yanzu Yalla ai yake nuna min hotunan ka da an China a waya, ga takarda an saka hannu. Allah ya cigaba da dafa maka Omar, Allah ya cigaba da shiga lamarinka Omar." Murmushi ya yi ya ce, "Amin Didi, Duk kin ru e, ki zauna don Allah." Didi ta ce, "ba dole na ru