← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 205

Sashe 180

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban Yaya." Suka yi dariya ita da Nayla, tare suka raka Didi har mota sannan ta tafi. Bata jima da fita ba suka fita shi da Nayla. A hanyarsu ta dawowa gida ne AbdulHamid ya kira yake shaida masa Didi na asibiti, kai tsaye asibitin suka wuce suka samu AbdulHamid a tsaye Omar ya ce, "Lafiya? Me ya same ta?." AbdulHamid ya ce, "ciwon cikin nan ne dai, ta ce na sanar da kai shiyasa ma na kira ka." "Tana ina?." "Tana aki ana dubata, bara su fito sai mu shiga." Zama Nayla ta yi shi Omar kam ya kasa zama har sai da likitoci suka fito suka shiga akin. A kwance suka samu Didi tana kallon masu shigowa, tana ganin Omar ta yi murmushi yana ri e da hannun Marmerh ya araso ya ce, "Didi sannu, Meyasa azu baki ce min baki da lafiya ba?." Didi ta yi murmushi Omar ya zauna akan kujerar da take gabanta har lokacin Marmerh na kusa dashi ta ce, "Bayan na koma gida ciwon ya samu Omar." Ya ri e hannunta ya ce, "Amma da sau i ko?." Ta aga masa kai tana kallonsa da murmushi. Didi ta kalli Nayla ta ce, "Nayla sannu." "Didi ya jiki?." "Da sau i Nayla." Omar ya ri e hannunta ya ce, "Babu abinda ki ke ji?" Sai ya kalli AbudlHamid ya ce, "ko dai zamu kai ta wata asar a duba wannan ciwon cikin nata? Yana damuna wallahi." AbdulHamid ya ce, "kuma lafiya lau ta koma gida daga gidan ku, tana sallar magriba sai ta ce cikinta na ciwo shiyasa muka taho." Ya sake kallon Didi ya ce, "Sannu Didi, ya kamata a san abinda za a yi akan ciwon nan naki, zan je na samu likita mu yi magana." Didi ta yi murmushi ta ce, "Kar ka damu Omar, zan samu lafiya." Nayla ya kalla da take gefe ya ce, "Zo ki zauna da ita mu je mu dawo." Nayla ta dawo inda Omar ya tashi ta zauna. Omar ya kalli hannunnsa ganin Didin bata sake shi ba, ya kalli fuskarta ya ce, "Didi." Murmushi ta sake yi shima ya yi murmushi ya ora hannunsa aya akan hannunta ya ce, "yanzu zan dawo." A hankali ya zame hannunsa ya bar kusa da ita.Marmerh ta saka kuka tana kiran Daddy ya auke ta suka fita tare shida AbdulHamid. Nayla ta ri e hannun Didi kamar yadda ya yi ta ce, "Sannu Didi." Didi ta yi murmushi ta ce, "Marmerh tana aunar Omar, yadda take ma ale masa in ta ganshi ko babanta bata yiwa haka."Nayla ta yi murmushi ta ce, "Shima yana sonta ai." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Nayla cikin wata nawa?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Wata biyu ne kacal." "Kai! Ashe akwai sauran tafiya." "Sosai ma Didi." "Allah ya raba lafiya, ya baki ikon iya kula dasu." "Amin Didi." Didi ta ri e hannun Nayla ta ce, "in ki ka haifi namiji ki saka sunan Abiy, shine ya zama silar aurenku, In mace ki saka sunan Hajja." Nayla tayi dariya ta ce, "in an biyu ne duka mata fa?." Didi ma tayi ar dariya ta ce, "Sai ki saka sunan Hajja da sunanki, in duka maza ne ki saka sunan Abiy da sunan Omar shikenan an raba." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Allah ya kaimu." "Amin Nayla. Zafi nake ji, bakya ji?." Nayla ta kalli akin ta ga ac aiki take yi, ta kalli Didi ta ce, "Ai kam babu zafi, bara na ara miki gudun ac." "Bar shi kawai Nayla, Bacci nake ji." Nayla ta ce, "to ki kwanta mana Didi, ki yi bacci zaki fi jin da "Amma bani ruwa na sha Nayla." Nayla ta mi e ta kawo mata ruwa ta bata ta sha, Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Kamar ban sha komai ba Nayla, sake bani na sha." Nayla ta sake bata, Didi ta shanye roba aya na ruwa Nayla ta ajjiye robar. Didi ta ce, "ikon Allah, kamar ban sha komai ba, Amma bar shi kar ya ulle min ciki." Nayla ta koma ta zauna ta kuma ri e hannun Didi tana kallon ta kamar yadda take kallon ta. Didi ta ce, "Uwar gidan Omar, Allah ya bar auna har aljanna. Omar yana sonki kina sonsa, ban ta a ganin halittar da Omar yake so kamar ki ba Nayla, yana sonki kamar ya ha iyeki." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Didi ai nima dai ina son shi, kar ayi min gori. Tun yana ora min wu a a wuyana nake son shi." Didi tayi murmushi ta ce, "Ni na isa na yi miki gori Nayla? Ina fa a miki ne dan ki sake ri e min shi hannu biyu. Ki cigaba da ha uri dashi, halin Omar sai fa ha uri, ki cigaba da rarrashinsa akan danginmu Nayla" Nayla ta ce, "ki yi baccin ki Didi, in kin tashi ma cigaba da maganar." Didi ta yi murmushi ta rufe ido sai kuma ta ja numfashi ta ce, "Hasbunallahu wani'imal wakil, Astagafirullah, allamuhmma salli ala Muhammad wasalmin" ta fa a a tare tana goge gumin goshinta ta mayar da ido ta rufe. Nayla ta ce, "Sannu Didi." Ta bu e ido ta kalle ta ta yi murmushi ta ce, "nima fa ina son Omar, ba ke ka ai ki ke sonsa ba." Nayla tayi dariya bata yi magana ba, Didi ta kuma yin murmushi ta sake maimaita salatin da ta yi ta rufe ido tana sauke numfashi a hankali. Nayla na rike da hannunta kusan mintina ashirin sai ga Omar da AbdulHamid da likita sun shigo. Likita ya araso wajan Didi ya kalli Nayla ya ce, "ta yi bacci ne?." Nayla ta ce, "ta ce min bacci take ji." Likita ya kalli ruwan da yake shiga jikinta ya kalli hannun Didi, sannan ya juyo ga kallonsa kan fuskarta da idonta yake a rufe. Hannunta ya ri e na wani lokaci sannan ya ajjiye hannun, ya ora stethoscope a irjin Didi, ya kalli computer da take daidaita numfashi ya yi ajiyar zuciya. Likita ya kalli AbdulHamid da yake kallonsa, ya kalli Omar da yake arewa Marmerh chocolate, ya kalli Nayla da take danna waya har lokacin hannun Didi na cikin nata, sai Musliha da take jikin Nayla tana bacci. Likita ya sauke numfashi ya ce, "Allah ya yi mata cikawa, ta rasu!." irjin mutane uku suka buga a lokaci guda aya, AbdulHamid ya zaro ido waje cikin tsananin tashin hankali da ru ani ya ce, "Wai wacece ta rasu?." Likita ya ce, "Gata a kwance." "Haba likita, dubata da kyau mana, mintina ashirin da fitar mu tana kwance tana magana yanzu ka ce ta rasu? Ko dai bacci ta yi?." Likita ya tako ya dafa AbdulHamid ya ce, "ka yi ha uri abokina, Allah ya yi mata cikawa, ta amsa kiran mahaliccinta, ta mutu ta bar duniya." AbdulHamid ya tako da hanzari zuwa wajan Didi yana kallon ta, ya kalli likutan ya ce, "Da gaske ka ke? Ko dai ka kira wani likitan ya sake bincikawa? Ta ya za a ce ta mutu bayan yanzu muka fita muka barta tana magana?." "Ba a wasa da mutuwa, bazan fa i abinda ban tabbatar ba abokina, Allah ya yi mata cikawa sai dai ku yi ha uri." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!! Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!!!. Likita yanzu fa...." Sai ya kasa fa a saboda rauni da karyewar zuciya ya mamaye masa jikinsa. P113 Omar kam yana tsaye yam yana jin me suke cewa amma ya kasa fassara kalamansu, mutuwa ya ji suna cewa wai ta rasu, to wacece ta rasu in? Meyasa AbdulHamid yake salati haka? Meye ma mutuwar, ya ake yin ta ya kasa tunawa. Likitan ne ya zo zai gifta ta gaba Omar ya ri o shi ya ce, "Ni ban gane ba, wacece ta rasu in?." Likita ya kalli Didi ya kalle shi ya ce, "Gata nan a kwance, gawarta ku ke tare da ita amma babu ranta" ya fa a a tausashe yana kallon Omar. Omar ya kalli Didi ya sake kallon likitan ya yi masa kallon baka da hankali baka san aikinka ba, ya ja tsaki ya ce, "Amma dai baka da hankali ko?." Likita ya yi murmushi kawai bai tanka ba. Nayla da take jin kalaman da ake yi duk da fa uwar gaban da take ji haka ta daure ta ce, "Likita me ka ke cewa ne? Kalli hannunta fa har yanzu yana ri ewa da nawa, bacci fa kawai ta ce min zata yi shine zaka ce ta mutu?. Gaskiya baka san aikinka ba." Omar ya yi tsaki ya taka zuwa inda Didi take kwance yana kallon fuskarta, gabansa ya yanke ya fa i ba tare da ya san dalili ba, rauni ya fara mamaye masa zuciya ya sauke Marmerh da take kafa arsa ya ri e hannun Didi da aka zare mata ruwan ya ce, "Didi! bacci ki ke yi ko?." Nayla ta ce, "Kar ka tasheta, ta ce min bacci take ji." AbdulHamid yana gefe ya ame kamar wanda aka tsayar, ya kasa motsawa sai kallo kawai yake yi zuciyarsa na bugawa a guje hankalinsa ya kai arshe wajan tashi. Mutuwa kawai yake maimaita a zuciyarsa, ya kasa amincewa matarsa ta bar duniya, ya kasa yarda ta tafi kenan har abada, ya kasa amincewa da batun likita. Likitan da ya fita bai jima ba suka dawo da manyan likitoci guda uku, Omar ya kalle su ya ce, "ku canja wannan likitan bai san aikinsa ba. Tana bacci ya ce wai ta mutu, ko meye mutuwar ma oho." Likita ya tako ya duba Didi ya yi ajiyar zuciya ya ja mayafin da yake jikinta ya rufe mata fuska. Ya dafa Omar ya ce, "Ka yi ha uri, amma da gaske abinda ya fa a maka, ta rasu ta bar duniya." Fizge jikinsa ya yi ya ce, "Wai wannan irin shirme ku ke fa a ne haka? Wanne irin rashin hankali ne wannan da rashin sanin aiki? Matar da na fita na barta tana hira ita za ka ce min ta mutu?. Oh kaima baka san aikin na ka ba kenan ko? To zan auke ta na kaita inda aka san aiki, kuma
Chapter 180 · 0% Book details