← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 205

Sashe 56

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hankali auren da bai wuce wata shida ba ace ya lalace?." Abiy kallon ta yake yi kamar mai karantar wani abu, ta kalle shi suka ha a ido ya dau e kai ba tare da ya ce mata komai ba. Shima Jawad in shiru ya yi yana mamaki, ko meyasa Mama bata son auren Nayla ya mutu oho, tun farkon aure ita ka ai ce mai goyan bayan auren har yanzu. Ya rasa meyasa take haka, yau kaga tana goyan bayan auren, gobe ka ji tana kushewa. Mama tashi tayi ta bar wajan zuwa akinta. Hannu na rawa ta kira waya ana auka ta ce, "Ke komai yana shirin lalacewa, Aziza wai Nayla ta bar gidanta ta koma gidan anwar mahaifiyarta, kuma na san halin dangin babar nan nata, sonta suke yi kamar su iga mata rai, tsaf zasu iya kashe auren nan ban cimma burina ba. In auren nan ya mutu yanzu ribar me na samu? Bayan kyau da Naylan ta ara yi a gidan? Tunda aka fara irin wannan yajin so nake a cigaba daga nan har a tashi duniya." Aziza ta ce, "kwantar da hankalin ki Yayata kuma awata, Yanzu Ina ita Nayla in?." "Tana Kano na fa a miki." "Shikenan ki kira ta, ki karya mata zuciya da kalaman da zata sake lulawa cikin duniyar qaunarsa. Ki kashe mata zuciya, ki tayar mata da tsumin soyayyarsa. awata ki yi mata laga-laga da zuciyata, ki dasa mata raunin da zata ji tana so ta koma masa. Daga nan in ta koma ya kamata mu yi wani abun da zamu jefawa yaron tsanarta a zuciyarsa, yadda ubanta ya ce kar ta zo masa gida shi Omar in ya dinga cin ubanta kinga bata da wajan zuwa." Mama ta ce, "Aziza na san Sa'adatu farin sani, babu lallai ta bar kalamaina su yi tasiri a zuciyar Nayla." "Haba Zeenatu kamar ba ke ba? Ki gwada sai ki zo ki bani labari. Ai tunda har aka aura auren nan wallahi baza mu bari a raba shi ba, in aka raba ma kenan itace da riba ba mu ba. Duk wahalar da Bilkisu ta ba ki shikenan ta tafi a banza? Matar nan har shara da wanke-wanke ta saka ki da cikin Ahmad wata tara. Ba tausayi balle imani kuma mu sai mu bar arta ta yi walwala a gidan miji?. Ni fa na so mai mata ta aura, da ace yana da mata zuwa zamu yi mu ha a kai da uwar gidan, in ta kama mu biya uwar gidan ta dinga cin uwar Nayla yadda zata girbi abinda uwatta ta shuka." Mama ta sauke numfashi ta ce, "Aziza ina son Nayla, amma bana son Nayla tayi walwala a gidan aurenta. Yadda na assasa auren nan har aka yi bazan yale ya lalace a banza ba, zan iya yin komai dan ta koma masa." "Ki samu ta koma in, in ta koma zamu canja taku ne, domin kuwa akwai wani malamin su awata ban ta a zuwa wajansa ba amma akan wannna maganar zamu je. Za a yi aiki akan mijin nata, a sake jefa masa dabi'ar shaye-shaye da wannan fa an daban yadda zai ci uba ta da hujja." Mama ta yi dariya ta ce, "Aziza ke muguwa ce wallahi." Aziza ta ce, "Baza ki gane ba Zeenatu, uwarta ta wahalar da ke sosai, har ni da nake ar zaman aki ba yale ni tayi ba. Shegiya mai ruwan aljanu, ana cikin kabari ana girbar abinda aka shuka, an bar mu a duniya muna walwala da jin da i, ga kuma arta a duniya zata girbar mata abinda ta shuka kafin ta she a barzahu." Mama ta ce, "in na tuna lokacin da nake naku ar Ahmad tana kallona ina juyi jini yana gudu yana bin asa amma baiwar Allah nan ta auke kai ta kuma i sanar Abiy abinda yake faruwa. Ba dan Allah ya kawo ku a lokacin nan ba da yanzu Ahmad bashi da rai. Ke ba a banza Alalh ya auki ran Bilkisu ba, barinsu a duniya ma mugun iri ne wallahi. Sai bayan ta gama aikata sharrinta wai yafe mata, an i a yafe in." Aziza ta ce, "kuma a haka zamu bar arta tayi zaman aure lafiya?. Ai Allah yana so ki auki fansa ne shiyasa ya auki ranta ya bar arta a hannunki, duk abinda ta aikata miki sai gashi ta mutu ta bar aya tilo da ta mallaka a hannunki. Sai abinda ki ka ga dama zaki yi mata, kin ma yi ari da kika iya rainon Nayla wallahi." "Ina son Nayla na fa a miki, ina jinta kamar Jidda. Biyayyar da Nayla take yi min Jidda bata yi min ita wallahi, kuma na ri eta tsakani da Allah da zuciya aya, kawai burina ta girma a zo wannan ga ar, bana so ta ji da in aure ko kusa Aziza." "Zaman aure mai da i ai sai Jidda da Jalila, su ne zasu yi rayuwar aure mai kyau da farin ciki amma ba Nayla ba. Yanzu ki kira ta ki yi mata laga-laga daga nan sai ki bani labari." Sallama suka yi Mama ta kashe wayar ta kira number Nayla kai tsaye. KRB3P030 Arewabooks@nanahaleema11. Nayla tana zaune ita da Mama Sa'adatu da Salma da Yaya Zahra kiran Mama ya shigo wayarta. Kallon wayar tayi kamar bazata auka ba sai ta auka, da yake wayar na nesa da ita sai ta saka a speaker ta ce, "Mama Ina yini." Mama ta ce, "Nayla kina lafiya? Ya na ji muryarki haka?." Nayla ta ce, "kaina ne yake ciwo Mama, Ina Jalila? Yaushe Twiny zata dawo?." Maa ta ce, "Nayla ba wannan ba. Yanzu Abiy yake fa a min abinda ya faru, da gaske kin bar gidanki Nayla?." Nayla ta ce, "eh mama." "To akan me Nayla? Me ya faru, meyasa baki fa a min ba?. Ba na ce duk abinda ya faru ki dinga sanar dani ba?." "Mama ni kawai na bar auren ne." "Akan me zaki bar auren bayan kina son mijinki? Ko dai zuga ki ake yi akan ki kashe aurenki?." Nayla ta ce, "A'a Mama, da kaina na gaji kawai." Mama ta ce, "to ki fa a min abinda yake yi miki mana har kika gaji in, dukanki yake yi?." A gajiye Nayla ta ce, "ni bai ta a dukana ba" ta fa a kamar zata yi kuka. Mama ta ce, "kin ji ko, ni na san kina son mijinki gashi nan muryarki har ta fara yin rawa. Nayla kar ki sake auren nan ya mutu, in ki ka bari hakan ya faru kin rasa masoyinki wanda ki ke so na har abada. Omar shine wanda ki ke so, shine wanda ki ke qaunar zama dashi a matsayin mijinki, na auka zaki jure duk abalalen da zaki fuskanta a gidansa ki rike aurenki amma tun ba a je ko ina ba kin fara barin gida?. Haba Nayla, meyasa baki yi min waya kafin ki bar gidan ba?." Hawaye ya sakowa Nayla ta ce, "Mama ni kawai...." Mama ta katse ta ce, "na fa a miki ha iri zaki yi ki jure ko me yake miki, Nayla ko da dukanki yake yi jurewa zaki yi saboda kina sonsa. In auren nan ya mutu ai sai Abiy ya yi mana dariya, tun farko kin san baya so ya yi ha uri ne dan ke, in kuma Omar ya sake ki zai ce daman ai ya fa a miki kika i ji. In ki ka yi ha uri a hankali komai zai wuce, da zarar kin fara jin da in auren shikenan zaki yi rayuwarki cikin farin ciki. Amma barin gida ki tafi yaji wannan ba abi'a mai kyau bace, tunda nake da Ummanki bata ta a yaji ba nima kuma haka, a ina ki ka gado wannan hali Nayla?." Nayla tayi shiru bata ce komai ba dan bata san me zata ce ba. Mama ta ce, "abinda nake so da ke ki koma gidan mijinki kawai, in akwai abinda ki ke so ki fa a min sai na aiko miki dashi." Nayla ta ce, "babu abinda nake so." Nayla taji Mama Sa'adatu ta ata, ta kalleta taga tana yi mata alamar da ta yanke wayar, sai ta ce, "Mama kaina ciwo yake yi zan kwanta." "To ki kwanta, gobe zan kira ki da safe ki tabbatar da kin koma kin ji?." "To Mama" ta fa a tana yanke wayar ta ajjiye a gefe. Yaya Zahra ta ce, "kan bala'i! Me matar nan take nufi ne wai?." Salma ta ce, "Nayla ki yi ha uri, Mama babarki ce, amma wallahi Yaya Zahra tun lokacin auren nan na lura kamar da saka hannun Maman su Jidda akan abinda ya faru, to bazan ce komai ba tunda uwa take a wajan Nayla, ga kuma yadda mu ke da Jidda. Amma wallahi tana da hannu a lamarin nan." Calmly Nayla ta ce, "Kai Salma, kawai tana bani goyan baya ne tun a lokacin amma ba dan wani abun ba." Mama ta kalli Nayla ta ce, "Daman duk abinda ya faru tambayarki take yi?." Nayla ta ce, "e h amma ba ko yaushe ba, tana tambayar lafiyar da nake ciki ne kawai, ni kuma in da damuwa sai na fa a mata." Mama ta ce, "ba laifi bane dan kin fa a mata damuwarki ba Nayla, Zeenatu uwa take a waja ki tunda ita ta raineki. Amma meyasa take so ki zauna a gidan Omar? Meyasa bata tambayi ra'ayinki ba?." Nayla ta ce, "Tun farko Mama ta san abinda yake zuciayata, ta ta a ji muna hirar nida Salma da Jidda. Itace take bani warin guiwa akan zan iya aurensa. Hatta lokacin da Abiy ya tambaye ni Mama ce ta saka na ce amsa masa da gaske ne Ina sonsa, sannan itace ta turo ni Kano a lokacin da Abiy ya yi fushi. Kawai tana supporting abinda nake so ne ba wani abun ba, ta na kuma guje min fa an Abiy shiyasa take yin abinda take yi ba dan ta cutar da ni ba. Mama tana sona sosai, tana yi min abinda ko Jidda bata yiwa." Mama ta ce, "daman mun san tana sonki Nayla, waye zai ce babarki bata sonki?. A yanayin yadda take
Chapter 56 · 0% Book details