Sashe 140
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gaggauce ya shiga saboda bai yi sallar la'asar ba ga magriba ta gabato, kai tsaye ya shiga aki da niyar yin alwala amma sai ya tsaya yana kallon akin. Decor aka yi masa mai matu ar kyau da aukar hankali, an rubuta welcome back Rouhi da flowers masu kyau da hamshi. Murmushi ya yi ya kalli table in da yake akin ya ga harda cake ya girgiza kai ya ce, "ko kina ina? Na ga cake ban ganta ba." A hankali ta fito daga bayan labule ya bita da kallon urilla ganin ta canja masa gaba aya, ta sake haske ga wata cikar jiki da ta sake yi na musamman. Nayla ta tako tana murmushi tana kallonsa. Murya a raunane ya ce, "rowar ganin ki ki ke yi min in na dawo ko? Wancan lokacin ma uya ki ka yi." "Sannu da dawowa Rouhii!" Ta fa a tana shiga jikinsa ya sanya hannu ya rufe ta a jikinsa ya yi ajiyar zuciya mai arfi kana ya ce, "Don Allah indan kina yi min addu'a akan Allah ya sa na ara sonki ki daina, Ashiq son da nake miki yana neman fin arfin tunanina. Kullum soyayyar ki aruwa take a zuciyata, shiyasa nake neman alfarma in kina addu'a ki daina kar ta zauce" ya furta a hankali yana ri e da ita a jikinsa ita kuma tana hasahen yanayin da zai kasance in ya san tana da ciki. "Rouhi I missed you." "Likewise Ashiq." Bata ago ta kalle shi kamar ko yaushe ba, amma yana bata mamaki in ta fa i abu ya bata amsa bayan ya ce shi bai iya ba, gashi in zata kwana tana tambaya akai bazai bata amsa ba. Sun jima a haka kafin ya ago ta ya yi mata peck a goshi ya ce, "ban yi sallar la'asar ba Ashiq." "Na ha a maka ruwa yana nan yana jiranka." "Na gode Masoyiya" Abinda ya ce kenan ya shiga bai saurare ta sai ta taya shi ba saboda sallah. Tana zaune a falo ya fito dan lokacin har an yi magrib, ya zauna a kusa da ita ya kalle ta ya ce, "Ni na ga kin rame, rashin lafiyar da ki ka yi ne ya jawo haka?" Ya fa a yana saka hannunsa a wuyanta yana shafa ashin da ya gani. Nayla ta kalle ta shi tana ganin kamar ana canja mata shi, ya ara haske sosai fuskarsa ta canja ya yi wani irin kyau mai aukar hankali. A hankali ta ce, "Mijina baya nan ba dole na rame ba? Ni wai wannan kyaun da ka ke arawa na meye?." Yana kallon ta ya ce, "Na kewar ki ne." "Shine zai ka ara kyau kuma?" Ta fa a tana kallonsa da shagwa "Eh mana, tunda bakya ganina ai dole ki ga na yi kyau. Ina tambayar ki baki bani amsa, ya naga kin rame?." Nayla ta ce, "Tunanin ka ne wallahi." Ya zuba mata ido bayan ya ri o hannunta ya ce, "Tunani ki ka saka har haka Jidda?." "Ni ka ai na san yadda na yi kewarka Rouhi" ta fa a tana kwanciya a jikinsa ya ce, "Bana tunanin kina jin abinda nake ji." Zame jikinta tayi ta ce, "abinci Rouhi." Bai musa ba ta kawo masa suka ci tare suka yi sallar i'sha tare. akinta shiga ta auko cake in da ta yi da kanta ta yanka ta bashi ya ci itama ya bata yana cewa, "kina ta zirga-zirga ko?." Nayla ta ce, "da kaina na yi fa, ko decor in ma da kaina nayi, kayan na siya kawai. Ya za ayi na bari masu decoration su shigar min akin mijina?." Kallon ta ya yi yana an ta e baki ya ce, "uhum ka ga mai miji." Dariya ta yi ta saka sauran cake in a fridge ta dawo ta zauna a kusa dashi. Shi kuma baya son zaman da take yi a inda yake, yanayin shigar jikinta da hamshin ta haukata shi yake yi, gashi daman kwa ayinta ya dawo, kuma bai manta da yanayin da ya barta ba, baya son yin abinda zai takura ta shiyasa yake kamewa amma ta kasa ganewa. A jikinsa ta kwanta ya yi shiru bai ce mata komai ba, jin shirun yayi yawa sai ta ago tana kallonsa, zai yi magana ta hana shi maganar ta hanyar fara kissing insa, ya mayar da ido ya rufe yana jin abinda take yi masa amma ya kasa bata ha in kai, baya so sai ya birkice kuma ta janye jikinta. Nayla a zuciyarta take jin zata iya a wannan lokacin baza ta bashi kunya, amma shirun da ya yi mata baya taya ta sai ta sare, duk arfin guiwar da take ji dashi ya gusshe, ta kalle shi ta ga idanunsa a rufe suke. Ajiyar zuciya ta yi kamar yadda ya yi, ta mi e ta bar jikinsa hankali ta shiga ciki. Shima tashi ya yi ya shiga aki ya zauna ya dafe kai da hannunsa. Bai san me zai yi mata ba, bbai san ya take so ya yi ba, indai za a cigaba da kasancewa a haka tabbas akwai babbar matsala. Ba jimawa Nayla ta dawo ta sake zama a kusa dashi, bata yi asa a guiwa ba ya cigaba da abinda zai faranta masa rai. Tun yana daurewa har ya kasa ya fara taya ta amma zuciyarsa na ji tsoron guduwarta. Nayla kuwa kuka take yi amma haka take daurewa ko zata iya amma ta kasa jikinta ya fara rawa tana jin numfashinta kamar zai auke. Ganin yanayin da ta shiga sai ya yaleta ya tashi ya fita daga akin gaba aya. Kuka sosai Nayla ta yi na rashin mafita, dan ita haushin cikin take ji da ya sakata a wannan yanayin da take cutar kanta da mijinta. Tunawa take yi rabon ta da shi har ta manta, Allah ka ai ya san halin da yake ciki dan ta san halinsa a wannan angaren. A falon bacci ya auke shi ita kuma a aki tayi bacci, ta riga shi tashi tana fitowa yana tashi ta kalle shi ta ce, "ina kwana." Kallon ta ya yi ya ce, "Kin tashi lafiya." "Lafiya lau." Daga haka ta shiga ciki ta yi wanka, ta fito ta dafa tea daman tana da bread ga kuma cake in jiya ta dawo falon ta tarar ya dawo ya zauna da alama shima ya yi wanka. Ajjiyewa tayi a gabansa, ya auki tea in yana sha. Ya share abinda ya faru a ransa ya fara bata labarin abubuwan da suka faru a China da nasarorin da aka samu da wanda za a samu nan gaba. Itama ta sake dashi suna ta hira kamar komai bai faru ba, amma ta san sai an zo angren zai nuna mata kuskurenta. Ta inda yake burgeta kenan, laifin angare aya baya shafar zamansu, zai ware a inda take masa laifi ya hukunta amma ba a komai ba. In dai kuwa ya birkice mata to tabbas ta ata masa rai sosai. Nayla bayan ta shanye tea ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Rouhii!." Ya kalle ta alamun yana jiran arin bayani dan bazai amsa ba. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Abinda yake faruwa wallahi bana sane nake yi, ka yi ha uri." Bai tanka ba daman ta yi tunanin haka, sai ta dawo kusa dashi ta ce, "baka ha ura ba?." Nan ma ya yi mata banza bai ce komai ba ta ce, "Ajiyarka da na kar a ce ta kawo wannan sa anin." Nan ma ya yi mata banza dan ko kusa bai kawo ciki take nufi ba. Ta ago da kansa tana kallonsa ta ce, "Rouhii!." Yana kallon idonta ya ce, "Jidda na ce miki kin yi min laifi ne?." Ta girgiza kai ta ce, "baka ce ba, amma ni na san ina yin abinda baka so wallahi." Shiru ya yi bai ce mata komai ba ta ce, "Rouhi ajiyar da ka ke cewa yaushe zan kar a ita na kar a fa." Da sauri ya kalle ta sai ta kawar da kai gefe, ta ri e hannunsa ta ora shi akan cikinta ta ce, "Da gaske Rouhi, da gaske nake shine silar canjawata" ta fa a tana fashewa da kuka. Shi ta rikita shi ya kasa gane me take nufi, ta ora hannusa akan cikinta ta kuma saka kuka sai ya kasa gane abinda take so ta ce. Ya ce, "Jidda meye na kukan? Ki fa a min meye a cikin na ki?." Ta kalle shi ta goge idanunta ta ce, "Ka tambayi Didi." Bai yi asa a guiwa ba ya kira Didi kai tsaye ya saka a speaker, tana auka ko gaisawa basu yi ba ya ce, "Meye a cikin Jidda? Ta saka ni a gaba tana kuka, wanne ciwon ne a ciki?." Didi ta yi dariya ta ce, "ita bata fa a maka ba?." "Inda ta fa a ai bazan kira ki ba." "ciki ne da ita Omar." Omar ya wara ido ya ce, "bana son wannan wasan da ki ke min Didi." "Ba wasa bane Omar da gaske ne, in zaka tuna lokacin da na ce maka na rakata asibiti ai cikin aka tabbatar mana dashi, ta ce kar na fa a maka ne shiyasa na yi shiru." Cikin ru ewa ya ce, "Wai da gaske ki ke?." "Wallahi da gaske nake Omar, kaima ka kusa zama uba." it ya kashe wayar ya cilla ta kan kujera ya zubawa Nayla ido yana kallonta ya rasa wanne irin farin ciki zai yi. Nayla ta goge idanunta ta ce, "Likita ya ce duk abinda nake yi shine yake sakawa. Rouhi ina kewarka nima, amma ban san ina barin ka ba sai bayan na yi." Shi ba ta wannan yake ba a lokacin, ya mi e tsaye ya ri e hannunta ta mi e itama ya kalli cikinta ya kalle ta ya ce, "yanzu da gaske kawai ana a nan Jidda?" Ya fa a yana ora hannunsa akan cikinta. Nayla ta aga kai alamun eh ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yana cewa, "Alhamdu lillah, Allah na gode maka, ashe nima zan ga wannan rana Jidda?. Kina da ciki fa, cikina ne a jikinki, zaki haifi yaro ko yarinya. Jidda na kasa sarrafa