Sashe 113
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da alfahari a zuciyarta. Kallon ta ya yi kamar zai yi magana sai ya auke kai bai ce komai ba, ya shiga mota Nayla ta shiga ya ja motar yana murmushi. Ya san in ya biyewa Didi kuka zata yi masa shi kuma kuka ne baya so. Yana so ya saka Didi farin ciki a rayuwarsa, yana so ya ga tana dariya shiyasa yake jin da i a duk lokacin da ya zama silar dariyarta. Cikin farin ciki ya cigaba da tafiya bayan ya ri o hannun Nayla. KRB3P067 Rayuwa tana ta tafiya Omar da Nayla zaman su abin burgewa, ko yaushe cikin nunawa juna kulawa da soyayya suke tunda ta ajjiye aiki yanzu babu inda take zuwa sai ta kama take fita. angaren sana'ar Omar ba a cewa komai, albarka sai samuwa ta ke yi daga inda ba a yi tunanin zuwan ta ba, alkhairi kawai ake samu ta ko ina, dan yanzu shagunansa sun sake yawa sannan sun canja inda suke aikin sun koma babban waje, ma'aikata sun sake yawa. Kasancewarsa mutum ne mai kyautatawa ma'aikata da basu ha insu akan lokaci ya saka ake tururuwar son yin aiki dashi, sai dai yana da shara in babu wasa da aiki. Ranar Sunday Nayla tana zaune a aki da daddare sai ga kiran wayar Mama Sa'adatu. Nayla ta auka suka gaisa Mama ta ce, "Kin san bikin Yayanki Abbas ya kusa ai." Nayla ta ce, "Ummimi ta fa a min, na ce ashe akwai shagali, ga na Salma ga na shi." "Sosai kam." "Allah ya nuna mana." "Amin. An kai kayan lefenki gidan Daddy azu." Nayla da mamaki ta ce, "Kayan lefena kuma Mama? Wanne irin kayan lefe?." Ta yi dariya ta ce, "Da alama baki sani ba kenan, to ai mijinki ya ha a miki lefe azu muna zaune sai ga Yayarsa da wasu mata masu kama da shuwa, ta ce mana an uwan mahaifiyarsu ne sun kawo kaya wai lefen aurenki. Suna can a ajjiye kaya ba ka an ba kaya masu uban yawa da tsada." Nayla ta ce, "Wallahi ban sani ba Mama, ni ko da wasa bai fa a min ba, ban ma san labarin ba ban da yanzu." "Shiyasa ai na kira na fa a miki. Daddy ya ce min na aika a kwashe a kai gidan ku Kaduna, Ni na auka ma ke kika yi masa maganar ya yi miki lefen." "A'a wallahi Mama, ko da wasa ni ban ta a wannan maganar ba, ni wallahi na manta ma da batun wani lefe a duniyar nan." "To shi bai manta ba kam, na yi matu ar mamakin kayan da aka zuba a ciki, na ce Allah ya arawa nema albarka. Kaya dai suna nan a ajjiye, inda ki ka san lefen Salma aka kawo, hatta kayan kwalliya an zuba." Nayla ta ce, "ikon Allah, ban sani ba." Mama ta ce, "Ya baki mamaki, Zan saka a auko hoton kayan a turo miki ki gani. Kaya sun y i kyau Nayla, sai ki yi masa godiya dan ya kashe ku i wallahi ba ka an ba." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "To Mama." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar. "Wai kayan lefe" ta maimaita da mamaki dan bata auka zai faru ba. arasa saka kayan ta yi, ta saka kaya riga da siket an kanti, rigar tana high neak amma daga irji a an tsage take, sannan bayan ta a bu e yake. Siket in kuma mai tsaga ne daga baya har cinyarta, kayan sun zauna ajikinta komai ya yi mata daidai. Gashin kanta ya sha gyara, ta gyara ta aura aramin ankwali. Ta gama shafa turare kenan ta ji ya shigo gidan, ta ajjiye abinda yake hannunta ta fito falon ta ce, "Welcome Rouhii" ta fa a tana arasawa ta an yi hugging insa ka an kafin ta janye jikinta ta kalli fuskarsa ta ce, "ka gaji da yawa ko?." Omar ya kulle idanunsa ya bu e ya ce, "na gaji." Ta ce, "sannu, mu je ka yi wanka yanzu sai kazo ka ci abinci." Bai musa mata ba suka tafi tare yana ta yaba kwaliyyarta ita kuma hakan ke yi mata da i, shiyasa ko bata yi niyar yi ba in ta tuna in dai ya gani sai ya yaba sai ta yi. Wajan yabon kwalliyarta da abincinta yana sakawa ta ara aunarsa. Tare suka fito bayan ya shirya ta kawo masa abinci, bai i ci ba ya ci bayan ya gama ya kalle ta ya ce, "Abubuwa suna neman yi min yawa Ashiq, bani da hutu ko ka an, nan su kira ni a waya can su kira ni a waya. Gobe za a bu e shago a garinku, babu plan in zuwa Kaduna a tsarina gobe, dole Bashir zan tura aje a san abinda za ayi." Nayla ta ce, "Sannu Rouhi, Allah ya cigaba da saka mana albarka a duk abinda ka saka a gaba, Kuma in sha Allah na Kaduna ba za ka samu matsala dashi ba, yaron a gida mu ya tashi bashi da wata matsala." "Amin ya rabbi. Amma ina shan wahala ko a iya amsa waya ne, gobe akwai ba in da zan yi ina tunanin ma nan gidan zasu same ni, kinga bani da lokacin zuwa Kaduna." Nayla ta ce, "na ce ka na a ni na zama personal assistant inka amma ka i, ka ga da ba sai na wakilce na zauna da ba in ko na tafi Kadunan ba?." Ya aga ido ya kalle ta cikin harara ya ce, "kawai sai na sallama ki ko wanne banza yana ganar min mata? Lalacewar tawa bata kai haka ba. Amma zan shigo dake ta dole, tunda naga na fara ba i turawa dole sai kina kusa." Dariya tayi sosai ta ce, "Ba wani nan, kana fa jin turancin nan kawai baka son yin ne, inda ka damu dashi da yanzu ka kai inda baka auka zaka kai ba a iyawa." Ya ta e baki bai ce komai ba kafin ya gyara zama ya ce, "kina ji." Nayla tayi dariya dan ta san indai zai ce kina ji in nan magana mai mahimmaci ce, ta gyara zama ta ce, "ina ji." "Me ki ke ganin zan iya a yanzu? Gida nan zan siya ko kuma na fara gina nawa?, Ko kina ganin na siyi babban waje da ku in sai ayi lissafin nawa za a kashe in za a ha a babban company?. Nan yana neman yi mana ka an, ma'aikata sai aruwa suke yi, wani so yake ko a mai goge-goge ne a auke shi. Kuma Alhamdu lillah tunda ana samun alkhairi bazan aukar ma'aikata ba." Nayla ta ce, "ginin ya kamata ka fara yi, kafin a gama kaga an samu wasu ku in sun sake shigowa in ya so daga sai a san ya za a yi a yi samar da company." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "To a ina ki ke so a yi ginin?." "Wannan kai zan tambaya, kaine an Kano ai ba ni ba." Ya yi murmushi ya ce, "in sha Allah za a duba." Nayla ta ri o hannunsa ta ce, "YaMar!." Ya kalle ta bai yi magana ba ta ce, "Wai daman kayan lefe ka ke ha a min?." Ya an murmusa ka an ya ce, "eh mana, Didi ta ce haka ake yi tun kafin haihuwar Marmerh tayi min mgaganar. Sai daga baya na dinga bata ku in a hankali har aka tara da yawa aka siya aka huta." "Amma Rouhii ni.....!" Ya katse ta ya ce, "kar ki fa i wani abu, in ka an suka yi miki Jidda zan iya arar da abinda na mallaka a kan ki, In akwai abinda ki ke so ki fa a min sai a kawo miki." Nayla ta ce, "A'a, ba ka an suka yi min ba Rouhii, Mama sai yabon kayan take yi , kawai na ga nida kai mun zama aya ai, meye na kwashe ku i ayi min kayan lefe?." "Na fa a miki ku in sun jima a wajan Didi, sai yanzu ne ta yi takai amma ni na jima da bata ku in. Ki yi ha uri na san kin fi arfin kayan, babu yawa ki yi amfani dasu, amma ban gama ba, in sha Allah ko me kike so koda a asar waje ki ke so a yi miki kaya ke ka ai a duniya zan kai ki a yi miki. Ki cigaba da taya ni addu'a kawai." Ta kwanta a jikinsa ya ora hannunsa a bayanta ta ce, "Na gode Rouhii, na gode. Allah ya bar m tare har aljanna." "Amin, abinda ya kamata ki ce kenan daman tun azu, kuma daman ina jin haushinki." Nayla ta kalle shi ta ce, "haushina kuma?." "Eh, mun je gidan tv nan sun zo sun sake aukar mana tallah tunda yanzu abubuwa sun cigaba. Sai yanzu na fahimci kwanakin baya da ki ka ce min dubu ari biyu ki ka kashe raina min hankali ki ka yi, ko a lokacin kin kashe ku i ya yi miliyan aya." Nayla ta yi dariya ta ce, "to ai kaima kaine da bincike, dan mata ta yiwa mijinta abu duk sai ka bi ka damu sai da ka biya ta? Ina sane na ce maka haka ai, ko addini akwai taimako a tsakanin miji da mata ai." "Na sani, amma abin ya yi yawa sosai. Ku in sun yi yawa sosai, dan haka zan dawo miki ragowar ku inki." "Wallahi bazan kar a, in kuma ka dawo dasu baka auke ni matsayin abokiyar sirrinka ba." Omar ya kalle ta ya ce, "harda wallahi?." Ta murgu a baki, ya yi murmushi ya sumbace ta a kumatu ya ce, "zan saka miki da wannan alkhairi in sha Allah, zaki zama gimbiyata a ko ina." Nayla ta ce, "ko a yanzu ni gimbiya ce, mijina babu abinda baya yi min." Murmushi ya yi baice komai ba. Ta kalle shi ganin fuskarsa ba yabo ba fallasa ta ce, "sai na tuna lokacin da ka ga ana haska tallan a tashar, ka tsare ni da ido kana hararata, nace maka nayi ne saboda kai Yayana ne ka yi min kallon banza ka ce ba a lissafoni a cikin wanda