← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 205

Sashe 129

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalle ta ya ce, Ban da fita ke ka ai Jidda, ban da yawo a mota ko yaushe. Duk inda zaki je ki fa a min, sannan ki saka a kai ki kar ki fita da kan ki. Ganin zata yi kuka ya ce, "Kar ki min kuka, zo mu je" ya fa a yana ri o hannunta ita kuma ta ta jawo trolly bag in da zai tafi da ita. Tare suka fito falo, Didi ta mi e tana kallonsu tana murmushi cikin burgewa ta ce, "Ka fito?." Kai ya aga ya kalle ta ya ce, "Na fito Didi, ki taya ni da addu'a." Didi ta ce, "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, ya baka abinda ka je nema." Murmushi ya yi yana kallon ta, ya saki hannun Nayla ya ri e na Didi duka biyun ya ce, "Amin Yaya Aisha, Duk abinda ki ke so ki fa a min kar ki ce bana nan baza ki fa a min ba, in wani abun ya taso na Marmerh ki sanar dani. Sannan ban da yawo ko ina musamman da daddare, bana so wani abu ya same ki. Didi tayi dariya jin sunan da ya kira ta dashi ta ce, "To Yaya Omar, in sha Allah." Ya kalli Nayla ya kalli Didi ya ce, "ki kular min da amanata Didi, da ke ka ai na yarda na bar ta a hannunki, kar ki bari ta dinga wannan kukan kin ji?." Didi ta ce, "in sha Allah Omar, zan yi duk abinda zan yi wajan tayata farin ciki." "Na san zaki yi Didi." Ya shafa fuskar Marmerh da take bacci, ya kalli Nayla da take hawaye ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Yaushe zaki tafi gidan Daddy in?." Cikin dauriya ta ce, "In anjima" ta fa a murya na rawa sosai. A tausashe ya ce, "Don Allah ina ro onki kar ki dinga fita ke ka ai, duk inda zaki je in dare ya yi kar ki ce zaki yi driving ki bari a kai ki. Ina so naje na dawo na same ki lafiya, bana so wani abun ya same ki kin ji?. Nayla ta aga kai alamun to, ya tako ya zo inda take ya ce, "in kina kukan nan sai na ji kamar na fasa tafiyar nan, gaba aya tafiyar ta fita daga raina wallahi, a haka kike so nayi farin ciki in kina kuka?. Baki ga Didi bata kuka ba?." Sake shiga jikinsa tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya yi murmushi tare da rungumeta idanunsa a kulle kafin ya sake ta ya agota daga jikinsa ya ri e hannunta ya ce, "Zan tafi." Ta goge hawayen idanunta ta ce, "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya." "Amin Ashiq, Ki yi min alqawarin baza ki cigaba da kuka ba." "Ban yi alqawari ba, ni ka na san me nake ji a zuciyata." "nima ni ka ai na san abinda nake ji, amma na yi ha uri kema ki yi kin ji?." "Bazan iya ba." Murmushi ya yi ya kai bakinsa kusa da kunnenta ya ce, "Aljanun da suka tashi jiya a wannan yanayin na baki ajiya Allah yasa ki kar a, so nake kafin na dawo na ji an ce ajiyata ta yi wari, har Didi ta san na baki ajiya anta." Murmushi tayi mai sauti ta rufe ido ya ja hancinta ya ce, "kunyar ce ko?." Murmushi take yi ta ce, "in dai ka bada ajiyar da kyau na kar a, in kuma baka bayar yadda ya kamata ba laifina ba ne." "Bara na fa awa Didi a ji laifin waye." Ta wara ido ta ce, "Rufa min asiri, kar ka fa a mata don Allah." "To na rufa miki, amma sai kin yi dariya na gani." Sai kuwa ta yi dariyar ya juyo inda Didi ta ke ya ga bata wajan ya kalli Nayla ya ce, "kin ga kin saka na za e da yawa a gaban Didi, gashi ta gudu." Nayla ta ce, "Allah babu ruwana, laifin ka ne." "Laifin ki dai." Ta kalli agogo ta ce, "Mu je na san su Bashir suna jiranka." aukar jakar ya yi ya ri o hannunta sai ta turje ta tsaya ta ce, "Rouhii!." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Na'am Ashiq! Me ki ke so?." Ta matso kusa dashi ta ce, "to ka an rage tsaho ka yi min tsahi da yawa." Bai ce komai ba ya agota jikinsa ya rabata da asa, ta yi kissing insa kamar yadda ya yi mata azu. Idanunsa a lumshe ta kalle shi ta ce, "Ina sonka Rouhii." Ya lumshe ido ya ce, "Ina sonki Ashiq!." Murmushi ta yi ya direta a asa suka fito tare, a nan suka tarar da Didi suna hira Bashir ganin fitowa su ya saka suka kar i jakar aka saka a mota. Didi ya kalla ya yi murmushi itama murmushi tayi, ya kalli Nayla ya girgiza mata kai alamun kar ta yi kuka. Bata yi kukan ba sai ya auke kai daga kallon ta, ya kalli manyan yaransa da suka zo yi masa sallama duk suka gaisa sannan ya shiga gaban motar Goje da Tk da sabon yaronsa Mustapha suka shiga baya suka fita daga gidan. Nayla tare suka koma da Didi, ta yi ari ta ware suna ta hira da Didi har ya kira ta a waya ya shaida nata sun shiga jirgi zasu tashi. Suka yi masa fatan sauka lafiya daga nan ya kashe suka cigaba da hira da Didi. Amma zuciyar Nayla babu da i, kewar mijinta take ji amma babu yadda zata yi. KRB3P078 Nana haleema. A daren Nayla ta auki motarta a gidan Hajja ta ha a kaya ta tafi gidan Daddy dan Salma ma ta koma har Hajja tana can ana ta shirin biki. Suna zaune gaba aya a falo ana ta shirye-shirye Mummy ta ce, "Nayla ai na auka Kaduna zaki gudu." Nayla ta kalli Salma tana dariya ta ce, "Ai Mummy ina nan, ni ce babbar awar amarya ina zan tafi Kaduna?." Mummy ta yi dariya ta ce, "Gaskiya ne. Kuma kin san da yake ma duk events in a nan ne ba damuwa za a yi da zuwa can ba." Nayla ta ce, "shiyasa ban saka a raina zan je ba, ina za a kai amarya ma tafi" ta fa a tana dafa Salma tana dariya. Mummy ta ce, "na auka baza ki je ba ai." "Zuwa kai Mummy." Suka cigaba da hirar biki tana yi tana kallon waya dan ta san har lokacin mijinta yana sama suna tafiya. Haka aka cigaba da hirar biki kamar baza su yi bacci ba, sai dare sosai suka yi bacci. Nayla tana tashi da asuba waya ta duba ta shiga WhatsApp tana tura masa sa on kewa da sauran su kafin ta cigaba da harkokinta. Sai da ya kwana biyu da tafiya da yamma tana zaune an gama yi mata gyaran jiki, dan duk abinda aka yiwa Salma sai an yi mata kawai ta ga kiransa ta whatsApp call. Hannunta har rawa yake yi ta auka ta saka a kunne ta kasa cewa komai. Daga nasa angaren shima bai ce komai ba sai daga baya ya yi murmushi tare da ajiyar zuciya ya ce, "Ashiq!." Nayla a kasalance ta ce, "Rouhii!." Omar ya ce, "uhum kina lafiya? Ina fatan kin daina kuka ko?." "Rouhi bazan daina kuka ba har sai ka dawo." "Ki fara lissafi, har an ci kwana biyu ko?." "Ka sauka lafiya?." "Lafiya lau, shigata hotel kenan na kiraki, Na damu na ji muryarki, zuciyata tana fa a min matata tana nigeria tana kuka." Nayla cikin shagwa a ta ce, "Baka huta ba?." "Ban huta ba Jidda, sai yanzu da na ji maganarki zan huta. Na gaji sosai, ina ma kina tare dani da kin yi min tausar nan taki mai saka ni bacci." Nayla ta lumshe ido ta ce, "Ka je ka huta Rouhi, na san in ka gaji sai ka fara ciwon kai, bana so kanka ya yi ciwo." "Zan huta Ashiq!. Kina lafiya? Kin fara jin alamun ajiyata?." Nayla tayi dariya ka an ta ce, "Rouhii haka ka ke son yara ban sani ba?." "Nima ban san ina so ba sai da aka haifi Marmerh, ina so na ga an nuna yarinya kyakyawa kamar ki an ce wannan ar Omar ce wacce Jiddan shi ta haifa." Murmushi ta yi ta ce, "Yanzu ka huta tukunna, bana so ka yi ciwon kai." "Yanzu kuwa Ashiq! Dare ya yi sosai a nan, asuba ta kusa." "Mu kuma ko sallar magriba ba mu yi ba." "zan kira ki video call in anjima, ki kasance ciki shiri zan ga abinda na yi kewa, ina nan ina tunani da kewar rashin jinsu a jikina da bacci tare dasu, kin gane ai." Dariya tayi shima haka ya kashe wayar. Nayla bayan sun gama waya sai walwalarta ta aru ko babu komai ta san yana lafiya. Ta cigaba da harkokinta bai kira ta ba sai bayan sallar i'sha ta shiga aki har da rufe ofa ta saka lock ta zauna sannan ta auki kiran. Fuskarsa ta bayyana akan screen in sai ta ga ya sake yi mata kyau yayi haske gashin kansa ya kwanta kamar ba shekaran jiya suka rabu ba. Omar ya ce, "Ya dai ki ke kallona, na yi miki kyau ne?." Nayla ta ce, "sosai ma kuwa, ka yi bacci kuwa?." "Ban yi ba, yanzu aka idar da sallar asuba da zan kwanta sai naji bazan iya ba sai na ga fuskarki. Ga ki nan kin yi kyau sosai, daga tafiya kwana biyu naga an sake canja min ke." Nayla ta ce, "mu kuma a nan an yi sallar 'isha, ka je ka huta in ka farka daga baccin sai ka kira ni." "Lokacin ai kin yi bacci." "Zan katse baccin na amsa kiranka Rouhii." "To Ashiq zan huta." Kiss ta yi masa sannan ta ce, "Bye Rouhi." Katse kiran ta yi dan tana so ya huta ta biye masa bazai huta ba. Kwanakin biki yana ta tahowa ana ta shiri Nayla na ta shan soyayya da mijin ta a waya, duk inda ya je sai ya fa a mata, haka duk abinda ya siya sai ya tura mata.
Chapter 129 · 0% Book details