Sashe 124
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ma hukuma ta auki matakin, tunda har suka ta a min matata...." Sai bai arasa ba yana girgiza kai cikin uncin zuciya. Nasiha suka dinga yi masa akan komai zai faru kar ya koma rayuwar baya yana jin su bai tanka ba. Omar ya kalli AbdulHamid ya ce, "Ka kular min da Yayata, in ba su samu dama a kaina ba kanta zasu dawo. Kana gani abinda suka yiwa Jidda, da basu samu dama a kaina ba sun citar da ita. Da Didi, da Marmerh, da Jidda, da kai kune ka ai dangina, zasu iya huce haushinsu a kanku. Ka kula da motsinta, nan kusa kar ka bari tana fita ita ka ai har sai an warware komai." AbdulHamid ya ce, "in sha Allah babu abinda zai faru, ka kwantar da hankalinka, tunda muna addu'a babu abinda zai same mu. Addu'ar ce ta ku utar da Nayla har abin ya tsaya a haka, in sha Allah babu abinda zai faru." Didi a sanyaye ta ce, "Nidai ko kaina suka saka a gabas suka yanka don Allah Omar kar koma ruwa ka auki mataki a hannunka. aukar matakin shine bazai yi min da i ba har a cikin kabarina." Ya bita da kallo kafin ya girgiza kai ya ce, "in nace miki kamar kina shan waya sai ki ga kamar wasa nake yi. To akwai halittar da ta isa ta saka kanki a gabas ta yanka na yaleta? Ai wallahi bisa ganganci aka sake arin hakan a kanun labaran na ranar sunan Omar ne zai fara fitowa. Ki daina wannan mafarkin. Hannun Jidda ma da suka jiwa ciwo sai sun biya bashin hakan wallahi" ya fa a yana kawar da kai. Ya girgiza kai ya ce, "Da ke, da Jidda, da marmerh, da mijinki, da su Bashir babu wanda ya isa ya ta a ku na tsaya ina kallonsa. Ai ba ruwa zan koma ba Didi, cikin kogi zan fa a dan wallahi abinda nayi a baya ba komai bane akan abinda zan yi. Ke dai Allah ya kiyaye kawai, amma ko....hmmm!" Ya fa a yana girgiza kai. Didi ta ce, "Allah zai tsare mu, babu abinda zai same mu in sha Allah. Ita Naylan Allah ya tsare ta, tunda gata a zaune a tare da mu." Ya bita da kallo ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai faru." Ta yi ajiyar zuciyar ta kalli Nayla da bata cewa komai. Ta kalle shi ta ce, "To Omar ka nemi sulhu da wal iyar kawai a huta mana. Ka duba abinda suka yi arin yi akan Nayla, in na nemi sulhu shikenan an huta." are mata kallo yake yi kamar mai son gano wani abu a tare da, kafin ya an yi murmushi ya ce, "Omar baya neman sulhu, sai dai a nemi sulhu dashi. Ki yale ni Didi, wanda ya yi gaba baya komawa baya." Didi ta yi shiru suna cigaba da yi masa nasiha yayi musu shiru bai ce komai ba. Sai da suka taso zasu tafi Didi ta kalle shi ta ce, "Nayla ta tsorata da kai Omar, ka rarrashe ta ka daina yi mata wannan fa an." an yi tsaki ya ce, "Tausayinta nake ji, ina gani kamar ban zama miji na gari a gare ta ba, ta silata ta shiga wannan yanayin, amma haushinta nake ji sosai. Ta raina ni ne kawai, dan ta ga ina yi mata dariya shiyasa ta samu wannan damar. A cikin wannan yanayin da ake ciki kawai ta hau napep ta fita ba tare da na sani ba? Dakonta fa ake yi a waje. Tk ya ce saran da suka kai mata a wuyanta suka so ya same ta, suna tsinke jijiyar wuyanta da yanzu ba wannan maganar ake yi ba. Ba dan Tk ba da me kike tunanin zai faru?." Didi ta ce, "Ka yi mata uzuri, bata ta a shiga irin wannan yanayin ba sai wannan lokacin. Kuma ita ta aukar fitar da tayi zai kawo mata sassaucin tsoron da take ji. Kuma tunda Allah ya yi sai ta ji wannan ciwon ko bata fita ba sai an shigo har gida an cutar da ita. Dole zaka ana irin abinda ka dinga anawa mazajen wasu akan matansu a baya..." Omar ya bita da kallo jin abinda take fa a, ta ce, "Eh Omar. ba dai kaji zafi a ranka ba? Ka ji ciwo da ra in a zuciyarka saboda abinda ya same ta ba?. To Allah ne ya ana maka dan kaji abinda wasu suka ji a lokacin da ka yiwa nasu, kai kanka baka san iyaka adadin matan da aka yiwa irin abinda aka yiwa Nayla ba, ba dan komai ba sai dan saboda laifin mazajensu ya shafesu. Dan haka ka nutsu kawai, mu yi fatan Allah yasa ya tsaya a haka." Ganin ya kasa magana ya tafi tunani sai ta ce, "A firgice take Omar, tsoronka ya riga ya tsarata, ka taimaka ta dawo nutsuwarta ta daina wannan firgicewar don Allah. Ka san a ina yarinyar nan ta taso, ba sabawa da wannan tashin hankalin tayi ba shiyasa ta tsorata. Bana tunanin allura in ba ta neman lafiya ba ta ta a sokarta, yau gashi hannunta a aure yake saboda an sare ta da wu a. Kuma ido da ido ta ganka da jini a jikinka dole ta ji tsoro, abinda bata ta a gani a zahiri ba sai a film, dole ta shiga wannan yanayin. Ka yi ha uri, ka yi mata uzuri, duk fushin da ka ke yi da ita a kan ta fita ka ajjiye shi don Allah." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba. Bashir ya saka suka raka su Didi dan a yanayin da ake ciki bazai yi sake da lafiyarsu ba. KRB3P074 Nanahaleema. Lokacin da ya koma bata falo, akin ta ya shiga ya tarar da ita a kwance a kan gado layi luf a kan gado, ya kunna hasken akin suka ha a ido ya ce, "kin ci abinci ne zaki kwanta?." Yadda yayi maganar babu wasa ya saka ta ce, "mun ci da Didi." Ya girgiza kai ya ce, "a nan kika saba kwana kenan?." Ta mi e zaune ta ce, "ba a nan ba ne." "Rainin ne ko?." Ta sakko daga kan gadon bata ce komai ba ta wuce ta tafi akinsa. Ya sauke numfashi ya bita akin dan bazai iya barinta ita ka ai ba a kusa dashi zata kwanta. Sai da ya shiga akin ya ce, "me yake damunki?." Nayla ta ce, "babu komai." Ya taka inda take ya ta a wuyanta, ya ri e kanta yaji babu alamun ciwo, ya duba hannunta yaga ciwon babu abinda ya same shi. Ya bita da kallo ganin tana rawar jiki ya ce, "ke wai meye abin tsoro a jikina?." Ta sunkuyar da kai ta ce, "ka yi ha uri." Yayi aramin tsaki ya bata waje ta kwanta cike da fargaba Washe gari da kansa ya kai ta aka yi swapping sim card in ta, bayan sun dawo suka biya asibiti aka duba ciwon, sannan ya siya mata sabuwar waya ya ajjiye mata. Jikin ta duk a sanyaye yake haka ta ora komai na wayar saboda ta san an gidansu suna nemanta. Kwana biyu suka kwashe a wannan yanayin, bata shiga harkarsa kuma a waje aya suke kwana, daga ina kwana babu abinda take iya ce masa, shima daga ya amsa shikenan babu wata magana. In ya riga ta tashi zai yi abinci kuma su zauna a waje aya su ci, in ta riga shi tashi zata yi abinci itama. Zuwa lokacin wa anda ake zargi hukuma ta shiga tsakani, komai ya wuce kamar bai faru ba amma ita dashi basu dawo daidai ba, dan ita tsoronsa take ji, sannan kuma tana jin haushin fa an da ya dinga yi mata ko ciwon hannunta bai duba ba. A haka ta je bank aka gyara mata account inta da aka yi blocking har lokacin ba shiri suke yi ba. Ranar da aka kwana biyar da faruwar abun da daddare sun dawo daga asibiti an duba mata ciwon, ta gama shan tea ta dawo aki ta canja kaya zuwa na bacci ta auki wayarta zuwa akinsa. Tana shiga suka ha u a hanya, suka ha a ido ta auke kai ta yi gefe zata wuce ya tare mata hanya, ta sake juyawa aya side in ya sake tare ta, ya matso kusa da ita har yana jin saukar numfashinta. Ganin ya hanata wucewa gashi ya matso kusa da kusa ita sai ta tsaya cak tana sauke numfashi a hankali. Cikin nutsuwa ya saka hannu biyu ya ago fuskarta yana kallon idonta da suka fara taruwa da hawaye. Kumatunta ya shafa, calmly ya ce, "Jiddana, Ashiq!" Ya furta a sanyaye yana kallonta. Fuska ta e zata yi kuka, ya an yi tsaki ka an ya ce, "Kar ki yi kuka mana..." Nayla ta fa a jikinsa da hanzari ta rungume shi tightly tana kuka. Murmushi ya yi ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali cikin salo na auna. Nayla cikin kuka ta ce, "Ka dana sona...ka daina sona...!." Omar ya ce, "Shiii! Ki daina magana" ya ha a yana ri ugunta ya sake ha e ta da jikinsa sosai. Sun jima a haka kafin ya sassauta ri on da ya yi mata ya ri e fuskarta ya fara kissing inta slowly. Bai jima ba ya raba kansa da ita yana yamutsa gashinta yana kallon idanunta da suke zubar hawaye. "Ki yi ha uri!" Ya furta a hankali, ya sake kissing in bakinta na an sakanni kafin ya zare bakinsa yana shafa fuskarta. Ta sake komawa jikinsa ta kwanta tana jan numfashi. Sake ri e ta ya yi yana jan numfashi kafin ya ri e ta har kan gado ya zauna da ita ya zauna a gefenta ya ri e hannunta baice komai ba. Ganin tana kallon sa sai ya ce, "Ki yi ha uri da ni, na fa a miki ban iya acin rai ba, daman kuma na fa a miki zan ata miki rai wata rana, gashi ya faru" ya fa a yana kallon ta. Nayla ta bishi da kallo ya an yi murmushi ya ce, "ki daina jin tsorona Jidda, abinda ki ke tunani bai faru ba