← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 205

Sashe 200

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

so, babu lallai na dawo da wuri. Ta amsa da to bai jima a zaune ba ya tashi ya fita. _Jiya na yi kuka sosai, na gama editing ina burin yau na yi update gaba aya na huta, ina shiga naga ya dawo farko over 10k words, haka na gama kukana editing ya dawo farko. Na so na gama uptade yau amma ba zai yu ba, sai zuwa gobe in sha Allah._ Nana Haleema. P128 Haka aka cigaba da kar an barka, mutane Kaduna zuwan su daban ne musmaman da suka ji sunan Abiy aka saka. An yiwa yaro hidima sosai ku i da kaya kamar ba a so. Ranar suna aka ra a masa suna Abdallah aka yi hidimar taro kamar lokacin Musliha. Sai dai wannan lokacin an fi arnar ku i, an fi kashe ku i kamar ba nema ake yi ba, an yi arnar ku i a sunan Mufty, dan sai da ya kai ya kawo duk wanda ya zo sunan bazai tafi ba sai da atamfa da takalmi da mayafi da dubu ashirin na inki. Ga abubuwa manya-manya na rabo da aka raba a wajan, an yi hidima sosai kowa ya yi farin ciki. (Can na hango an Kiran Rabo comments section an hau layin kar ar Souvenirs, an arewapen har sun fi an whatsapp za ewa, ana ture su suna komawa). Bayan suna da kwana sati uku ya kama sati hu u kenan da haihuwar Mufty, Umma Saroot ta shiryata koma gida bayan ta gama shirya Nayla ta gyara ta yadda ya kamata. Dan ta lura an nata fitinanne ne, tunda ya lura Nayla ta samu tsarki babu zaman lafiya, har inda Umma take zai zo ya ce tazo, sai dai in taje ta gudo. Shiyasa tayi mata ha in da ba a yi mata a haihuwar Musliha ba, an yi mata gyara mai kyau sosai. Kyautar mota Omar ya yi mata ban da kaya da ku i da aka ha a mata, ba dan ya biya ta abinda tayi ba sai dan ya kyautata mata ya saka ta farin ciki. Ai kam ta yi farin ciki sosai, ta ji da i tayi masa addu a sosai. Dan a yanzu iyaye yake yi dasu, Umma sama Umma asa yake fa a cikin girmamawa da nuna su in dangin mahaifiyarsa ne, in zai gaishe ta kuwa har asa yake dur usawa. A an uwansu babu wanda bai kira sa ya yi murnar kyautar da ya yi ba, shi kansa da i yake ji a zuciyarsa, da in alkhairin yake ji a duk lokacin da yaga ya aikata ana farin ciki ana yi masa addu a, sai yana ji ina ma tun Didi tana raye ya bar komai ya wuce haka da bai san farin cikin da zata yi ba, Allah bai nufa zata gani ba. Ranar da Nayla ta kwana arba'in ranar suka bar bar Nigeria ita da mijinta da anta. A asar Canada suka yada zango, a cikin HoneyRose hotel. Babban hotel ne a asar, hotel ne da ya yake cikin five star kuma yake cikin top ten a best hotel in honeymoon. Hotel in yana angaren VIP, standard da kuma luxury. A vip suka yi reserving room, suka auki one parlor and two bedrooms, aya kids room, aya kuma couples room. Nayla ta bu e kids room in, ta ga akwai toys na yara da aka tanada a ciki saboda yara su yi wasa. Nayla da take kallon akin ta kalle sa ta ce, "Zaka iya bari su kwana su ka in ne?." Omar da yake bayanta ya yi ar dariya ya ce, "ba dole na ba, shiyasa aka tanadi wannan akin." "Daman kaine ai baka so su kwana su ka ai, kamar wani abun zai same su." A nan suka kwantar da Marmerh da Musliha da suka yi bacci, kasancewar wheather da suka samu asar ta show ce akwai sanyi sosai, sai da suka kunna wood stove akin, Nayla ta saka musu safa a afarsu saboda sanyi. Sai da ta gama shirya su sannan ta shiga nasu akin, babban aki ne mai girma, wanda aka zagaye ko ina da glass kamar kana waje. Kana ganin korayen furani da suka zagaya glass in. Bata tsaya arewa akin kallo ba ta shiga wanka. Saboda sanyin garin ko Mufty bata yiwa wanka ba, ta canja masa kaya ta goge masa jikinsa da baby oil. Tana gama shirya sa Omar ya fito daga wanka, ya shirya suka yi sallah sannan ta dawo ta tarar da Mufty ya yi bacci. Pecking insa ta yi a goshi ta ce, "Allah sarki Abiyna, har ya yi bacci." Kallon Mufy ta yi ta kalli Omar ta ce, "Wallahi babu ta inda Mufty ya bar ka, komai irin naka sak. Wannan in ya girma gaba aya kamannin ka zai yi." Murmushi ya yi yana daga zaune ya ce, "Haka ake ta cewa, Nima dai ina ganin kamar sosai. Lokacin da ake cewa ina kama da Didi bana gani ko ka an, in na kalle ta sai naga babu wata kama, amma shi kam ina ganin kamar sosai." Ta yi murmushi ta ce, "gaskiya kam kuma yi, har ya danne Musliha gaba aya. Ko nimeyasa basa yin kama dani oho." "Ina ki ke da arfin jinin da zasu yi kama dake? Ai daman da ni ya kamata su yi kama ba da ke ba." "Saboda me?." "Saboda ni nake yin cikin, ke aikin ki haihu kawai." Ta yi aramar dariya ta ce, "to da yi da haihuwar wanne ne mai wahala?." Ta fa a tana kafe sa da ido kamar yadda yaka kallon ta. an yi tunani kana ya ce, "eh to, gaskiya haihuwar tafi wahala. Ni fa na firgita a lokacin da kika fara na udar haihuwarsa, gabadaya kin fita hankalinki, kin ri e min hannu zaki kara ni. Wai daman haka ki ke da arfi ko duk cikin ciwo ne?." Dariya tayi sosai harda ri e ciki, ta dawo kusa dashi ta zauna ta ce, "Wallahi zafi ciwon ne kawai Rouhi, haihuwa ai ta wuce tunaninka. Shiyasa nake so da zaka bari mu yi family....." ai bata arasa ba ya ce, "wallahi ba za a yi ba, kuma ki daina yi min wannan zancen na fa a miki bana so. Yau zan samar da mai sunan Hajja in sha Allah." A firgice ta kalle shi ta ce, "Allah bazai yarda ba in sha Allah, wannan wanne irin fata ne? Kwana arba'in da biyu da haihuwa ka dinga yi min zancen ciki? Dan baka san ya ake yin haihuwar ba sai ka dinga yin min wannan mugun bakin?. Haba don Allah, ka bar fa a don Allah, wallahi gabana fa uwa yake yi ta fa a a sanyaye tana kallon sa. Hannunsa ya ora a saitin zuciyarta ya ji yadda take bugawa alamun tsoro da fargaba ya ce, "To shikenan na janye, Allah ya bamu kamar yadda aka samu bayan haihuwar Musliha." Ta kalle sa idonta ya ciko da hawaye ta ce, "Akwai wahala Rouhi." "Ke da kike jaruma? Haba ni ai bana jin ki, nasan zaki iya." Ta harare sa ta ce, "yadda baka son zuga nima bana so, ka daina zuga ni, ba wata jaruma." Dariya ya yi ya jawo ta zuwa jikinsa ya ce, "To na daina. Kar ki yi min kuka mana, kin ga dai amarci zamu ci, ki adana wannan kukan sai lokacinsa ya yi. Ta kalli fuskarsa ta ce, "nida ko kazar amarcin nan ta hausawa baka siya min ba." Ya yi dariya sossi yana girgiza kai tare da murza goshinsa da yatsu biyu ya ce, "ni fa ban san da ita ba a lokacin, sai yanzu da nayi abokai nake ji ana fa a, amma wallahi a baya ni ban san ana siyan wata kaza ba Jidda. Na san dai ana yin sallah, wannan marigayi Malam Salahudden shine ya sanar dani shekaru baya da suka wuce. Addu ar da ake yi in an idar kuma a waya na iyata, yawan zama active da nake yi a kan network a haka naji malamai suna koyawa har na haddace. Duk da sallar ta mu a makare muka yi ta amma mun yi in, kaza ce dai ba a siya ba Ya sauke numfashi ya ce, Allah ya kai hasken rahama kabarin Didi, ta yi wahala dani a rayuwa sosai, ba dan ita ba wata ila yanzu ko karatun sallah ban iya ba." Nayla ta ce, "Amin ya rabbi. Kuma ban auke maka ba, sai ka siya min kazar ." Ya kalle ta yana murmushin gefen baki ya ce, "za a siya Jidda, wacce kike so, fried ko grill one?." Ta an juya idanunta kana ta ce, "grill in dai." "Yanzu zan samo miki tunda yau ma amarya ce ke ai, na je na dawo?" Ya fa a da sigar tambaya. Ta sake kwanciya a jikinsa tana ri e kafa arsa ta ce, "Akwai sanyi kar ka fita, na yafe." "Ni ban yafe ba, yanzu zan je na dawo, ki jira ni." "A'a kar ka fita, Allah na yafe." "Allah ban yafe ba, ina zuwa" ya fa a yana tashi ya auki jacket in da yazo da ita ya saka, ya saka hular sanyi ya rufe kunnensa sannan ya fita. Da murmushi ta bisa, sai ta tashi ta shirya cikin shigar da zata gigita mata shi da hamshin da zai tashi hankalinsa. Ba jimawa ya dawo, da yake tana zaune bai ma kula da shigarta ba ya ce, "na sha wahala kafin na samo miki, kin san da yake ban san asar ba. Maza zo ki ci." Ya fa a yana bu e kazar sai tiriri take yi. Bata musa ba ta tashi ta sakko kusa dashi suka ci tare suka oshi. Sai bayan ta gama ci ta ga yana yana kallon ta yana dariya tare girgiza kai, ta ce, "me ya baka nisha i haka?." Ya an bu e idanunsa ya a ce, "An ce in aka ci kazar ai ana biya ko?." Ta kalle sa kamar bata gane ba ta ce, "Kamar ya ana biya? Wai gobe sai na siyo na biya ka?." Ya zuba mata ido ya ce, "ke a nan zaki bi ai madam" ya fa a tana nuna mata kan gado akin. Ta
Chapter 200 · 0% Book details